Comment on AUREN KWANGILA Page 81 to 90 by Unknown
Ashraf ne da sadeeq cikin mota suna kan hanyarsu ta dawowa daga sallar jumu’a.
Sadeeq ne ke tuqi while ashraf na danne danne a waya.
Sosai ya shagala da abinda yake a wayar don bema lura da sadeeq ya dauki wata hanyar ba saida sukayi nisa sosai sannan ya ankara.
Kallon waje yayi yana yatsine fuska sannan yajuyo ga sadeeq yace
“And where are you taking us to?”
Ta6e baki yayi yace “sai yanzu ka lura”
“That’s not the answer to my question” ashraf ya ansamashi yana harararshi
“Inda kake complaining ina zuwa zan kaika kaima” sadeeq ya amsa mashi yana shan wata corner
“Ina kenan?” Inji ashraf
“Gani ya kori ji” inji sadeeq batareda ya kalleshi ba.
Be sake cemashi komaiba sai maida hankalinshi dayayi kan wayarshi yana scrolling information on *how to make a girl fall for you* dayayi browsing.
Jin tsayuwar motarsu ya dawo dashi daga duniyar karatun daya lula, ajiyar zuciya ya sauke sannan ya dago idanunshi daga kan phone din yashiga bin inda suke da kallo cikin mammaki.
“Ina ne nan?” Yafada still yana bin harabar da kallo cikin mammaki
“Idanunka sun fara ciwone halan?” Inji sadeeq yana bude murfin kofar sannan yafita.
Shima fitowa yayi yana qara bin environment din da kallo.
“Waye be lafiya?” Inji ashraf yana kallon sadeeq
“Kaidai muje” inji sadeeq yana yin gaba.
Maida wayarshi a aljihu yayi sannan shima ya maramashi baya yana wondering waye be lafiya aka kwantar dashi asibiti.
Saida suka biya office din wani Dr sannan suka fito gabadaya da Dr din suka nufi wani ward, shidai ashraf binsu kawai yake batareda yasan wazasu je ganowaba.
A bakin wani ward suka tsaya Dr din yabude kofar yashiga sadeeq yabishi sai lastly ashraf da shima ya maramasu baya very eager to know what’s happening.
Daga farko be dago wacece ba saida yakusan kaiwa bakin gadon sannan ya ganeta wanda hakan yasashi tsayawa cak daga tafiyar dayakeyi yana kallonta.
Itama kallonshi take agalabaice da alamu dai tana jin jiki ga wasu hawaye dasukayi forming a idanunta dasuka fada ciki.
Juyawa yayi batareda 6ata lokaciba ya nufi hanyar fita don baxai juri ganintaba don zuciyarshi wani irin suya take.
“My…. my please don’t leave…please” tafada cikin muryar kuka.
Beko saurareta ba ya cigaba da tafiya harya isa bakin kofa yakama handle zai bude yaji tace
“Please don’t leave without forgiving me, nasan mutuwa zanyi, please forgive me” tafada cikin kuka sosai.
Tsayawa yayi hannunshi kan handle din kofar batareda yajuyo ba.
Ganin hakan yasata cigaba dacewa
“Am so sorry my… na cuci kaina, beebah ta cuceni, nabiyewa son zuciya da hudubar muguwar qawa nafada hallaka, please forgive me”
Shiru yayi yana sauraronta zuciyarshi na zafi, duk ya tuna kazafin dataje tayimusu wajen ummy saiyaji kamar yaje ya shakureta a inda take.
Cikin sheshekar kukan dabai fita tacigaba dacewa
“Ashe beebah ba masoyiyata bace? Ta kaini ta baro, A.A nasan bani cikin mata masu kyawun hali, nasan bana cikin masu isashiyar tarbiyya.
Ashraf nasan kasoni ada, kasha yunkurin nunamini hanyar gaskiya amma nayi wasa da damata na 6ata wayauna na biyewa rudin qawaye da rayuwar turai na lallata alaqar dake tsakaninmu.
Ashraf tunda nafara ganinka a uk nakamu da matsanancin sonka wanda hakan yasa naji idan ba kaiba babu wanda zan iya rayuwa dashi amatsayin mijina.
Hakan yasani tattalin kaina da mutuncina don kai ganin kai kamili ne.
Duk iskancina ban ta6a wuce romance don nasa a raina kai kadai zanba kaina saboda na samama kaina mutunci awajenka bayan aurenmu.
Ranar daka ganni da chris muna kissing har hakan yayi sanadin rabuwarmu, aranar nashiga tashin hankali sosai kuma nadama tashigeni amma na nade tabarmar kunyata da hauka don ganin zan wulaqanta a idanun jama’a.
Daga lokacin natuba daga romance life saidai kaqi kabani wani damar.
Nabi duk hanyar danasan zanbi inshawo kanka amma kaqi saurarata.
Alokacin da labarin aurenka ya riskeni na shiga tashin hankali sosai.
Tun a lokacin naso tada bori amma beebah ta hanani acewarta asannu zamu warware komai.
Na biyemata nakuma yarda daita saboda duk duniya banida qawa kuma aminiya data fita.
Ita tayi convincing dina takaini wajen wani boka da nufin shiga tsakaninku kai da matarka yakuma cusa maka tsananin sona yadda zakaji bazaka iya rayuwaba batareda niba”
Shiru tayi sakamakon kukan dayaci qarfinta.
Izuwa yanzu ashraf yajuyo yana kallonta ya jingina da kofa hannayenshi harde da qirji shima sadeeq ita yake kallo shima jingine da bango.
Babu wanda yacemata uffan har taci kukanta mai isarta sannan ta tsagaita don kanta sannan tacigaba dacewa
“Bansan wannan ne hanyar lallacewar rayuwata ba, bansan kaini zatayi ta baro ba.
Ataqaice dai the man demand for my virginity domin samun biyan buqata ta.
Dafarko naqi yarda don banga amfanin auren ba bayan nayi loosing din abinda zai kankaromin mutunci awajenka ba amma sai sukayi convincing dina dashi da beebah cewa aikin da za’ayimaka bazai baka damar tantance am virgin or not ba, kawai dai burinka a lokacin ka mallakenine kuma bazaka ta6a barinaba har abada.
Ina sonka kuma banida burin daya wuce in mallakeka na har abada hakan yasa magangannunsu sukayi tasiri azuciyata nabada kai”
Sniffing tayi ahankali sannan tacigaba
“ranar nayi loosing pride dina ga dirty tsohon nan, nayi kukan takaici sosai saidai beebah na kwantarmin da hankali cewa yanzu you’re mine forever.
Shiru shiru har aka kwashe wata banji alamun nasaraba saima canjin danakeji ajikina cos am always sick.
Hakan yasa na tsare beebah da qorafi nan ta kwantarmin da hankali tareda cemin akwaima hanya mafi sauqi dazamu warware aurenku batareda munjira bokanmu ba.
Nan tagayamin tasamu information awajen helen cewa aurenku is based on contract.
I was shocked alokacin don abin yazomun a bazata, nan na buqaci evidence tace tasa helen tasamo mana akan yarjejeniyar huge amount of money.
Hakan yasa nadanji dama dama saidai me? Bayan kwana biyu jikina yayi worsening.
Dakyar na iya kai kaina hospital inda aka gwadani aka bani result din daya giggita rayuwata.
Result ne na juna biyu wanda ya nuna inada jaririn ciki sai kuma cutar nan mai karya garkuwar jiki wato HIV/AIDS.
Ina gama karantawa na yanke jiki nafadi saidai nasake bude idanuna naganni akan gadon hospital.
Nayi kuka sosai nayi baqinciki marar misaltuwa.
Qarshe dai na lalla6a dakyar nakai kaina gidan beebah.
Sosai na burkuce mata don gani nake tawa tazo qarshe kawai.
Dakyar ta rarrasheni ta nuna haryanzu is not too late wajen mallakarka, ta fiddomin takardun datasamu wajen helen na yarjejeniyar aurenku takuma kitsamin yadda zan maku makirci wanda dolene umminka tasa ka aureni
Banida za6i, a lokacin banida kingin burin daya wuce in mallakeka kafin inmutu hakan yasa nazo har gidanku nayi maka kazafin danayimaka.
Bayan wannan ranar kuma zazzafan zazza6i yakuma lullu6eni ga laulayi daga qarshe beebah tabani shawarar terminating din cikin.
I dont have choice don alokacin inajin jiki sosai haka takawoni wannan asibitin don zubda cikin.
Wanda garin zubda ciki akasamu matsala mahaifata ta ta6u.
Tunda takawoni hospital yau kwana goma kenan ban sake ganinta ba, ina cikin matsanancin hali gashi tagudu tabarni, banida kowa, bansan ta ina zanfara contacting din yan uwana ba.