Comment on AUREN KWANGILA Page 81 to 90 by Unknown
“Same”
Murmushi yayi sannan ya miqe yafara takowa wajenta.
Bugun zuciyarta ne yafara qaruwa jin kamar takunshi na kusantota.
Daidai centre table din ya tsaya ya dora hannu akan drink daya yana kallonta, sannan ahankali yace
“Should I?”
Qin dago kanta tayi ta kalleshi don batason qara hada idanu dashi ta daga kai ahankali tanajinta duk a takure.
Murmushi yayi ya bude drink din idanunshi a kanta ta tsiyaya kadan a glass cup din sannan yamaida ya rufe ya dauki glass cup din.
Maimakon yakoma mazauninshi saiya dawo kujerar dake gefenta ya zauna irin zaman balancing dinnan daya riga ya bi jikinshi ya kai cup din abaki yana kur6a idanunshi akanta.
Ji saudart tayi kamar ta dora hannu aka taita ihu, jitayi tafi dazu takura dukda akwai dan tazara tsakanin kujerun nashi.
Wani haushi takeji na kafeta da idanun dayakeyi, wannan kallon ko maye albarka, why zai tisata gaba kamar t.v ya takurata da wadannan mayun idanun nashi?
Dan kawar da kai tayi dayan gefen fuskarta a hade tanajin kamar ta tashi tabar dakin.
Haka suka qaraci zaman nasu in silent kowa da saqe saqen dayake a zuciya. Basu san iya lokacin dasuka daukaba ahakan sai jisukayi anyi knocking din kofa wanda hakan yayi sanadiyyar dawowar dukansu daga dogon tunanin dasuka lula.
Da sallama sadeeq yashigo riqeda bottle din drink dinshi dayasha rabi.
Dan ware idanu sadeeq yayi ganin ashraf yayi changing din wurin zama sannan yadan saki murmushi ya ida qarasowa.
“To love birds, time up. Naga alamar idan aka biyemuku kuna iya kwana anan” yafada cikin barkwanci.
Dan ta6e baki saudart tayi batareda ta dagoba don dama a qagare take sutafi ko tajita normal.
“To ai saika tashi mallam, ranki ya dade zamu ruga kauyenmu”
Dan dagowa tayi ta kalleshi sannan ta sadda kai tana cewa “allah ya tsare”
Amsawa yayi da amin ya kalli ashraf dashima daidai ya kalleshi ya daga mashi gira alamun yatashi su tafi ko?
Harara ya gallamashi sannan ya miqe daga xaunen dayake hakan yasa sadeeq ficewa daga dakin.
Takowa yayi har gabanta yana kallonta.
Bugun zuciyarta yaqarayin saman jin tsayuwarshi akanta ga kaffafuwanshi datake gani agabanta kasancewa qasa take kallo.
Ahankali ya duqa gabanta yana kallonta, saurin ja da baya tayi ta shige ma kujerar tana ware manyan idanunta akan fuskarshi a mammakince don kusancin nasu yayi yawa don har tanajin saukar numfashinshi.
Daga glass cup din hannunshi yayi ya miqomata yana murmushi.
Kasa ko motsi tayi sai kallonshi datake cikin mammaki tana tunanin anya lafiyarshi lau?
Kamo hannunta yayi ya sakamata cup din aciki ya hada yariqe tenderly yana mata wani irin kallo mai tsayawa a zuciya.
Saurin sauke idanunta tayi qasa tana qoqarin zame hannunta acikin nashi amma takasa hakan yasata lumshe idanu don wani iri takeji har cikin 6argonta
“Thank you” yafada cikin rada yana kallon yadda ta limshe idanu taqi budesu ga zara zara lashes dinta dasuka hade waje daya kamar na fixing
Matso da hannun yayi saitin bakinta wanda hakan yasata saurin bude idanu tana kallonshi kamar zuciyarta xata fado tana qoqarin janye hannun.
Ahankali yayi placing din light kiss kan yatsunta dake riqeda cup din batareda ya janye idanunshi daga fuskarta ba wanda hakan yasata saurin maida idanun ta rufe gabanta na faduwa sosai.
“I love you” yayi wishpering cikin wata iriyar cool voice.
Sake tamke idanunta tayi zuciyarta na bugu sosai tanajin kanta na juyamata ahankali.
Ganin kamar hannunta nadan 6ari yasashi zare glass cup din hannun nata ya ajiye sannan ya saki hannun nata tayi saurin maida hannun cikin hijab still idanunta arufe.
“Take care of yourself… for me” yafada cikin rada in an extra cool voice wanda saida taji tasirin hakan har cikin kwanyarta.
Miqewa yayi ahankali yafara tafiya da baya baya yana kallonta.
Jiyake beson tafiya, jiyake kamar yatafi daita, jiyake be gaji da ganinta ba amma he have no choice, dolene yabi komai ahankali if he really want her, zai jira, zai jure harzuwa lokacinda zayayi nasarar mallakar zuciyarta, zai cigaba da hqr har lokacinda zata koyi sonshi, so mai tsanani irin wanda yake mata.
“Bye” yafada ahankali daidai yakai kofa sannan yajuya yafita.
Ta dade ahalin datake ciki, takasa koda bude idanunta ne bare tayi wani kwakwarrar motsi.
Jitake kamar haryanzu yana gabanta, jitake kamar haryanzu yana riqeda hannunta, jitake kamar haryanzu watery lips dinshi na kan hannunta. Jikinta haryanzu yakasa dawowa daidai, abinda yafaru yakasa barin brain dinta.
Jin an dafa kafadarta yasata saurin bude idanu a zabure.
Ganin habeeb ne yasata sauke ajiyar xuciya tana dan waige waige.
“Mamy tace what are you still doing here” inji habeeb yana kallonta.
Sauke numfashi tayi sannan ta miqe trying to be normal again
“Muje” tafada tana kama hannunshi
Haka suka fito suna tafe yana bata labarin chocolates dasu sadeeq suka bashi, itadai jinshi kawai take amma haryanzu bata ida dawowa daidai ba.
Koda suka shiga falon wucewa upstairs tayi batareda ta tsayaba.
Binta da kallo mamy tayi ta ta6e baki sannan tacigaba da kallonta.
Tunda suka kamo hanya yaketa sakin murmushi akai akai, allah kadai yasan farincikin dayakeji azuciyarshi a wannan lokaci.
“Uhmm am i really safe? Karfa inji saukar bugu, wannan dariyar dakake kai kadai anya lafiya?” Inji sadeeq daketa satan kallonshi tun dazu.
Komawa ashraf yayi ya jingina da kujerar dayake xaune yasake sakin wani broad smile kamar wanda akawa babban albishir
Murmushi shima sadeeq yayi ya maida hankalinshi kan tuqin dayake yana fadin “ba sabon ba”
????????????????????????????????????????????????????????????????
Zaune take adaki sanye cikin kayan barci idanunta a lumshe.
Duk yadda su abdul suka so ta tsaya suyi firar dasuka saba da daddare qiyawa tayi tace kanta ke ciwo don har lokacin bata gama dawowa daidai ba kuma babu abinda tafi buqata alokacin kamar kadaici.
Tayi nisa sosai cikin tunaninta taji ringing din wayarta alamun shigowar text.
Sauke ajiyar zuciya tayi ahankali sannan ta bude idanunta ta kalli wayar dake gefenta sannan ta dauka ta bude.
Wannan special number dince, bude message din tayi a sanyaye don jinta take too weak tarasa meke mata dadi.
Gani tayi an rubuta
*the best kind of friend is the one you sit with, not saying a word and leave feeling it’s the best conversation you’ve ever had*
*being with you today made my day and i know the smile you left on my face won’t fade even in my sleep… sleep without worries JHAN*
Shiru tayi tana kallon message din, qara karantawa tayi for the second time trying to figure out something.
*Being with you today* kenan the special number is Ashraf’s? Shine mai turomata all these messages dama?
Goge message din tayi tana cilli da wayar gefen gado tana jan tsaki.
“Hakan bazai chanza komaiba, nothing can change my hatred towards you, bazan ta6a bama wanda besan darajar mutane dama ba, you’re wasting your time ne kawai wlh” tafada ita kadai cikin jin haushi.
So wannan sabon salon duk don ta soshi yakeyi kome? Lallai iska na wahalar da mai kayan kara.
Idan ma mafarki yake to yadaina, dadin bakinshi bazai amfaneshi da komaiba, wama yasani ko kawai lust yakeji gameda ita, the first time yayi stolen kiss from her yanzu ma daga zuwa yayi wani grabbing din hannunta yayi kissing. Me hakan ke nufi?