Labaran Kannywood

Cika shekara 14 da aure: Ba mu taɓa kai ƙarar junan mu ba – Lawan Ahmad

JARUMI kuma furodusa a Kannywood, Lawan Ahmad, ya bayyana cewa shi da matar sa Saratu Abdulsalam ba wanda ya taɓa kai ƙarar wani gidan su a cikin shekara 14 da su ka yi tare.

Lawan Ahmad tare da Matarsa

Ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke tattaunawa da mujallar Fim kan farin cikin sa game da cikar su shekara 14 da aure a yau Talata, 25 ga Oktoba, 2022.

 

Lawan dai ya wallafa hoton sa tare da maiɗakin nasa a yau domin murnar cikar su shekara 14 cif da aure.

 

A bayanin da ya yi wa mujallar Fim, jarumin ya ce, “Alhamdu lillah, abin farin cikin ma shi ne da har Allah ya sa cikin hukuncin Ubangiji mu ka kawo har shekara 14 tare, kuma ba tare da wani daga cikin mu ya taɓa kai ƙarar wani gidan su ba. Mu na zaune da daɗi, babu daɗi har mu ka kai tsawon shekarun nan.

Lawan Ahmad

“Lallai ba ƙaramin abin alfahari ba ne, kuma ba ƙaramin abin godiya ba ne ga Allah har da mu ka yi wannan tsawon lokaci, kuma ana zaune lafiya. Gaskiya na yi farin ciki ƙwarai da gaske.”

 

Kasancewar Lawan ya na daga cikin ‘yan fim ɗin da ba a taɓa jin kan su tsakanin sa da matar sa ba, amma wasu na ganin cewa ‘yan fim ba su iya riƙe mata, me zai ce a kan haka? Sai ya ce, “Ai babu wanda ba ya zaman aure. Da ma shi aure idan an yi shi, kuma akwai saki, wanda a addinance ma haka ne, kuma kowa ya riga da ya sani.

 

“Sannan abin da ya sa ake ganin kamar ‘yan fim ba su zaman aure, su abin su komai a buɗe ya ke.

 

“Ka ga kamar yadda ka yi min magana, in wani ne ba ka ma san ya yi ‘posting’ ba, amma yadda ka ga na yi ‘posting’ ka ga yadda mutane ke ‘reposting’, ka ga ya dace ka kira ni, mu yi magana a kan ‘posting’ ɗin da na yi. Mu abubawan mu ne a buɗe su ke, tunda an riga da an san ‘yan fim.

 

“Amma da mutane za su riƙa la’akari da za a yi saki miliyan ɗaya a rana ɗaya, amma idan ɗan fim ɗaya ya yi sai ka ga duniya ta ɗauka, saboda mu an riga an san mu ne. Kamar mutuwa ne, idan mutum ɗaya ya rasu a cikin ‘yan fim sai duniya ta ji. A kullum iya Jihar Kano kaɗai za a rasa sama da mutum dubu goma, ka ga su ba a san su ba.

 

“Wannan wani abu ne da Ubangiji ya ƙaddaro mana da shi kenan; ko ya aka yi abu sai ka ga an ji, bayan kuma ba mu kaɗai ne ke aure mu yi saki ba, ba mu kaɗai ke mutuwa ba, ba mu kaɗai ke bikin suna da sauran su ba. Haka rayuwar tamu Allah ya ƙaddaro mana ita, sai dai mu yi ta haƙuri kawai.”

 

A kan batun ko ya na da burin ƙara aure a nan gaba, Lawan ya amsa da cewa, “Ai ka san shi aure zuwa ya ke yi; ko mutum ya yi niyya ko bai yi niyya ba, in Allah ya ƙaddaro maka za ka yi. Don haka ba mu da wani zaɓi sai abin da Allah ya zaɓa mana.”

 

A yanzu ‘ya’yan Lawan da Saratu huɗu ne, wato Ahmad, Aliyu, Faɗhima da Habiba.

 

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button