Comment on AUREN KWANGILA Page 81 to 90 by Unknown

“Ehen? Ni mezan miki?” Inji mamy tana dan harararta
“Zanje saloon please” tafada a marairaice
“Yaushe?”
“Yanzu, this is five, i promised kafinma su habeeb sudawo nadawo kawai wanki kai ne” tafada a marairaice.
“Ok kin gayawa mijinki?” Inji mamy.
Jimm saudart tayi tana kallonta batareda tace komaiba
“I said kin gayawa mijinki?” Inji mamy tana dan waremata idanu.
Kauda kai saudart tayi tana dan turo baki.
“kinzo wajena wai zaki saloon, ni ke aurenki? Ko kin manta ke matar aurece? Duk abinda kike ina sane samaki idanu kawai nake don ganin gudun ruwanki, yanzu duk nasihohin danake miki shiga suke a kunnen dama su fita ta haggu ko? Gaki kamar kinsan abinda yake maki ciwo amma ba haka bane, cigaba to allah yabada sa’a and if you really want to go to saloon ki nemi izinin mijinki ni ba ruwana, duk laifinsu abbanki ne dasuka wani zubamaki ido ahakan, i wonder why za’a kyaleki anan da igiyoyinki uku akai, wannan bayi bane is better ki tarkata ki koma gidanki inhuta da kayan haushi” inji mamy cikin fada don sosai zamanta ahakan ke damunta tayima abba magana yace zata koma lokaci suke jira tarasa wane lokaci suke jira.
Shiru saudart tayi tana kallon mamy tun sadda tafara fadan nata.
Kwana biyun nan talura abu kadan zatayi mamy zata rufeta da fada kamar dama a wuya take.
Shiyasa ma tun da can sunfi shaquwa da daddy don be cika saurin fushi ba unlike mamy dakeda fada sosai, abu kadan fada.
“Am sorry to” saudart tafada ahankali sannan tajuya zata fita.
“Kiranshi din zakiyi ki gayamashi?” Mamy ta dakatar daita da hakan.
Batareda ta juyoba ta turo baki tace
“Nafasa, zan wanke dakaina”
“Eh ki wanke da kanki tunda ke kinfi qarfin ayimaki gyara, ficemin daga daki shashasha” taqarashe maganar cikin dan daga murya.
Juyowa tayi tana kallon mamyn kamar tayi kuka, ita rabon ayi ma yasa tazomata maganar tun farko da bari tayi ta wanke abinta dakanta jejely da hakan be faruba.
“I’ll call him” tafada kamar zatayi kuka
“Mtcheew kanki akeji ni ficemin da gani”
Asanyaye tafice tanajin tsautsayi ma yasata dawowa gidan da yanzu tanacan wajeb daddy yana petting dinta kamar kwai.
Daki takoma tana kumburi, ita tayayama zata fara kiranshi, mutumin da be ta6a kiranta ba sai texts din dayake mata kawai.
Tayaya ma zata gayamashi? Me zata cemashi? Zani saloon?
Daukar wayarta tayi tana kallo not knowing what to do, yanzu idan bata kiraba mamy fushi xatayi tace taqi bin umarninta.
Shiga wajen rubuta sms tayi tayi shiru tana tunanin me yakamata ta rubuta mashi don bata tunanin zata iya kiranshi.
Ta dade tana daurawa da kwancewa daga qarshe ta sadaqat tayi typing din.
*Good afternoon, zanje saloon, permitted?*
Tsayawa tayi tana kallon abinda ta rubuta tanaji kamar tagoge but she has no choice haka ta danna send botton ta senda mashi.
Zama tayi wayar ahannunta tana kallonta tana jiran jin shigowar reply amma shiru.
Haka tazauna kusan 30mins amma ba reply.
Ranta ya 6aci sosai jitake me ma yakaita yimishi text at the first place? Jitake kamar ta dora hannu aka.
Qin fitowa tayi don haushi har saida taji hayaniyansu abdul alamun sun dawo.
Dagowa tayi ta kalli wayar dake can gefen gado ta jawota ta kunna taga babu reply. Kwafa tayi rai 6ace ta ajiye wayar tafita dakin ranta na suya.
Aqasa ta tadda su abdul wanda dawowarsu kenan zasu hau sama su chanza uniform.
Sannu da gida duk sukayi mata ta amsa ba yabo ba fallasa sannan suka haye sama don chanza kayan.
Zama tayi tana kallon t.vn dake kunne fuskarta ba walwala.
Mamy dake zaune falon ta kalleta sannan tace
“Yanzu saudart banida ikon gayamaki gaskiya sai ki tsiri kumbure kumbure? Wacce uwar arziqi zata bar diyarta tafita yawo da aurenta batareda izinin mijinta ba? Nabaki shawara as a good mother shine kike fushi kika ma fasa tafiyar? Dakyau” taqarashe zancen tana jinjina kai.
Saudart da dama kamar a wuya take sai kawai tafashe da kuka.
Sakin baki mamy tayi tana kallonta a mammakince don bataga abinda tayimataba da zata samata kuka.
Kuka saudart take sosai kamar wanda aka daka don harda shesheka.
“Ikon Allah, me akamiki kike kuka?” Inji mamy tana kallon yadda take kukan bilhaqi
“Mamy nifa baqin bin umarninki nayiba, na gayamashi yayi banza dani, ya zanyi?” Takuma fashe dawani kukan, dama me neman kukane akaima dariya.
“To shine saiki 6are baki kamar yar 5yrs kina kuka? Lallai wannan sangarta tayi yawa, allah ya shiryaki” inji mamy tana girgiza kai.
Itadai batace komaiba sai hade kanta datayi da gwiwa tana cigaba da kukanta qasa qasa.
“To nidai kimin shiru, kuma yanzu su abdul zasu sauko suganki kina kuka godai godai dake, kitashi kishiga dakinki kije kiyitayi hankali kwance babu mai takuraki”
Shiru tayi ta kyaleta batace komaiba tana sniffing ahankali.
Jin saukowarsu abdul yasata share hawayen a6oye tayi fuska tacigaba da kallonta saidai haryanzu ranta a6ace yake sosai.
Zama su abdul sukayi suna bata labarin abinda yafaru a school yau.
Sama sama take amsamasu don batajin yin magana ma kwata kwata, suna haka sukaji knocking a kofa.
Dagudu abdul yanufi kofar dagudu don duba wanene.
Ba’a dadeba yadawo falon yana dan tsallen murna.
“Aunty, uncle is here!” Yafada cikin murna.
Juyowa tayi tana kallonshi kawai not saying a word.
“Wane uncle?” Inji mamy
“Uncle A’A wai inkirata” inji abdul
Kallon saudart din mamy tayi tayi saurin kauda kai.
“Saiki tashi ko?” Inji mamy
Turo baki tayi sannan ta tashi tayi sama cikin jin haushi.
Ba’a dauki lokaci ba ta sauko sanye da doguwar hijab akan kayan jikinta.
Bata tadda mamy ba a falon hakan yasa tafice kawai.
Koda tafita bataga motarshi ba a inda yasaba parking ba hakan yasata nufar falon baqin tana tunanin yau bezo da mota bane.
Maigadi ya nufota yana gaisheta, amsawa tayi cikin fara’a kamar yadda tasaba tanufi bangarwn bakin.
“Hajiya ai yana waje” inji maigadin.
Hakan yasata chanza akalar tafiyar tata zuwa waje tanajin haushi dikya cika mata zuciya.
A gaban gidansu gefen hanya taga wata dalleliyar baqar mota parke wanda ko ba tambaya tasan tashi ce.
Ahankali kamar mai tausayin qasa tanufo motar kanta a sunkuye.
Tunda tafito yaketa kallonta, yarasa dalilin da kullum take chanza mashi, gani yake kamar kullum chanzata ake, she looks soo adorable.
Ja tayi ta tsaya bakin motar batareda ta dagoba.
Gani tayi anbude kofar 6angaren datake tsayen.
Dagowa tayi ta kalleshi suka hada idanu tayi saurin kauda kai tana sake tamke fuska.
“Get in please” yafada ahankali.
Shiru tayi kamar bazata shigaba saikuma ta qaraso ta shiga ta zauna batareda ta maido kafafun cikiba ta sadda kanta jin idanunshu na yawo akanta, ga qamshin turarenshi dasuka fara addabar kofofin hancinta.
“Good evening?” Yafada ahankali yana kallonta
“Uhmm evening” tafada kamar wanda aka tilastamawa
“Zaki saloon right?” Ya tambaya yana kallonta
“No, that was then” ta amsa tana kauda kai
“Yanzu fa?” Yasake tambayarta still yana kallonta
“Nafasa” ta amsa mashi a taqaice.
“Why?” Yasake tambaya
Cikin qosawa da maganar tace “kawai” tana kauda kai
Ajiyar zuciya ya sauke sannan yayi starting din motarshi yace “get your legs in muje”
Kallonshi tayi taga ita yake kallo saita dauke kai tace “nifa nafasa”
Shiru taji yayi hakan yasata sake juyowa ta kalleshi
Gani tayi ya kafeta da idanu wanda yasata jin wani iri cikin jikinta hakan yasata janye idanu ta sannan ahankali tace