Comment on YANCIN KI Page 41 to 50 by Anonymous

Shiru ne yabiyo bayan zamanta , kafin daga bisani chairman yayi gyaran murya yasoma magana cikin kwararren turancinsa wanda bazaka ta’ba cewar ya had’a jinsi da hausa fulani ba”acikin yan kwanakin nan abubuwa dayawa sun faru Wanda yasa dole mu tautauna akai, Abu na farko da campay tasoma fuskanta shine karancin income din da company bai samu ,ta hanyar sakacin manager. Me’ad ta d’ago idanunta da sauri ta d’aura akansa tana kallonsa , chairman ya fuskanceta da kyau kana yacigaba da mgn “sakacin rashin tsayuwarki akan aikinki da rashin bawa aikin mahimmanci yana kokarin janyo mana babbar hasara, a halin yanzu dakatarwa ce tafi dacewa dake ,Amman saboda wannan shine karo na farko da muka ta’ba samunki da wasa da aiki, yasa zamu yi sausaci akai ,Dan hk daga wannan lokacin bama bukatar sakaci ko rashin bawa aikinki mahimmanci, Dan idan muka sake samun rashin ingancin tsayuwarki aiki zamu sallameki……
tunda chairman ya fara magana ta nemi miyo ko daya tarasa abakinta, zuciyarta ke wani irin bugawa da sauri sauri ,duk karfin ac dake aiki acikin conference room din ,hkn bai hana gumi tsatsafo Mata ba..
take furucin mahaifinta yashiga dawowa mata “aikin da kike takama dashi Wanda ni kad’ai nasan irin wahalar Dana sha akansa kafin ki sameshi shima zai bar hannunki ……
“inna lillahi wa inna ilaihi rajiun kawai take furtawa a zaunen dake agurin gumi na sake tsatsafo mata , iya abinda ta iya fahimta kenan daga bakin chairman duk sauran maganganun da yacigaba dayi babu abinda ta fahimta hatta Wanda sauran ma’aikatan suka taunana bata fahimci komai ba ,sakamakon zuciyarta data tsaya ta daina aiki na wani lokaci …
Lokacin da zuciyarta tacigaba da aiki ta dawo cikin hanlinta ta nemi kowa tarasa acikin conference room din sai ita kad’ai zaune ,ashe tuni taron ya watse .
runtse idanunta tayi sosai, wasu zafafan hawaye suka shiga kokuwar zubo mata “me ke shirin faruwa da rayuwata ?
“gidana babu dadi ,bani da jituwa da mahaifina , aikina na neman subuci min ,tabbas wata maseefa na kusanto rayuwata “ya Allah ka kawo min sauki cikin lamarina ,ya Allah karka barni haka, na tuba Allah kasanyaya zuciyar mahaifina akaina ya yafe min abinda nayi masa ,domin nasan bakinsa ne ke bibiyar rayuwata,
ta Dade zaune agurin tana kuka ,ganin kuka da tunani bazai bar kanta ba yasa da kyar tasamu ta mike tsaye tare da gyara zaman mayafinta zuciyarta bata shawarar ta nemi mutane suje su bawa mahaifinta hakuri ya yafe mata, mahaifin sajida shine mutun na farko da zuciyarta ta hasasho mata Amman ina bazata taka kafafunta zuwa gidansa ba, ‘yarsa tayi mata katangar karfe Dan wannan gidan har abada bazata sake sanya kafafunta cikinsa ba ,ta kofar baya ta biyo Dan batason jama’a su ganta ,Dan zasu fahimci halin da take ciki ..
kmr jira ake duk inda ka yi acikin ma’aikatar maganar me’ad ake da irin matakin da chairman yace zai d’auka akanta, su mudansir kuwa ansamu abinda ake so ,sai murna suke har da rawa kmr wad’anda akayiwa albishiri da gidan aljannah ” kai mutumina wallahi ina cikin farinciki mara misaltuwa ka koma gurin malamin nan naka ya sake k’ara wutar aiki, ayi ayi akoreta wallahi ban so uzirin da chairman yayi mata ba ,naso yayi mata me gabadaya ne injin cewar ma’aruf..
wata uwar dariya mudansir ya kwashe dashi “sha kuruminka abokina komai daki daki yafi ka zuba ido kasha kallo muna nan za’a yi mata me gabadaya..
Tahir ya saukar da ajiyar zuciya daman kuma tun da suka soma mgn bai tsoma bakinsa ba sai yanzu yace “gsky na fara jin tausayinta me zai hana abarta hk idan ka lura tayi sanyi ba kmr lukutan baya ba .
“Kunji shirme banza ,kai ta tafi can kabawa mutane guri ,da alamun ka soma sauya ra’ayinka na bukatar matsayinta daka furta tun farko?
“Ko ban sauya ra’ayina ba nima da wasa na fad’a mgnr , ina ni ina matsayinta, ku kanku kunsa wasa nake yi bazan ta’ba samun matsayinta ba sai wani ikon Allah.
Maaruf yace “mudansir rabu da da wannan shirmammen banza da alamun cutar hauka tasoma kama…..
ai bai kai ga karasa mgnr ba tahir ya cakumi wuyan rigarsa da iyakacin karfinsa “ni ne cutar hauka ta kama,?
“ni zaka cewa hk saboda kai Mara imani ne da tausayi ” ina zamu da hakinta ?
“Meye ribarmu idan munyi sanadin rabata da aikinta da har zaka dangantani da kalmar hauka?
Mudansir yayi saurin shiga tsakaninsu “haba tahir meye hk ne ?
wasa yake maka fa bai kamata ka d’auki zafi ba ma’aruf ya fizgo mgn da kyar yace “rabu dashi ance masa me cutar hauka yayi duk uwar da zai yi ,mahaukaci dolo sauna dakiki..tahir ya kai masa mari sai ga jini ya balle abakinsa abu kmr wasa suka dinga zagin kansu da son yin dambe, da kyar mudansir yasamu ya rabusu tahir yana huci yace “ni… ni …na cire hanuna acikin shirinku daman kuma ba dani akaje gidan malam ba ,daga yau babu hannuna cikin shirinku duk abinda zaije yazo karku sani ciki azzalume Kawai ya fita yana banko musu kofar da karfi .
suka tsaya sororo suka bi kofar da kallo kirjinsu na mahaukacin bugu”kaji abinda wannan D’an iskan ya fad’a ko ? Ma’aruf ya fad’a yana naushin iska “rabu dashi shima zan gama dashi wata killa kafin ita tabar aikin shi zai rigata barin aikin.
Kai tsaye tahir harabar ma’aikanta ya nufa inda ya iske me’ad tsayen tana zariya abar tausayi, kunnenta manne da waya “wallahi ta bani tausayi ya fad’a acikin zuciyarsa yana jin kmr yaje ya sameta ya sanar daita abinda aka yi mata,Amman yana jin tsoro saboda yasan halinta, yasan yadda take da saurin d’aukar zafi, karshen abun ya juye ya dawo kanshi ,shi kad’ai .
kad’a kansa yayi kawai ya kama gabansa ya koma bakin aikinsa .
************
Zaune Alhaji ediris takai yake agaban amininsa kuma abokin shawararsa mahaifin sajida suna fuskantar juna kafin daga baya yasoma mgn a natse cikin sanyayyiyar murya “me yasa zaka hanata auren abinda take so, ?
“A ganina daga me’ad har sajida abu daya ne agurimu ta wani fannin ma har gara sajida tunda duk rashin son da batawa emran ta hakura ta auresa daga baya Allah ya kawo rabuwa atsakaninsu, Dan haka banga dalilinka na hana auren fu…ya datse harshensa yakasa karasawa saboda baya tunanin zai iya karasa sunan wannnan D’an matsiyatan, shi kansa bazai so sajida ta auresa ba saboda irin tsanar da yayi masa Amman domin kuntatawa me’ad zaiyi tsayin daka ruwa da tsaki akan yaga yaron ya aureta shi da yasan inda zai ga najma har ita sai yabata makudan kudi ta auresa , kawai dan yaga me’ad cikin bakiciki kmr yadda tayi silar jefa safwan da shi kansa da har yanzu wannan bakinciki yaki barinsa.
“abinda bazai ta’ba yiwuwa bane wannan AI cin amanar kauna da yarda ne Sam sajida baza ta’ba auran mijin me’ad ba har abada …iniji Cewar mahaifin sajida .
Dady yace “ta ina aurensu yazama cin amana ?
“Gsky ni banga wani cin amana ba acikinsa ba.
Mahaifin sajida yace “Ko babu cin amana ai ana barin halak Dan kunya, “banda wannan halak din mahaifin me’ad ya fad’a yana furzar da iska .
muhawura ce tashiga tsakaninsu kowa na kawo hujjarsa Akan auren daga karshe dcp aliyu ya Mike ransa a matukar ‘bace ya bar parlour’n saboda idan yacigaba da zama agurin zasu raba gari ,da shi da amininsa da Allah kad’ai yasan tsakaninsu .