Uncategorized

Comment on AUREN KWANGILA Page 81 to 90 by Unknown

Haka ta kusan raba dare cikin takaici da haushin abinda yaimata don gani take this is not love, it’s lust, pure lust.

Ashraf kau a 6angarenshi ranar kwanan farinciki yayi, sosai ganinta dayayi yayi tasiri a zuciyarshi, he can’t just take away her picture from his thoughts. Kosu ummy saida suka lura da sauyin yanayinshi.

Washegari ma haka ya tashi da ragowar farincikin jiya, last night was filled with her dreams, mafarkan dayayi daita basu qirguwa jiya, jinshi yake so un top…✍

Sorry for the short chappy.

Aski yazo gaban goshi.

Masu complaining saudart ta riqe wuta dayawa kuyi hqr, everything will be alright insha allah, lokaci guda ake jima mutum ciwo a zuciya, warkewarshi sai ahankali. Banason rushing din komai ne, hope zaku fahimceni????

Ummin fasihu????????‍♀️

[9/2, 11:48 AM] حبيبة عبدالله علي????????: ????????????????AUREN KWANGILA????????????????

(Contract marriage)

083

Washegari yana tashi first thing daya farayi shine duba phone dinshi ko zaiga reply don har mafarki yayi jiya tayi mashi reply din.

Ganin babu komai yasashi ajiye wayar dissapointedly ya tashi ya nufi bayi don daura alwala.

Bayan yan mintuna yafito daure da alwala yana dan yarfe ruwan hannunshi.

Wayar ya dauka yana kallo na yan seconds sannan ya sauke ajiyar zuciya yafara typing din short good morning text yayi sending sannan yajefa wayar a aljihu yafita.

Tana zaune tagama raqa’atainul fajr tana jiran a kabbarta sallar asuba taji ringing din shigowar txt a wayarta dake jikin socket.

Bata bita kanta ba tacigaba da danna counter din hannunta.

Saida tayi sallar asuba tadanyi tilawa sannan ta tashi daga sallayar ta linketa ta ajiye sannan tabi lfyar gado don yau weekend ba batun shirya su abdul makaranta.

Ba ita ta farkaba sai wajajen takwas nasafe.

Brush tashiga bayi tayi sannan tafito ta yafa dan qaramin veil akan rigar jikinta ta zare wayarta gindin chaji ta fita da nufin shiga kitchen.

Tana tafe ta danna power botton din wayarta taci karo da message agaban screen din.

Kallo daya tama number din ta ganeta don the number is too special to forget.

Sliding din wayar tayi wayar ta bude sannan tashiga message din taga ansa

*it is very important to start our day with a positive affirmation, we are the greatest gift of the universe, we are loved and appreciated. I prayed this day will bring you alot of happiness and muslim ummah altogether…SABAHAL KHAIR*

Tsayawa tayi daga tafiyar datake tana qara maimaita saqon again and again wondering waya turomata.

Kamar tayi replying da wanene? Saikuma ta fasa ta goge text din ta qarasa kitchen din.

Mamy ta tadda ciki tana peeling din irish.

“sabahal khair mamy” tafada tana dan rungumota daga baya.

Fizgewa mamy tayi takaimata bugu tai saurin kaucewa tana dariya.

“Ja’ira” inji mamy tana kwafa.

Murmushi saudart tayi tace “yau irish zamuci? I thought abdul yace indomie yakeso”

Harara mamy ta 6allamata

“Don yace ita yakeso shikenan kowama ita yakeso? Idan biyemashi za’ayi kullum ita zamu dinga ci kamar yan yari, idan bazaiciba yabarshi”

Kwa6e fiska saudart tayi

“Kai mamy autan naki?”

Ta6e baki mamy tayi batace komaiba.

“Ni bari to na dafa mashi” inji saudart tanufi inda kwallin indomien yake

“Dadai yafi, dama ke ke qara 6atashi” inji mamy.

Haka suka hada breakfast din tare suna dan fira jefi jefi har suka kammala sannan sukakai dining saudart tawuce sama don watsawa.

Da rana ma saida ashraf yasake turamata text, dukda be iya love text ba but yana qoqari wajen ganin ya rubuta something meaniful and educative, sai text din yake shige da irin quotes dinnan na encouragement.

Shima shiru babh reply, bejin dadin rashin ganin reply dinta amma hakan be saremashi gwiwa ba cos he’s determined to fight for her love.

Ataqaice dai kullum da kalan text din dazaiyi mata. Safe, rana da dare.

Kuma duk babu wanda yata6a samun reply dinshi amma hakan be dameshi ba kuma be hanashi sake yimata ba.

Saudart ma a 6angarenta kullum saita karanta text dinnan na wannan special number din.

Kuma kodayaushe kamar tayi replying ta tambayeshi wanene ko wacece sai kuma tafasa acewarta idan mai turowar yagaji ko tagaji da 6oye 6oyen zata bayyana kanta.

A 6angaren sadeeq kuwa yasamu nasarar persauding din suzy tabada number uncle dinta.

Babu 6ata lokaci ya sanar dasu yarsu fa na hospital.

Washegari saigasu, abin dai ba dadin ji don koke koke akaitayi ranar a ward din don labarin daya riskesu gameda diyarsu ba qaramin giggitasu yayiba.

Babu 6ata lokaci suka nemi transfer aka maidasu hospital din garinsu suka tarkata suka koma can.

A 6angaren saudart kau zaune take gidan mamy hankali kwance don har mancewa take dawani aure dake kanta.

Jin duk anyi shiru da batun yasa hankalinta kwanciya sosai tana addu’ar allah yasa a tafi ahakan don itakam tama kasa picturing din yadda zaman aurensu zai kasance a karo nabiyu aranta, gani take this will be worst than wancan zaman.

Mamy kau biris tayi daita dafarko amma ganin kamar abin bewani dameta ba yasa tafara yimata hade hadenta irin wanda tayimata wancan karon

Chanzamata sabbulan wanka tayi ta siyamata masu kyan gaske masu gyara fata takuma sa aka hadamata man shafawa mai hade hade kala kala don kamshin man ma kanshi ya isa kasan ba qaramin hadi aka mashiba sai turarrukan sawa a ruwan wanka data siyamata suma ba’a magana.

Sadda taba saudart su, tsayawa tayi tana kallonsu baki sake don ita ba yarinya bace tasan duk hade haden na menene.

Ganin kallon datake musu yasa mamy hade rai tabata umarnin takwashe tawuce dasu kuma daga yanzu suzama na amfaninta.

Babu musu takwasa tafita tana turo baki don ba haka tasoba.

Babu yadda ta iya haka tafara amfani dasu, saidai tun amfani na farko datayi dasu taji sun bala’in yimata don idan tagama wani cool qamshi takeyi mai sanyin gaske wanda hakan yasa taji takamu da qaunar kayyayakin don dama ita ma’abociyar son qamshice.

Can kuma mamy ta tsiri yimata ferfesu duk daren allah bazata bari ta kwantaba saita sha farfesu da pure milk sannan ta kwanta sai kuma fruit datake yawan tilasatata ci don duk ba’a son rantaba take ci dondai bata iya yiwa mamy musune sai jitayi dama zamanta tayi can wajen daddy da duk hakan be faruba.

????????????????????????????????????????????????????????????????

Yau thursday, suna zaune a falo dukkansu mamy na waya, saudart kuma da abdul da habeeb na baje qasa suna buga game, su aminu kau basu gidan suna gidan granny (mamansu Abba)

Dan ihu habeeb yayi ahankali gudun kar mamy dake waya taji yayiwa saudart gwalo yana maida fuskarshi puppy face.

Kallon juna saudart da abdul sukayi suka 6ata fuska tare.

Dauke papern game din abdul yayi ya cikwikwiyeta yana cewa

“Dama don kaga kai kadai ka iya shiyasa ka nace ayi to munfasa mu buga ludo”

Dariya habeeb yafashe daita yace

“Nadaiyi winning dinku, taar! Imagine ku biyu akan ni daya amma naciku 5:0 shame!!”

“Don dai bamu iya bane yaro da shi kadai ya isheka” inji saudart tana harararshi

“Me wannan ajebon ya iya banda shirme?” Inji habeeb yana fashewa da dariya don ya qule abdul

6ata fuska abdul yayi ya kalli saudart kamar zaiyi kuka.

“Habeeb banson wulaqanci, mind yourself” tayi warning din habeeb tana gallamashi harara.

Sunkuyar dakai yayi yana dariya qasa qasa ganin yadda abdul din keta rau rau da idanu hawaye harsun taru a idanun.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button