Uncategorized

Comment on YANCIN KI Page 41 to 50 by Anonymous

Ta fito sanye cikin wando da rigar body hook Wanda ya matse jikinta sosai ,A tsaye ta sameshi jikin motarsa dake kusa da nata motar ,ya hard’e hannuwansa duka akirji, tun sanda ta fito ya tsurawa surar jikinta idanunsa,yana kallonta daga sama har kasa yake kare mata kallo tsab irin macen da yake burin so da mallaka kenan arayuwarsa ,ji yake duk duniya babu mace me kyawunta sannan yana ji tmkr ya isa gareta ya rungumeta akirjinsa , yanayin yadda yake kallonta kwata kwata baiyi mata ba ,Dan har ya sata jin wani iri ajikinta saboda gabadaya ya tsurawa nonuwanta idanunta kmr zai cinyesu , kallo daya tayi masa ta d’auke idanunta akansa ta haye saman motarta ta zauna tana kallon wayar hannuta batare da tace masa komai ba 

Khalid kyakkyawa ne shima sai dai bai kai fu’ad a komai ba , gyara tsayuwarsa yayi tare da matsowa gabanta still rungume yake hannunwansa a kirjinsa ahankali yasoma mgn cikin sanyayyiyar muryarsa “plz sajida kinsa na dad’e ina binki ta hanyoyi daban daban , ina sonki kuma tsakanina da Allah ,ki manta kowa ki bani damar na shigo cikin rayuwarki dan Allah…. 

Ta busar da iskar bakinta idanunta har lokacin yana kan wayarta, kanta tashiga girgizawa sannan d’ago ahankali tana dubansa a yatsine kana tace ” Khalid Kake ko wa ?

“Wai me kake tunani Akaina ne? 

“meyasa ba zaka fahimceni ba sannan ka fahimci ina na dosa ,?” Try to understand me Khalid …..”bana son ka bana kaunar wata halaka da kai kuma halakar da mukayi abaya ta mutunci Allah yasanya mata albarka Amman dan Allah ka fita cikin rayuwata , saboda kai ba irin namijin danake so bane ,you not can of man I like”

” am not can of man ?ya tambayeta yana tsareta da manya idanunsa “yes of course ta bashi amsa tare da shayi ko wata fargaba ba sannan ta maida idanunta kan wayarta tacigaba da abinda take. 

muryarsa cike da rauni da in ina yace “meye bambamci tsakanina da kalar namijin da kike so? 

“khalid…..bana tunanin yau ne zan fara gaya maka wannan mgnr ,I have my type, ina da type din namijin da nake so , wanda zuciyata take so da muradi ba kai ba ,kuma zan tabbatar da na bawa xuciyata abinda take so tak’arasa mgnr tana hura masa iskar bakinta me zafi sannan ta tsaresa da idanunta “just forget about any love you have for me coz I can’t love you kaje gaba da rayuwarka watakila zakayi cath up wata tasoka but not me ….

 “but ai ni ke zuciyata ta za’ba kuma take muradin rayuwa daita ina sonki saji….”enough khalid don’t ever say that rubbish again..bazan ta’ba sonka ba koda kuwa zaka mutu ka dawo sajida nada ra’ayin mijin datake so okay ,”ina son namiji kamili natsatse wanda yasan darajar da ciwon kansa, dogo baki me faffad’an kirji me sex eyes me haiba da Kammala, ma’aboci kyau wanda a duk sanda na kallesa zanji Feelings dinsa na ratsani …

” idan na kallesa zan ji dadi acikin zuciyata sannan zai sani na jini a new level ba kai ba me zaka min ?

“me zanji a tattare da….. …?

“common short up there my friend karki tozartani akan wannan sifoffin da kika lisafa … ni meye na rasa ajikina ?

” meye banda shi acikin abubuwan da kika lisafa?

ta kai hannunta ta gyara gashin kanta daya zubo gefen fuskarta sannan tace “karka fad’i abinda kasan ba haka bane, da kace duk abubuwan dana lisafa kana dashi khalid ta ina ?

“Ina suke ?

“ina abinda na lisafa?

“Sam ni banga komai ba danake so na namiji ajikinka , da kana da abinda na lisafa da yanzu mun wuce gurin ,abu na karshe da zan gaya Maka ka bar rayuwata ..

Muryasa a matukar sanyaye yace plz sajida wallahi ina ..”

“Ka daina ronkona plz Dan ba zaka ta’ba samun abinda kake so ba kalleka fa D’an Allah wani gaja gaja da kai .

 kai yanzu bakiji kunyar cewa Kana sona ba a girme na girmeka nesa ba kusa ba Khalid me zan ji aurenka …? zai yi mgn ta katseshi ta hanyar cewa “stop beging me khalid kaje kaso wata plz.. 

ya sauke naunauyen ajiyar zuciya tare da zura hannunwansa duka cikin aljihun wandonsa yana fitar da wani hucin Numfashi me gyaraye da tsagwaron ‘bacin rai”ammm.. amm naji baki sona sai mijin aminiyarki kike so, saboda shi ne wanda ke da dukkanin tsifofin da kika lisafa ,tell me i want know? 

Ta d’ago fuskarta a d’aure tana dubansa shima kallon cikin idanunta yake cike da isgilanci rainasa din datayi “khalid am not long interested on you just live my life plz …

 ya juyar da fuskarsa kad’an yayinda dryrta ta subuce masa yayi murmushin mugunta sannan ya juyo ya fuskanceta “dole ki waskewa mgnta saboda kinsa nasan komai , auren cin amana kike kokarin yi amman bari nagaya miki wani good news, ki hakura ki aureni saboda nasan duk abinda kike bukata daga cikakken nmj wallahi zan miki ,Zan iya cika wannan bombom din naki tsab da zan mararki Dan hk ki daina rainani yaro ne ni a zahirance Amman baki San badini na ba ..kuma ki rubuta ki ajiye a inda bazai goge ba ni ne zan aureki as ending …….

A matukar tsawace tace “plz just go tana nurfafashi tmkr me cutar asma ” i don’t want see you near me ta fad’i hk cikin murya mai rawa ala’mun tana son yi masa rashin mutunci “

“sajida …yakira sunanta muryarsa a kasalance “khalid can you live plz ? “dole ne nace bana yi bana sonka bana kaunarka bazan iya soyayya da kai ba ka bar rayuwata mana “naji amman yakamata ki duba girman son danake miki ki bari muyi ….”no no we are not talk to anything just go …get out ..live ..bye… ta fad’a a matukar harzuke tana me dafe gefen kanta data ji yasoma Sara mata “plz i beg you sajida tayi saurin d’aga masa hannu out bey tana nuna masa kofar get da hannunta.

 jimmmmmm yayi yana kallonta sannan ya meida hannuwansa duka cikin aljihun wandonsa yasoma d’aga kafafunsa kmr kazar da kwai ya fashewa aciki tsaki taja ta gyara zamanta tayi consentret akan wayarta datake aikin turawa fu’ad text message tana jin lokacin da me gadi ya bud’e masa get ta juya a matukar fusace “you stupid man if you ever open get to that stupid boy you wil see what wil happen to you,” a’a kunji min jaraba da maseefa irinta primature… karami yaro dashi sai jarabar naci ko ya zaiyi dani oho? 

“nace banayi banayi !! ana so do…. shiru tayi ta kasa karasa mgnrta taja tsaki kawai ….

cikin sauri fu’ad ya fito daga cikin d’akinsa yana waya sanye da farar singlet da wando sai dai ya d’aura rigar t shirt a saman singlet din bai sanya botira ba “okay ina jinka tana wajen har yanzu ?

 Can bangaren kabeer yace “tana wajen Amman kayi sauri da alamun ta kusan gama abinda tazo yi ..”dan Allah ka tsayar min daita . Kabir yace “kaima kasan halin wannan rikitacciyar matar taka ba tsayawa zatayi ba ,yanzu ma data ganin bazata tsaya ba .”, okay ganin nan zuwa suna tare da nasreen ne ?

“A’a injin cewar kabir cikin sauri fu’ad ya isa ya bud’e motarsa yashiga ya kunna tare da danna hon…..da karfi me gadi ya bud’e masa ya fita aguje.

 sai dai yana zuwa yashiga bud’e idanun yaga ta inda zai ganta ,kai tsaye inda kabir ya gaya masa ya nufa da sauri Amman bai ganta ba Dan hk yak’araso gurin kabeer yana riko hannunsa “ina take kabeer …?

Cire hannunsa kabir yayi cikin nasa yace “wallahil yanzu nan ta wuce naso na bita sai dai banzo da mota ba ,goshinsa ya dafe yashiga zagaye gurin tare da ya furta Allah yana me runtse idanunsa “why me’ad me yasa kike son ruguza mana rayuwarmu alhalin kinsa muna bukatar juna ..?

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button