Uncategorized

Comment on YANCIN KI Page 41 to 50 by Anonymous

cikin kidima da tashin hankali me’ad ta durkushewa agaban mahaifinta tana wani irin kuka “dan girman allah dady kayi hakuri ka yafemin , na yarda nayi kuskure arayuwata,Amman na tuba dady karka min haka ,karka juya min baya, banida wad’anda suka fiku ,ka yafemin nasan hakinka ne ke bibiyata ya fixge karfarsa daga rikon datayi masa.

 “baki ga komai ba tukun me’ad sai ranar da kikaji na d’aura auren sajida da mijinki ,kijira abinda zai biyo baya sai fu’ad ya zame miki annoba arayuwarki sai ya tarwatsa rayuwarki da farincikinki ,ke hatta wannan aikin da ni nasan wahalar dana sha kafin ki sameshi da har kike tinkaho da dashi, wallahil azim matsawr ina da haki akanki shima sai yabar hannunki kmr yadda Fu’ad ke shirin barin hannunki ……

“ki tashi ki bar min gidana ya k’arasa mgnr cike da hargagin ‘bacin rai …

Kuka me’ad take sosai tana Jan gwiwowinta tana bashi hakuri ,momy ma ta durkusa agabansa tashiga bashi hkr. “kayi hakuri Dan girman Allah kabarta ta zauna tare damu ,yanzu ina kake tunani zata ga yarinyar mara lfy atare daita ?

“khadaji ….dady yakira sunanta a zafafe “na’am dady. Ta amsa masa jikinta na rawa. 

“a iya tsawon arayuwamu, mun ta’ba samun wata matsala dake ?

momy tayi saurin girgiza kanta tana jujuya hannuwanta alamun dai yayi hakuri .

“to karki bari musamu matsala akan wannan yar isakar yarinyar mara jin magana .

“gidan nan ma tukun naki ne ko nawa ? 

Momy tayi saurin girgiza masa kai tare da cewar “naka ne. 

“to nagodewa Allah daya kasance nawa ne ba naki ba, kuma lokacin dana tashi gidansa baki sanya sisin kwabonki ciki ba ,Dan haka bana bukatar ganin me’ad cikinsa taje can gurin wad’anda take tunani sun fini daraja agurinta, sannan ya fuskanci me’ad sosai yana huci “minti biyu kacal nabaki ,ki d’auki yarinyarki kibar min gidana bana bukatarku cikinsa, hakuri tashiga bashi amman sam yace bai san da zance wani hakuri ba sai ta bar masa gidansa .

Ta mike ta tashi tsaye jikinta na rawa ta janyo hannun NASREEN ta rike cikin nata gam kmr wace za’a kwacewa ita, tasoma tafiya tana kuka ,momy na kuka , hatta NASREEN kuka take sosai tana tausayawa momy’nta “yanzu saboda ta auri dady’nta yasa babanta yayi mata wannan wulakanci, daman grandpa dinta bayason auren iyayenta ?

 Hakuri take son bashi Amman tashin hankali datake hangowa tattare da momy’nta da ita kanta yasanya ta kasa magana sai kukan datake har da shesheka. 

Jikin momy na ‘bari tabiyo bayan me’ad tana kuka tana kiran sunanta….shi kuwa dady ko ajikinsa, Sam bai ji wani abuba dangane da halin da ta tsinci kanta ba.

 me’ad ta tsaya tare da cewa ” momy ki daina kuka ki koma kawai duk abinda ya faru dani ,ni na jawowa kaina na zabi d’a namiji akan mahaifina ,na fifita soyayyar fu’ad akan ta mahaifina, yau wa gari ya waya? 

“”yanzu ina zaki? 

“duk inda Allah yayi momy zan tafi na bar rayuwar kowa, zanje nayi sabuwar rayuwa tare da diyata, zan rungumi kaddarata….

“amman ki rokon min dady yayi hakuri ya yafe min abinda nayi masa wallahi nayi danasani arayuwata, ki min addua momy ko zan daina jin rad’ad’in da zuciyata ke min … ta juya tacigaba da tafiya har ta isa jikin motarta tashiga ta tayar , ta fito daga cikin gidansu tana wani irin kuka.

Gudu kawai take shararawa akan titi, duk hanyar data gani ,bi take saboda bata San inda zata ba ,banda bugawa bubu abinda zuciyarta keyi, kuka take sosai tana dukan sitiyari motar “me yasa nayiwa mahaifina abinda nayi masa akan soyayyar fu’ad ta furta a fili? 

” me yasa ban bi zabinsa ba nace lallai sai fu’ad zan aura gashi komai na neman birkice min ?

Ta sake fashewa da wani sabon kukan ,hakika na cuci kaina, iyaye duk lallacewarsu sun wuce wulakanci ,ballanatana irin nawa iyayen da samun irinsu ke da wuya, dady uba ne har da rabi ,wanda ke maye gurbin uwa idan tana raye ko amace .

“sun haifi ne sun min gata ,mahaifina ya inganta rayuwata sosai yabani abinda duk wani d’an Adam zaiyi tinkaho dashi arayuwar duniya ,bai rageni da komai ba a tun tasowata ,komai nace shi za’ayi .

“,me yasa nayi masa abinda nayi masa?

” me yasa banyi masa biyayya ba alokacin dayace na auri safwan? ” why why why !!! Me’ad meyasa nayi abinda nayi ?

“Wayyohlly Allah na cutar da kaina, Kuka take sosai Sam ta manta da nasreen dake zaune agefenta sai da taji yarinyar ta riko hannunta a matukar afirgice tare da sakin razananniyar k’ara sannan taja birki da karfi ta tsaya cak tana Jan ajiye zuciya, hawaye sha’be sha’be kwance Akan fuskarta, itama nasreen din kukan take sosai har lokacin da shesheka ,tana jin tausayin dady’ntan sosai fiyye da mahaifiyarta , Amman ayau tausayin momy’nta ne ya rinjayi nashi har batasan a mizanin dazata ajiye hkn ba, rungumeta me’ad tayi ajikinta tana kuka “am sorry bby gudun danake ya tsorotaki ko.. ? 

Nasreen ta d’aga mata kanta al’amun Eh tana kuka. 

“am sorry na daina bazan sake ba kinji bbynah, ta d’aura idanunta akan agogon fatan dake d’aure da tsinyayar hannunta , lokacin shan maganin nasreen din yayi ,Dan HK ta kai hannuta sit din baya ta d’auko ledar maganinta da ruwa ta balla ta bata ta sha sannan ta mai daita ta kwanta akan kujera, itama ta meida bayanta akan kujerar datake zaune akai, byn tayi baya kad’an daita, ta runtse idanunta still hawayen idanunta suki tsayuwa har lokacin nadama ce fal cike da zuciyarta. 

Kusan minti talatin tana gurin tana zance zuci wayarta ta d’auki k’ara sauti me dadi da ta’ba zuciyar Wanda ya saurara,ko bata duba wayar ba, tasan ko waye me kiranta, sakamakon sautin dataji “fu’ad dinta ne ,dan shi kad’ai tasanya wannan sautin saboda matsayinsa gareta ,” mutumin data sadaukar da rayuwarta da komai nata akansa, mutumin da shine silar ‘batawarta da mahaifinta,a yau tayi datasanin a had’uwarta dashi a wancen lokacin” duk duniya tasani kowa yasani babu halittar da mahaifinta ke so sama daita Amman an wayi gari sanadin had’uwarta da fu’ad komai ya canza, soyayyarta ta juye zuwa kiyayyar da batasan ranar gushewarta ba..

Wani kukan ne ya kufce mata tasanya duk hannuwanta ta toshe bakinta ,”tarasa fu’ad rashi na har abada, sannan tarasa soyayyar mahaifinta, ga aikinta datake ganin shine gatanta da rufin asirinta shima tana nema rasashi adalilin takasa samun natsuwar zuciyar gabatarwa.

 akalla bazata tuna karshen shigarta office dinta da sunan yin aiki ba, gashi tun rashin lfyr nasreen bata taka kafafunta zuwa cikin ma’aikatar ba, ko kiran chairman bata samu damar yi ba ,batasan me zai biyo bayan faruwar hkn ba ,tun yanzu tacire rai da tsammanin da aikinta bisa kaidodinsu ,na ko fashin rana daya mutun yayi zai fuskanci babbar matsala da chairman.

 “zuwa yanzu tasan komai ya rigada ya tsaya mata ,shikenan rayuwarta zata zamo abar tausayi mara amfanin ..

Fu’ad yakira wayarta sau babu adadi ,Amman batayi yunkurin d’auka ba sai hawayen datake zubarwa .

jiki a sanyaye nasreen takamo hannunta”momy !!! dady na kira ,should I pick the call?

“No……tace mata atakaice tana me runtse idanunta”why momy ki d’auka mana…….,” koni na d’auka plz…?

“Pick….ta fad’a saboda batason k’arin damuwa akan wacce take ciki .

Nasreen ta d’auki wayar tare da cewa “hello dady nah.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button