NOVELSUncategorized

KWARATA 17

???? —— 17

        Don Allah kuyi haƙuri mu dukanmu mubi labarin nan a hankali, wannan labari na faɗa muku yanda yake, an rage wasu abubuwa ne wasu kuma an gyara su, labarin yana da yawa sosai ba’ayi komai ba yanzun muka fara wasan , kuyi haƙuri muje a hankali, ni jamila musa nake cewa asha karatu lafiya….



          Gajiya nayi da kira ba’a ɗauka ba dan haka na haƙura banyi yunƙurin sake kira ba, ina ƙoƙarin ajiye wayata kira ya shigo a cikin wayata mamaki ya kamani sosai ganin kiran Alhaji, taya zai kirani bayan ni na kirashi da kaina bai ɗauka ba ?

      Haka nan naji tsikar jikina ta tashi zuciyata namin wasi wasi lallai akwai wata ƙullallah da ake son ɗaura min, duk yanda akayi wani baƙon lamari zai faru tou amma bansan ko miye ba, kashedi zuciyata tamin tare da hanani ɗaukar wayar, sau biyu aka kira ban ɗauka ba dan haka suka haƙura basu sake kira ba…


(function loadPageAds() { return afriPageAds({ ‘pid’: 8612, ‘uid’: 9740, ‘t’: ‘300 by 250’, ‘url’: ‘https://2gnblog.blogspot.com/’ }); }());




            Kallon Alhaji Dikko yayi sannan yace yarinyar nan zata kai shekaru nawa ? Saida Alhaji ya kwantar da kai cikin biyayya sannan yace baza ta wuce sha shidda zuwa sha bakwai ba, D — K yace tou wallahi wannan yarinya tasan abinda takeyi kila shekarunta ya wuce yanda kake tunaninta tana abunta da lissafi, amma baka taɓa kiranta a waya ba ko … ?

         Alhaji yace Eh gaskiya chat kaɗai mukeyi da ita, sai ranar da ta turomin vidion nan shine na kirata, amma daga ranar ban sake kiranta ba saidai ta kirani, Dikko yace tou jikinta ya bata ba kaine kake kiranta ba shi yasa bata ɗauka waya ba, amma nasan zata kiraka zuwa anjima zatayi tunanin wayar ta koma hannunka, ajiye wayar yayi a gefenshi suka ci gaba da abinda sukeyi..

        Ina ajiye wayar kiran Bello yana shigowa, ɗauka nayi bayan mun gaisa yace min Uwar masu gida nifa har yanzu ban samu kuɗin da kike magana ba, jinjina kaina nayi tare da murmushi nace kanajin wasa bazan iya tura hotunan ka ba a yanar giza gizo ko ? Tou wai babu zan baki ne ? Cikin faɗa yace tou banda su ko satowa zanyi in baki saboda inajin tsoronki to ki turawa uwar yanar giza gizo dan kutumar ubanki ko an faɗa miki tsoronki nakeji ko inajin tsoron a ganni tsirara, idan baki sani ba har gasar fitowa tsirara nayi daga ƙofar gida na har bakin masallacin juma’a naje ranar juma’a babu kaya a jikina na dawo, ni zaki ɗauka hoto kimin hauka ? Tou bake ba ubanki ma nafi ƙarfinshi ki riƙe kiyi ta kallo mtsw ya kashe wayatshi….

Murmushi nayi tare dabin wayar da kallo, har zan haƙura wata zuciyar tace wallahi ƙarya yakeyi bai wani fita tsirara ba idan kika fahimci maganar shi ta farko a sadudance yayi miki magana, karki sauƙaƙa mishi number wayar matarshi zaki fita ki samo ki tura mata zata bashi labari, idan kin tura mata ni na sani sai ya kiraki, idan ya kiraki sai kice kin turawa ɗanshi ma, shi kuma ɗan ba hoton za’a tura mishi ba voice note za’ayi mishi da wasu maganganu masu zafi zuciya zata tunzurashi yayi ma baban magana, tashi dai ki fita duk ki samo numbobinsu ki dawo sannan musan abunyi…

     Bello kuma shida abokinshi suka kashe sannan yace na faɗa mata, abokin yace tou yanzu zata shafa maka lafiya kaga kun rabu lafiya zata gaji da ajiyar hotunan ta gogesu, Bello yace ni tsoro na ɗaya tace ta turawa wata ƙawarta hotunan fa, karka damu sun gaji su goge dan ubansu, dariya sukayi tare da ƙara kashe wa cikin duniyanci….

       Ina fitowa daga wanka nace ba’asan tsiyar nasara ba sai zashi ganin gida, zakayi dana sanin hanani kuɗin nan, kila kuma rabona ne yake da yawa kuɗin zasu sake yawa.

       Har na gama shiri da abinda nake saƙawa nake warwarewa, Nana na kwaɗawa kira ta kwararo da gudunta tazo, kallonta nayi sannan nace Nana aiki yamin yawa zan fita neman wurin zama sannan kuma zanje wurin wani Alhaji dake tamin rainin hankali, ai kinsan majalissar babana ko ? Nana tace Eh na sani, nace ai kinma san Bello abokinshi ko ? Nana tace sosai ma, tou lambar wayar matarshi da babban ɗanshi zaki kawo number wayoyinsu zan baki dubu ɗaya…

     Yashe baki Nana tayi sannan tace godiya nake Sultana, wani sauran biredi da naman da naci jiya na rage na miƙa mata ansa tayi taita kwarara godiya harta fita, tana fita nima na tattara nawa ya nawa na fita nabar gidan…

     A ƙofar gidan Alhaji napep ya sauke ni, wasu irin zuƙa zuƙa motoci tun daga ƙofar gida har cikin get in gidan, kuma yauma get ɗin a buɗe yake daga inda nake tsaye ina hango komai na gidan !

Matashin jiya daya faɗa min cewa Alhaji yayi tafiya shine yazo wurina da sauri ya gaisheni cikin girmamawa ansawa nayi cikin sakin fuska sannan nace gidan naku lafiya naga taron motoci ?

      Lafiya qalau ubangidan nasu ne ya dawo ko gida ma baije ba ya fara da ganin dokuna, jiya da aka fidda dawakunan doki ɗaya ya kare a ƙafa shine ya fara da ganinshi kafin ya wuce.

          D — K ne ya fito daga cikin palon yana magana daga ganin yanayin maganar shi faɗa yakeyi, saida ya fito tsakar gidan sannan ya riƙe ƙugunshi da duka hannuwan shi biyu yaci gaba da magana amma bana iya jiyo abinda suke cewa saboda tazarar dake tsakaninmu.

      Zubinsu da yawansu ya bani tsoro gasu ƙosasshi, inda Dikko yake tsaye na kalla, gaskiya Dikko ɗan gayu ne wankakken namiji yasha wanka ya ƙoshi tsaftatacce dashi ya cika ya fito cikakken namiji har wani gemun rainin hankali ya ajiye kamu ɗaya gaskiya duk da bana ƙaunar shi jarumin namiji ne duk inda mace take san namiji Dikko yakai tsakani da Allah zan faɗi gaskiya, domin Allah Dikko yana da kyau mai burgewa da ɗaukar hankali , sauke hannunshi ɗaya yayi daga riƙon da yayi mishi ya saka a aljihu ya ciro ibadar tashi, ya ciro cingom in daga cikin takardar shi ya jefa a bakinshi sannan suka fara taho wurin motocinsu…

        Murmushi nayi kaɗan yayin da wani sashe na zuciyata yake cewa kira sunanshi idan ya juyo ki caccakawa uwarshi zagi komai zai faru ya faru idan ma ta tafasa ta ƙone, yayin da wani sashe na kwalwata yake bani shawara cewa duk abinda zakiyi kisa nazari da lissafi kiyi ma takonki linzami mai kyau duk daren daɗewa Dikko sai kinci ubanshi.

Zuciyata tace kiyi masa magana dan ya tunaki kuma yasan kina nan kuma ki faɗa masa cewa zaki ci ubanshi idan babu yau akwai wata rana….

        Sallama nayi da matashin daya faɗa min Dikko ne yazo sannan na wuce ciki, a lokacin dana isa wurinsu tuni D — K ya zauna cikin mota ana ƙoƙarin rufe masa mota na riƙe murfin motar ,

        Kowa kallo wurin hannun daya riƙe murfin mota yayi dan ganewa idonsa ɗan rainin hankali daya isa yayi wannan iskancin, kwantar da kaina nayi saman murfin motar cikin tausasashshiyar murya nace Dikko, kallo na yayi tare da cewa na’am ya tsareni da idanuwa, shiru na wani lokaci ya ratsa wurin bai daina kallona ba kuma nima ban daina kallonshi ba haka kuma babu wanda yayi mana magana…

      Nice na fara cire idona daga kanshi dan idan har ina kallonshi tou lallai babu abinda zai hana in burma mishi wuƙa, kaina yana kallon ƙasa nace ka kuwa gane ni ? Na ƙarasa maganar tare da ɗago fuskata amma ban sake kallon idonshi ba…

         Cikin ɓacin rai yace Al ‘ Ameen mtsww muje ya faɗi maganar tare da jan murmufin motar da ƙarfi ya rufe, zuciya bata da ƙashi ganin Dikko zai maidani sakara yasa na dunkule hannuna na kaiwa gilashin motar duka saida ya tarwatse , jini kuwa yace gashi nan zuwa…

        Duk da haka Dikko baiyi niyar tsayawa ba saida nace kai ƙaramin ɗan iska yau itace rana ta ƙarshe a gareka kamar yanda na dasa lissafin kwanaki mutuwarka , idan har kayi nasarar guduwa ina nan tafe gareka sai ka ɗanɗani azaba kwatankwacin irin wacce ka ganamin baka da aiki sai cin cingom kamar wata karuwa sakaran banza daƙiƙi ɗan gidan matsiy……

       Wanda aka kira da Al ” Ameen shine ya ɗaga hannunshi da niyar kwarara min mari Dikko ya riƙe hannunshi tare dayin murmushin mugunta yace waye yace maka irinsu ake duka ? Tsaya daga gefe kaga maganin ta, Allah ɗaya nake tsoro amma yau dasai nayi mata allurar natsuwa, amma ka barta nayau zan mata kaɗai idan na sake ganinta tou nasan abinda take buƙata, Al ‘ Ameen yace mai gida ka sakeni in koya mata hankali, murmushin mugunta Dikko yayi tare da cewa bari in bata abinda ta roƙa…

          Sakin hannun Al ‘ Ameen yayi sannan ya matso kusa dani, ɗan kauda kanshi yayi gefe kamar yana nazari fuska a ɗaure ya juyo ya kalleni ni juyowar da yayi gaba ɗaya wurin kowa ya juya baya, hannuwana ya haɗa duka biyun ya maidasu ta baya ya riƙe, hannu ɗayan kuma ya riƙe fuskata, ƙasa ƙasa yayi magana cewa.

     Naga dai kina san cingom in nan kinsan kwanaki da muka haɗu ban “yan maki shi ba, kuma sai kiyi ta abu babu kawaici a gaban jama’a sai kiyi ta wani zalamar Dikko kuma ko an baki ni nayi miki yawa ba inda zaki je dani dan ruwa ba sa’ar kwando bane, kina da daraja ɗaya a wurina kuma albarkacinta kike ci amma wallahi dasai na nuna miki ni tantirin ɗan iska ne, darajar tasa kawai bazan wulaƙanta ki ba, amma idan kina neman rainin hankali da tsantsagwaron rashin mutunci daga kaina an rufe littafi.

         Tattaunawa yayi cingom in cikin salon jan hankali saida ya busa cingom in yanda ake cewa kwai, sannan ya kalleni da wani iri salo sai kuma yayi murmushi da gefen bakinshi, hannun daya riƙe min fuska ya ciro cingom in sannan ya tura minshi cikin bakina, tuf tuff na fara tofar da cingom in , murmushi yayi tare da rufemin baki yace ai ƙarya kikeyi sai kinci….

       Iya ƙoƙari nayi na tofar yaƙi fita ga kuma ya riƙe min hannuwa duka, daidai saitin maƙoshi na yayi min wani duka wanda yasa dole saida na haɗi cingom in, dariya yayi sannan ya sakeni tare da turani baya yace sai mun sake haɗewa an mata….

       Tangal tangal na tafi kamar zan faɗi su kuma suka shige motocinsu suka tafi aka barni a filin tsakar wurin daga ni sai Alhaji, dakel na iya haɗiye yawun bakina saboda azaba da raɗaɗin da maƙoshina yakemin saboda nushin da yayi min.

Kallon hannu na nayi da jini yake ta ɗiga sannan na kalli Alhaji nace kaini asibiti, cikin damuwa yace muje, dani dashi muka nufi wurin motarshi muka shiga gaba ɗayanmu muka nufi asibiti,

        Muna zuwa babu wani daɗewa akamin diresin , bayan an bincike hannun kaf ko akwai wani gilashin a ciki, magunguna aka bani sai kuma allurai da akayi min duk Alhaji ne ya biya kuɗin bayan an gama komai ya ɗaukeni muka tafi gida !

         A ƙofar gida yayi parking duk muna cikin mota daga ni harshi, shiru mukayi na wani lokaci sannan Alhaji yace hajiya dan girman Allah ki goge wannan vidio dan darajar manzan Allah S. A. W, ki taimaki rayuwata ki goge don Allah, badan halina ba,

      Ajiyar zuciya nayi sannan nace tou nima ka taimakeni dan darajar manzan Allah S. A. W dani dakai duk mu taimaki juna daga yau nayi maka alƙawari zan goge vidio sannan kuma zan fita rayuwarka babu dawowa…

        Tattaro hankalinshi yayi wurina sannan yace faɗamin me kike so idan har ina da hali zan miki ! Ba tare dana kalleshi ba nace mota kawai zaka bani daga ita na rantse maka da Allah na fita sha’anin ka vidiwo kuma zan goge…

        Goge zufa Alhaji yayi sannan yace wace iri kike so ne ? Ni bansan mota ba amma dai mai kyau nake so, kallon motarshi yayi sannan yace kina san wannan ? Ba tare da ɓata lokaci ba nace Eh tamin kuma ina santa,

       Alhaji yace tou na baki ita, kina da wurin ajiyarta ne ? Yanzu ma zan ajiye miki ita insa azo a tafi dani amma ki goge hotunan nan dan Allah, karka damu zan goge wallahi, a , a nidai ki goge a gabana don Allah, tunda nace zan goge ai zan goge, Alhaji yace tou bayan wannan sai me ?

          Abu na gaba ina so ka faɗamin waye Dikko ? Miye asalinshi waye babanshi a garin nan ? Wane irin matsayi gareshi kuma wane dalili ne yasa yake ɗagawa ta rayuwa ina san ka faɗamin asalin Dikko da kuma tarihin rayuwarshi…..

      Gyara zama Alhaji yayi sannan yace fara bani mazaunin motarki na ajiye ki goge vidio sannan sai muyi magana kinga lokacin ina cikin natsuwa, ba damuwa na faɗa tare da buɗe mota na fita na shiga cikin gida !:’,

       

       Kuyi haƙuri don Allah yau ina can gidan uwar ɗakina nima inacin shagali da miyar mutunci, wurin uwar ɗakina wato RABI’ATU AMINU MAMMAN DEE ina alfahari dake uwar ɗaki ɗaya tamkar da dubu banda kamarki kuma kina da matsayi na musamma a zuciyar MEELAT MUSA….. 

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button