Uncategorized

YAU DA GOBE 13-14

 ????????????????????????????????????

  ????YAU DA GOBE ????

????????????????????????????????????????

Story & writing by mmn fareesa

????️13&14

…..Wata irin zabura hjy jamilah tayi”Afusace tace danaga wannan ranar gara naga mutuwar Sadiq!natsani Maryam da y’arta”sbd kaf zuriyarmu bbu wacce akama kishiya sai ni”ta mallakeka shima d’ana ya auri y’arta su mallake munshi ko?”hakan bazai tab’a faruwa ba ko byn raina.. tafad’a tana kallonshi ido cikin ido”Abba yyi murmushi me ciwo. kafin yace banyi mamakinkin jin wa an nan maganganun dg bakinkiba”inaso kisani Sadiq nine mahaifin sa dake dashi duk Kuna a k’arkashin ikona! sannan kicigaba da nunawa Maryam k’iyayya karki fasa….katsesa tayi da cewa wlh !wlh!!wlh!!! Muddin ka kafe akan ya aureta to Zan tsine Masa albarka”Koda kuwa aurena ayanzun zai mutu…cike da mamaki Abba kedubar umma”sbd beyi zaton

wannan kalmar dg bakinta ba…tashi yyi tsaye fuska asake yace duka abinda kika lissafa bazai faruba!Zaki zauna gdn aurenki sbd y’ayanki”Sadiq Kuma bazai auri sumayya ba”saidai inaso kisani hassada gamai rabo takice! sumayya zata mallaki mijin dayafi Sadiq insha ALLAH Kuma saikin ciji yatsa inhar kikaga Wanda zata aura….hmmmm Allah ko?”yo saime tunda anraba d’ana da jaraba Allah natuba”tunda tayi kwantai dole atura mishi ita… murmushi Abba yyi yace sumayya shekaran ta 20″ jidda 23 acikin su wayayi kwantai?”jamilah sai yaushe Zaki canzane?”to Bari bari kiji Sadiq shiyazo dakansa yace sumayya yakeso”na b’oye mikine sbd nasan halinki” amma ba cusa Masa ita nayiba koki yarda ko karki yarda”inbacin wasu dalilai dasai ta kammala karatunta za’ayi aurenta…tabe Baki hjy jamilah tayi had’e da cewa can matsalar suce “d’ana yamata nisa wlh….girgiza Kai kawai Abba yyi yafice parlourn yabar Mata abincin ta data kamishi…Yana fitowa “hjy jamilah ta nufi part d’in su sumayya sbd akan idonta Abba yahau mota suka fita da driver…



“””Babu ko sallama hjy jamilah ta kutsa Kai cikin parlourn”sumayya da Sadiq na zaune Yana koya Mata yadda zatayi amfani da wayarta”ba shakka wlh!hjy jamilah tafad’a tana watsa musu mugun kallo dg Sadiq d’in har sumayya”

     Inna lillahi wa inna ilaihir raju’un… sumayya ta fad’a aranta”Sadiq kuwa gabansa yyi mugun fad’uwa”munafiki Ashe kana nan dama ko?”nan kake zuwa Koda yaushe ni Ina zaton kafita”to wlh Kama sani kasake zuwa part d’in  nan dasunan Kai ka aiko kanka ba mahaifin ka ya aikokaba banyafe maka ba?”

     Tafada tana kallon sumayya tace ke Kuma algunguma keda uwarki dangin matsiyata kinyi kwantai za’a likama d’ana ko ?”to yafi karfinki”bazan had’a zuri’a da matsiyata irinku ba”wadanda talauci yyima kanta…ko kunzata bansan har wankau da dakau uwarki tayiba sbd talauci…Dan ALLAH umma kiyi hakuri bazan koma shigowa ba muje Kar Abba yazo Dan ALLAH”bazan tafiba sai minafikar uwarta ta fito namata kashedi… sumayya na kuka ta tashi tashige bedroom d’in mama sbd tasan maman najin duk rashin mutun cin da hjy jamilah ke musu…tsaki hjy jamilah tayi cikin d’aga murya tace ai wlh Allah yataimake ku ba part d’aya mukeba dako ruwa bazaku shaba”y’an iska matsiyata”Kuma gd gaku gashi”badai kinyi ciki ba sbd gado zanyi maganinku daga ke har alh..Sadiq rufe idonsa yyi cikin b’acin Rai da wani yanayi”aransa Yana jin da ana canza uwa da yacanza wlh…zaka wuce muje ko kuwa inma asiri suka maka wlh dg yau ya karye.. tafad’a tana kallonshi suka fice dg part d’in…



Mama kuwa duk abinda hjy jamilah tayi tsab taji”bakuma tsoronta yasakata k’yaletaba”tabarta Kiran lokaci”da Kuma jikin dake cikinta”sannan ta fahimci tabbas da  Sadiq Abba keson had’a sumayya”inkuma har yasanar Mata gsky bazata aminceba sbd halin uwarsa”amma bazata Masa maganar ba”kallon sumayya dake kuka tayi tace kiyi hakuri kiyi shiru komai na duniya yanada lokaci”YAU DA GOBE in ance tamana hakan bazatayi ba”d’anta kuwa koshine autan maza bazaki auresa”komai yafaru da bawa sumayya Yana cikin k’addararsa!

Share hawayenta Sumayya tayi tana tunanin yaushe zasuyi farin ciki itada mamanta?”sannan tana tunanin kodai Abba aura Mata Sadiq zaiyi sbd gudun karta auri muttala…mama ta katse Mata tunani Gurin cewa kije ki d’auki alk’ur’ani Mai girma ki k’aranta Zaki samu nutsuwa insha ALLAH.

    da to sumayya ta amsa tana tashi…




????????????????????????


Abba kuwa suna fita yace wa driver yakaishi gdn hjy Aysha…byn sun iso angama gaisawa Abba yyi guran murya had’e da cewa hjy nazo da wata mgn dakuma neman shawarar ki amatsayin ki na uwa ga Aliyu!ummi ta gyara Zama had’e da cewa to alh inajinka”Abba yace inaso na had’a Aliyu da sumayya y’ar amaryata aure”sbd wasu manyan matsaloli dasuka taso tsakanin yarinyar da dangin ubanta”har suna k’ok’arin zuwa su karb’e ta dg gun mamanta”sannan nayi tunani yarinyar nan dasuke tare da Aliyu ubanta yacika izzah tamkar bayasan bashi”yanzun Aliyu yakamata ace yanada iyali ,Amma sai yawo da hankali suke Mana”inhar Aliyu zaimun biyayya ya auri sumayya kodaga baya sai ya auri ita waccan din”amma wlh banison ganinsa hakan bbu iyali…ajiyar zuciya ummi tayi tace Masha Allah!alh Ina bayanka d’ari bisa d’ari”sbd wlh tunda na aza idona akan yarinyar nan naji tamun yarinyar ta”saimuyita adduar abinda yafi alkhairi…baki washe Abba yyi murmushi had’e da cewa ameen hjy”sbd dama yasan hjy Aysha nada sauk’in Kai”ummi tace to amma alh ga shawara”dama babana baya gdn bejimaba da fita kazo”in yadawo zance kazo kace yaje kanason ganinsa”inyazo saika fad’a Masa”banason yaji ta bakina”zai iya musawa “amma inyazomun da maganar Zan nuna hakan nada kyau yyi hakuri  yamaka biyayya” 

Abba yace hakan yyi insha Allah inyazo aturo munshi”ummi tace to alh amma yarinyar baza’a Sami matsala agunta ba ko?”eh gsky sbd insha Allah zatayi biyayya tanada hankali sosai…to shikenan Allah yashige Mana gaba.nan sukayi sallama…



 ************


Fitowa yyi dg bath room d’aure da towel sai wani rataye awuyansa Yana goge ruwan jikinsa”yanufi gurin mirror”agaggauce ya shirya cikin jallabiya milk yanufi masjid !sbd inyadawo zaije gdnsu rukky kwana2 su gaisa sbd bayason tana zuwa asibiti gurinsa Yana aiki..Koda yadawo shiryawa yyi cikin wata dakakkiyar shadda Fara k’ar ,riga iya gwiwa amma aiki da bakin zare”ya aza hula baka da takalmi sawu ciki… hmmmm Masha Allah duk budurwar data ganshi dole yaburgeta kota k’yasa…lolx sai k’amshi ketaji ajikinsa “SAFANA badai iya wanka ba”kyansa yafito sak abaka nensa…agogon dake daure atsintsiyar hannunsa yaduba yaga 8:12 pm yasaka “yafito yarufe parlourn sa”yanufi cikin gdn…zarah naganinsa dukda tana cikin damuwa saita tuna da musty”murmushi tayi had’e da cewa Kai Yaya wannan zazzafan wankanfa?”murmushi yyi yace kin rainani ko baby?”hmm Yaya Gurin anty rukky zakaje ko?”kafin yace wani abu ummi dake kalonsu tace “tun d’azun nike jiran shigowarka “nazata byn magarib zaka shigo! Dr safana yace eh ummi nagajine sai kawai na wuce ciki”Zan fita adafamun shayi innadawo zansha…

Ummi tace to shikenan! amma duk inda zakaje kafara zuwa gdn abbanku yazo d’azun da marece yanason ganinka…hakan kawai safana yaji fargaba akan Kiran”azatonsa ko kan maganar daya masane kan yabashi 3 month yafito da wacce yakeso…

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button