BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO 27

27

……….A hankali ta ajiye wuƙar tana murmushi, ta miƙe cike da isa da izza tana magana da shan gaban Anam, “To ƴar wasa da biri, ya akai ke kika zama birin kuma a hannun ƴan wasa?”.
       Idanunta dake cikin gilashi ta ɗago tana kallonta, ta saki ɗan murmushi da kauda idanun kamar bazatace komai ba. Sai kuma ta hurar da numfashi da sake maida kallonta gareta. “Mi kikeci na baka na zuba Madam. Da Juwairiyya kike tare fa, Juwairiyya Anam Usman MD Shareff bana gaggawa akan al’amarina, sai dai ina bama maƙiyi damar da zai sharemin hanyar fagen isar da saƙona. Su kin faɗa musu ni na zubar miki da ciki right? Tom ki jira shi kuma mai cikin yazo ya ɗaura bincikensa akan yanda akai na zubar ɗin, daga haka game ɗin zai fara ok!”. Ta ƙare maganar da kashe ido ɗaya ta rabata ta wuce tana dariyar rainin hankankali.
      Wani irin bugawa ƙirjin Fadwa ya shigayi da sauri-sauri, tabita da kallo harta shige. Juyawa tai ta kalli mai aikinta, ganin aikinta take hankalinta baya kansu tai saurin barin wajen ta nufi bedroom ɗinta. Kai kawo ta shigayi cikin tashin hankali, dan da gaske kalaman Anam sun mugun dukanta, kanta ya kulle harma ta rasa kalar tunanin da zatayi. Tayi waya da Shareff a daren jiya amma bai nuna mata komai ba akan maganar rigimar zubda cikin balle tace ko Anam ɗin ta sanar masa ne. (To mi yariyarnan take nufi?) ta tambayi zuciyarta batare da tasan ta inda amsa zata fito ba. Ganin ta rasa ina zata kama ta yanke shawarar kiran Sima, dan tana da basira sosai, tasha warware mata ƙulluka da ita ta gaza kuncesu musamman da abokan hamayyarta irin su Anam ɗin……

       Sima tazo, sai dai Fadwa ta jata sun fita can garden ɗin gidan dake bayan sashen maigidan saboda kar a ƙara maimaita irin na ranar. Acan suka tattauna. Har Sima ta wuce Aysha da Anam basu ma san da zuwanta ba dan suna can suna kwasar barci. sai yamma sosai suka tashi saboda saurayin Aysha daya kira ta zai zo…..

          Tun daga waccan ranar Fadwa bata sake shiga sabgar Anam ba. Itama Anam ɗin bata shiga tata ba aikinta ma ya ɗauke kaso mafi yawa na hankalinta. Babban burinta tayi ta kammala tabar Nigeria ta huta. Bata sake waya da Shareff ba tun waccan ranar shima. Sai dai taga sunayi da matarsa wadda in ta gama Aysha kawai take cewa Shareff ɗin na gaidawa. Takanyi murmushi a duk sanda hakan ta faru, duk da kuwa a ranta tanajin zafi da haushinsa. Sai dai takan ce inma baice yana gaida tan ba sai me.

★A ranar wata alhamis da tai dai-dai da zubewar cikin Fadwa Daddy yay kiran Aysha da Anam akan su samesa a gida. Daga wajen aiki Anam ta wuce, inda ta samu Aysha tuni tana can. Basu sami zama dasu Daddy ɗin ba sai bayan sallar isha’i. Cikin kulawa su Abban ke tambayar su babu wata matsala dai ko?. Murmushi Anam tayi, dan kai tsaye tambayar tafi ƙarfi a kanta ne. Tace, “Babu wani damuwa sai na zafi”. Dariya Daddy da Abbah sukai mata.
Bayan sun sarara Daddy ya dubesu a tsanake, “Yauwa kun san miyasa muka kiraku nan?”. A tare sukace a’a. Daddy ya jinjina kansa da cigaba da faɗin “Magana ce mai muhimmanci akan aure, yanzu dai kunga kun kammala karatunku, babu abinda ya kamaceku sai aure inba so kuke mu zuba muku ido ku tsufa a gabanmu ba, dan haka muna mai baku umarni ba shawara ba, kowaccenku ta bama wanda yake zuwa wajenta dama yazo mu gana da shi”.
A ɗan tsorace Anam ta ɗago tana kallon daddy, ganin shima kallonta yake ya sata maida kanta ƙasa. Aysha kam murmushi ne ya suɓuce mata, dan kuwa dama Junaid nata damunta akan hakan, itace taƙi bashi dama saboda ganin yanxu ta Yaya Maheer akeyi ba suba. “Mamana yaya dai?”

Abba ya katsema Anam dogon tunanin data tafi. Kanta ta girgiza idonta na cikowa da ƙwalla. “Abba babu komai, kawai dai….” sai kuma tai shiru.
“Kawai dai mi? Faɗi kanki tsaye kinji Mamana. Maganar aure ba maganace ta wasa ba, shiyyasa muka zaɓi baku damarku duk da hakkinmu ne zaɓa muku mazan aure matsayinku na ƴammata”.
“Tabbas babu wanda zuciyarta ta aminta zata iya tsaidawa, sai dai kuma bata iya jayayyaba, koda wasa bazata iya ƙin bin umarninsu ba dan batun yanzu ba Abie yasha sanar mata su ɗin kamar shi suke a gareta, idan har taja da su akan koma minene na rayuwa dabai zama saɓama UBANGIJI ba tamkar tayi jayayya da shine. Sannan wani ɓangaren ta sani babu abinda iyayenta ke buri a yanzu tamkar ganin tayi aure, kuma itama a karan kanta tana son taga wannan rana kamar kowace ɗiya mace duk da zatai matuƙar kewar iyayenta a kusa da ita. Abu na gaba kuma burin Abie ɗinta ta fidda miji a ƙasarsu ta haihuwa Nigeria, ta tabbata kuma hakan zaisa su dawo kusa da ita suma duk da can yafi musu kwanciya hankali fiye da nan… A hankali taja numfashi, batare data yarda ta kallesu ba ta gyaɗa kanta alamar amsa umarninsu. Daga Abba har Daddy sunji daɗin hakan, dan haka suka sallamesu akan suna jiransu.

 Gaba ɗaya Anam rasa sukuninta tayi a kwanakin da suka gabata, musamman akan wanda ya kamata ta tsayar matsayin miji a tsakanin samarin dake faman mata kaikawo su biyu. Wato Muzzaffar da Dr Jamal. Daga ƙarshe da ta fahimci zata saka kanta cikin wani hali sai kawai ta kira Mamie domin neman shawararta. Mamie uwace, sai dai ta raini tilon ƴarta da matsayi kala daban-daban bana uwa kawai ba. Shiyyasa Anam bata da wata ƙawa ko aminiya a duniya sama da Mamie, dan ko shawara zatai da Aysha ko Amrah sai ta gama da Mamie, koda abun mai nauyine a gareta tanajin kunya zata rubuta ta bama Mamien a rubuce. Yanzun ma hakan tayi, dan haka koda Mamie ta gama karantawa sai tai murmushi, Abie dake zaune a kusa da ita ta nunawa, shima dai murmushin yayi harda ƴar dariya. Ya amsa wayar yana faɗin, “Nine zan bata amsar daya dace da ita”. 

Mamie tai dariya da fadin, “Uhhm nidai naga yanda zaku ƙare a wannan rana”. Dariya kawai Abie yayi, ya tafa saƙon ya turama Anam da dama zaman jira take. Shiru tai tana kallon saƙon, zuciyarta cike da wasiwasi. Sai dai kuma a ganinta tunda Mamie tace mata yayi to itama koda son sa bai kai mata har can cikin zuciya ba zata aminta da shi kuwa watarana zata so sa da izinin ALLAH. Sai dai kuma kamar yanda Mamie tace kartai masa magana da kanta bazatayi ba, tunda dama ya jima bai zo wajenta ba bai kuma kira wayarta ba sai lokaci-lokaci sukan ɗan gaisa a chart, shima kullum cikin cemata uzirine ya riƙesa yake.

★Kwana takwas dayin wannan magana abin al’ajabi ya sauka a MD Shareff family, ba komai bane kuwa sai baiko da saka ranar Anam da Muzzaffar, Aysha da saurayinta Junaid, za’a haɗe biki tare dana Maheer.
Su Mommy kasa magana sukai dan mamaki, duk da wani sashe na zukatansu sunji tamkar an musu rahama ne, amma kuma sunajin ɗaci da zafin ganin Anam ɗin zata auri wanda shima ba baya ba, dan mahaifinsa akwai kuɗi, shima kuma Muzzaffar ɗin a karan kansa akwai kuɗin dan wani babban gwaska ne a kamfanib MTN. Duk yanda suka so kuma danne abin a rayukansu kuma kasawa sukai har saida suka haɗu suka tattauna, sai dai a ɓangaren Fadwa ranar har ruwa ta zuba ƙasa tasha. Jitai kaso talatin cikin ɗari na tsanar Anam ya sauka a zuciyarta harta kasa ɓoye hakan. Ita Anam ma data lura da ita sai abun yay matuƙar bata dariya……..✍

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button