Comment on AUREN KWANGILA Page 81 to 90 by Unknown
Beebah ta cuceni A.A, taci amana ta, tasani tafka kuskuren da bazan ta6a iya gyarawa ba.
Please forgive me ashraf, ka yafemin kona dan ji sauqin abinda ke damuna, ka yafemin ko allah zai sassautamin halin danake ciki” ta qarashe maganar cikin kuka sosai.
Shiru dakin yayi sai sheshekar kukanta kadai da akeji qasa qasa.
Sosai magangganunta suka ta6a ashraf, sosai tabashi tausayi kuma yaji har aranshi ya yafemata don bega amfanin rashin yafemata dinba.
Allah yasani ada yasota kuma yaso ya taimakamata wajen ganin ta gyara hallayenta amma the deed is done and it can never be undone.
Kallon Dr dake tsaye shima tundazu yayi sannan yace “A minute please”
Sannan yajuya yafita Dr din ya maramashi baya.
Hada kai da gwiwa tayi taqara fashewa da kuka mai cikeda danasani.
“Ehrm… please kibar kukan haka it’s not good for your health, everything will be alright ok?” Inji sadeeq ahankali.
Saida yayi making sure tabar kukan sannan shima yafita waje yarufo kofar.
A corridor ya tadda ashraf tsaye hannayenshi zube a aljihu yana fuskantar Dr dake mashi bayyanin status din suzy.
Qarasowa yayi shima yana cigaba da sauraranshi har yakai aya.
Furzar da iska A.A yayi ahankali sannan yace
“So sad.. yanzu i think the best option here shine a sanar da familyn ta, koko?” Ya maida akalar tambayar ga sadeeq daya rungume hannaye a qirji.
“Yes abinda yakamata kenan” inji Dr
“Yanzu ya maganar bill?”
“Sir yayi settling din komai” dr yafada yana nuna sadeeq da beyi mgn ba haryanzu
“Alright please take good care of her, zamuyi qoqarin contacting din family dinta as soon as possible” yafada yana gyara tsayuwarshi
“Ok insha allah” inji dr din.
Nan sukayi sallama suka fita daga hospital din batareda sun sake komawa dakintaba.
Shiru motar ta dauka tunda suka baro asibitin.
“Tayaya kasan tana asibitin” ashraf ya jefoma sadeeq dake tuqin tambayar.
Dan kallonshi sadeeq yayi sannan ya ta6e baki yace
“I’ve been looking for her tun bayan faruwar abinnan don koyamata hankali, dakyar naganota nan din da taimakon wani neighbour dinta”
“And ina beeba ko mema take kiran friend din nata?”
“Babu inda ban nemeta ba, yanzu hakama nasa anaimomin ita duk fadin garinnan itakuma helen ta dade da barin garinma takoma qauyensu” sadeeq ya amsa idanunshi akan titi.
Ajiyar zuciya ashraf ya sauke yace
“To allah ya kyauta, yanzu ina zamu nemi familyn nata?”
“Suna jos, phone dinta ta 6atane kuma she doesnt wanna give any of her family number, guess tanajin kunyar suganta a wannan halin ne”
“Wannan ba hujja bace just look for a way to find their contact, is better susan halin datake ciki”
Harararshi sadeeq yayi yace
“Look for a way… kenan ni zanma nemosu ko?”
Daga kafadu yayi yace
“You started it all ai, saika ida ladarka”
Daga hakan basu sake cewa komaiba har suka isa company.
Ashraf na sauka sadeeq yasake tada motar yafice daga company din.
Ta6e baki ashraf yayi yanufi cikin company din yana cewa
“Aifa, aiki ya ganka”
Haka yanufi ciki walking majestically ma’aikata nata miqo gaisuwa yana dagamusu hannu harya isa sama.
Harya wuce yasake dawowa dabaya yana kallon kofar office dinta.
Dawowa yayi yanufi kofar office din ya bude ahankali yashiga.
Office din very neat don kullum sai an gyarashi ga qamshin freshner dayakeyi mai dadin gaske.
Ahankali ya qarasa gaban desk dinta yaja kujerar baya ya zauna yana lumshe idanu tareda sauke ajiyar zuciya.
Bude idanun yayi yana bin files files din dake jere neatly akan desk din sannan yamiqa hannu ya dauki guda.
Budewa yayi daga qarshe qarshen file din inda yakeda tabbacin rubutunta ne yana kallon neat and unique handwriting dinta.
6ata lokaci sosai yayi yana dudduba abubuwan office din wanda duk yawanci aikintane yayinda sonta ke qara hauhawa a zuciyarshi ganin yadda tayi ayyukan ba ha’inci kuma cikin tsari wanda shi a lokacin hauka ya hanashi ganin hakan don shi alokacin burinshi daya shine quntata mata.
Saida yagaji don kanshi sannan ya zaro wayarshi yakoma ya jingina da kujera ya lalibo numberta dayayi saving da *other half* ya danna kira.
Kamar dai yadda yayi zato qin shiga tayi don tuni tasa number a blacklist don idan ta daga baya magana saidai taita 6a66atu ita kadai. Hakan yasa tasashi a blacklist kawai.
Komawa yayi ya jingina da kujera yashiga sms don rubuta saqo kamar yadda yagani dazu dayayi browsing din hanyoyin da mace zata falla ma namiji, love txt na cikinsu saidai shi empty-headed ne a wannan fannin besan me zai rubutaba don beta6a ba, dama be ta6a soyayya ba sai akan suzy kuma yawanci ita ke liqe mashi so besan wani abu ba waishi love massage.
Rubutu yafara haryayi nisa kuma yaga beyiba ya goge yasake wani shima saida yakusan gamawa yaga rubbish ne ya goge.
Haka yaitayi yana gogewa, be ankaraba saidai jiyayi ana kwada kiran sallar magrub.
A mammakince ya miqe yana kallon time don lokacin yayimashi saurin tafiya.
Fasa rubuta text din yayi yafita yafarayin sallar magrub din sannan yadawo ya dauki briefcase din yafita.
A gidama bayan yagama duk abinda yake yana kwance kan gadonshi sanye da fararen sleeping robe, wayarce a hannunshi yana jujjuyawa yarasa me yakamata ya rubuta mata gashi beson using idea din wani ko yayi browsing, yanaso ne yafadamata what’s in his heart, yanasone ya fadamata kalamanshi bana wani ba.
Daga qarshe dai ya sadaqat yafara rubutamata akaro na ba adadi, be tsayaba saida yakai aya sannan ya sauke wani nannauya ajiyar zuciya yana kallon text din yana qara karantawa, gani yayi kamar beyiba don it doesn’t sound romantic amma allah ma yasan qarshe qurewarshi kenan.
Yatsarshi yakai wajen send botton yana tunanin ya danna koko?
Kamar an kwa6e hannunshi sai gani yayi ya danna send botton din.
Waro idanunshi yayi yana cewa “No!” Amma harya shiga.
“Shit!” Yafada yana dafe kai don besoba.
Sake karanta text din yayi again cikin takaici, shi sai yanzuma yaga text din beyiba kwata kwata, wannan ai se tayi zaton dan primary ya rubutata.
Tsaki yaja cikin takaici yana kallon wayar yaga ko za’ayi replying.
Jin shiru har kusan minti talatin yasashi haqura yayi tilli da wayar qarshen gado ya kwanta takaici fall zuciyarshi na sending din wannan message din dayayi saikace idan yagoge be turaba wani wanda yafi wannan yake iya rubutawa????
Itakau saudart a lokacin tana ma qasa suna fira kamar yadda ya zamarmasu al’ada a gidan.
Ba ita tashigo dakin ba saida 10:30pm yayi.
Saida ta canza kayanta zuwa na barci sannan ta fada kan gado ta jawo wayarta don kiran daddy tayimishi good night kamar yadda tasaba.
Ganin text da wata special baquwar number datayi yasata dan yin jim tana kallon number don it’s very special, kallo data tayima number ta haddace don simpliness dinshi.
Bude text din tayi don ganin abinda aka turo mata, sai gani tayi ansa
*helloo, how are you? Hope kinci abinci? And hope baki cika cikinkiba sosai so as not to feel uncomfortable, good night, sleep like a baby*
Wara idanu tayi tana sake maimaita text din wondering who the sender is.
Tsaki taja ta goge text din sannan tafita tashiga call log takira daddy.
Saida suka dan ta6a fira kadan sannan sukayi sallama kowa ya ajiye waya, tayi addu’ar barci ta shafa sannan ta kwanta.
Sharp sharp barci yayi awon gaba daita don dama tagaji sosai…✍