Uncategorized

Comment on AUREN KWANGILA Page 81 to 90 by Unknown

Sallamar megadi ne ya katsesu.

Duk kallon kofar sukayi harda mamy da tagama wayar sai danne danne datakeyi.

“Habeeb get the door” inji mamy tana maida kallonta akan wayarta.

Tashi yayi yawuce yayinda saudart ta ciro wayarta zata shiganma abdul game din ludo kamar yadda yace.

Adan jima kadan saiga habeeb yadawo dakin.

“Mamy baqine” inji habeeb

“Who?” 

“Don’t know sundaice inzo ince zasu shigo gaidaki”

Kallon juna saudart da mamy sukayi sannan mamy tace “ok saudart jeki daukomin mayafi na, abdul tattara rubbish takardun nan kayi sama”

Tashi saudart tayi tanufi upstairs dakin mamy while abdul ya tattara takardun games din hannunshi riqeda wayar saudart dayake game daita.

Can saiga saudart da mayafin mamy ta bata tajuya takoma sama abinta.

Kallon habeeb tayi dake tsaye tundazu bayan tagama yafa mayafin tace

“Jeka shigo dasu”

“Tou” yafada yajuya don shigowa dasu din.

Ajikin motarsu ya taddasu tsaitsaye, qarasowa yayi yana murmushi yace

“Mamy tace kushigo”

Shafa kanshi sadeeq yayi yace “alright good boy muje”

Habeeb yayi gaba sadeeq yabishi.

Saurin kamo hannunshi A.A yayi yana wiqi wiqi da idanu kamar marar gaskiya.

“What” inji sadeeq daya juyo yana kallonshi cikin takaici.

“Please sadeeq, am shy” yafada cikin marairaicewa

Tsaki sadeeq yaja cikin takaici yace

“You know what? Idan najuya nabar gidannan natafi kenan wlh, wannan wane irin wulaqancine, ka tilastamani rakoka kuma kazo kana behaving annoyingly? Haka kabani kunya wajen daddy agidanshi dazu, kasan bazaka iya zuwaba ka jiji6oni?” Yafada yana harararshi

“Mtcheew yanzu am sorry muje, wai maimakon ya kwantar ma mutum hankali saiya rufe mutum dafada” 

“Hankalin ya dade be tashiba, yafi rocket tashi” inji sadeeq.

Wuceshi ashraf yayi cikin fushi yanufi habeeb da harya kai bakin kofa.

Binshi shima sadeeq din yayi yana harararshi yana gunguni qasa qasa.

Koda yakai bakin kofar kasa shiga yayi saida yajira sadeeq ya iso sannan.

Harara sadeeq ya gallamashi sannan yasa hannu yatura kofar ahankali yana sallama.

Shima ashraf daduk yake very nervous ya maramashi baya shima yana sallamar.

Akan kujera suka tadda mamy zaune fuskarta asake tana amsa sallamarsu tareda yimusu sannu dazuwa.

Ahankali suka qaraso cikin falon kansu a sunkuye suka zauna kan carpet suna fuskantar mamy.

“A’a? Ku zauna kan kujera mana” 

Duk murmushi sukayi kansu a sunkuye suka shiga gaidata batareda sunyi yadda tace dinba.

Amsa musu tashigayi tana kallonsu most especially ashraf don kallo daya tayimusu tagane kosu waye.

“Ya mutanen gida? Ya aiki?” Inji mamy

“Alhamdulillah, yasu Abba” inji sadeeq yana murmushi shikau ashraf kunya ta hanashi cewa komai sai sunkuye kai dayayi kawai yana sauraronsu.

Amsamasu tayi da yana wajen aiki be dawoba.

Saida suka gama gaishe gaishen sannan mamy ta tashi tsaye ta kalli habeeb dake zaune can gefe yana qoqarin chanza channel ta 6allamashi harara a fakaice tace

“Zoka kaisu falon baqi”

Tasowa yayi yazo wajensu ya tsaya, tashi duk sukayi suna yimata sallama tana amsawa cikin fara’a tanacewa su gaidamata Hajiya fateema idan sun koma sannan itama tajuya tahau sama bayan sunfita.

Wani gauron ajiyar zuciya ashraf ya sauke bayan sun fito yana dafa chest.

Harararshi sadeeq yayi yace “matsoraci kawai”

Shima hararar ya rama batareda yace komaiba sukabi habeeb dake gaba don kaisu falon baqin.

Kwankwasa kofarta da akayi yasa tadago daga linkin kayan datake, kafin tace komai har mamy ta bude kofar tashigo.

Murmushi saudart tayi mata tace

“Har baqin sun tafi?” Tafada tana ajiye zanen data linke.

Fuska ba yabo ba fallasa mamy tace

“A’a kije suna falon baqi and kitafi da refreshment”

Dan waro idanu saudart tayi tace

“Nikuma mamy?” Tana nuna kanta da yatsa.

Wata harara mamy ta gallamata tace “no ni, zakiyi abinda nacene ko kuwa? And change into something more decent kuma karkiyi wasting dib time” tana kaiwa nan tafice tabarta sake da baki.

Asanyaye ta maida kayan data linke cikin sip dinta sannan taciro wata dark blue din hijab doguwa ta dora kan kayan jikinta tadan gyara fuskarta ta fesa cool turare sannan tafita.

Bata tadda kowaba falo hakan yasa tanufi kitchen tadauki tray ta bude fridge tafiddo drinks uku ta daura akai da cups ma uku don batasan adadin baqinba ta debi snacks ma sannan tafito kitchen din tanufi falon baqi.

Tafiya take tana tunani nason gano su wanene, haka kawai taji beating din zuciyarta na chanzawa. She feels very nervous and uncomfortable.

Koda takai bakin kofar saida tadanyi jimm na yan daqiqu sannan ta daga hannu ahankali tayi knocking sannan ta tura kofar bakinta dauke da sallama.

Sadeeq kadai ya amsa sallamar while ashraf da muryarta ta saukar mashu da wata iriyar kasala ya kafe kofar da idanu cikin son ganin ta inda zata 6illo.

Anitse tashigo dakin kanta qasa tana sake maimaita sallamar datayi hannunta riqeda tray.

Lumshe idanu ashraf yayi akanta ya bude jin wani sanyi na ratsa zuciyarshi by the mere sight of her…✍

Ummin fasihu????????‍♀️????????????????AUREN KWANGILA????????????????

(Contract marriage)

085

Tun daga wannan zuwan ashraf yasamu ticket din zarya gidan mamy.

Every two days saiya biya gidan duk don ya ganta yaji sanyi, wani lokacin ma daga office zai biya gidan yaganta sannan yawuce gida.

Shaquwa sosai tashiga tsakaninshi da qannen saudart musanmman abdul don mafi yawancin lokuta dashi take zuwa falon baqin tasameshi susha firarsu itakau daga gaisuwa bata qara uhm bare uhm uhm.

Zaryar da ashraf keyi gidan ba qaramin haushi yakebata ba don gani take duk salon takura ce, babu abinda yafi bata haushi kamar maidata t.v dayakeyi tsabar kallo shiyasa daga baya ta tsiri fita da abdul don taji sauqin kallon ko yaya ne.

Messages kau tun yana turowa tana gogewa har ta haqura ta share don wasu bata ma budesu, bataga amfaninsu ba don basa qarar daita da komai, shikau a 6angarenshi be ta6a sarewa ba ya maida abun dialy route dinshi dukda be ta6a samun reply ko sau daya ba.

***

Yau saturday, tunda ta tashi ta yanke shawarar yau saitaje saloon ayimata retouch daga nan tawuce supermarket tadanyi sayayya.

Tunda tadawo gidan mamy bata qara fitaba sosai takeson fitan nayau koba komai zata dan motsa kafa.

Fitowa tayi daga bathroom qirjinta daure da farin towel iya gwiwa kanta sanye da net cap.

Kallo daya zaka mata kasan wanka tafito duba da yadda glowing jikinta ke jiqe da ruwa. Gashin hannunta gaban goshinta duk sun kwanta luff sanadiyyar ruwan daya jiqasu.

Gaban mirror ta nufa tana gyara daurin towel din qirjinta.

Tsayawa tayi tana kallon kanta a mirror ganin yadda skin dinta ya chanza sai glowing yake.

Murmushi tadanyi sannan ta dauki man shafanta ta shafa tadanyi simple makeup sannan ta saka riga da skirt na atamfa ta yafa veil tafita.

Direct dakin mamy tanufa don tasan tana ciki, su abdul kau ana islamiyya kasancewar weekend idan suka tafi tun safe sai shidda na marece suke dawowa.

Tadda mamy tayi tana gyara gadonta hakan yasa ta ida shigowa tana sallama.

Amsawa mamy tayi batareda ta dagoba har tagama gyaran gadon sannan ta juyo ta zauna tana kallonta.

Zama itama saudart tayi kan bedside locker tana shagwa6e fuska.

“Menene?” Inji mamy tana kallonta

“Mamy my hair, yayi dirty dayawa” tafada tana dan turo baki.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button