Comment on YANCIN KI Page 41 to 50 by Anonymous

Da sauri ya sake dawowa inda kabir yake tsaye yana dubansa cike da matsanancin tausayawa “wani hanya tabi kabir …?
Kabir ya nuna masa hanyar da tabi ..yabi hanyar da kallo yana tunanin yabita ne ko ya fita harkarta ya hutawa rayuwarsa, shi daman ba saboda ita bane yake wannan wahalar…
Jiki a sanyaye ya k’arasa jikin motarsa yana kokarin bud’ewa kiran sajida yashigo wayarsa ya ciro wayar daga aljihun gaban rigarsa yana duba screen din wayar,number da ya gani ne yasashi Jan tsaki , kmr bazai d’auka ba sai kuma ya d’auka “uhmmm meye kuma?
“I lost a lot of things arayuwata amman banaso kaima na rasaka fu’ad hope sir malik ya isa maka da sakona?
“Wani banzar sako kenan “sajeeda ya kirata ransa a matukar ‘bace”karki k’ara min matsala da damuwa akan wanda nake ciki ,wai ma Sajid me kike nufi dani ne ?
“Babu komai sai alkairi kuma InshaAllahu zai tabbata ,tun da har ka furta tare da amincewa aurena wannan kawai ya isheni nacigaba da rayuwa har zuwa sanda zamu mallaki juna sannan kuma karshen matsalata tazo ,ka daina zurfafa tunaninka ,ka daina damuwa I promise zan baka dukkanin kulawar dakake bukata ,zan baka kulawar daka rasa saboda irin son Da nake ma …
“common that was not on fear, sajida bakya sona ki duba kiga yadda nake cikin tashin hankali akan matsalar gidana nasan kinsa komai amman ke k’ok’ari kike kawai a d’aura mana
aure.
“Tabbas aurenmu shine agabana kuma shine abinda nake buri a halin yanzu sannan zanyi Iya kokarina naga na mallakeka , yanzu dai kana ina ,Dan ina son mu had’u da kai akwai maganar da zamuyi very important”
“bani da lokacinki a halin yanzu neman inda matata da yarinyata nake “ta kwashe da wata uwar dry sannan tace “ka sani ko nasan inda matarka take da yarinyarka just try and come…jikinsa yayi sanyi yasoma ya rage murya “Dan Allah ko kinsa inda take ne ki gaya min …?
“Uhmm a’a ban sani ba ,Amman ka dai kazo akwai Wanda yasani “rubbish ya furta a harzuke ganin raina masa wayo take son yi akwai siyar data sake shirya masa ,shi kuma ya ranse ba zai sake barin su had’ u ba either ko tazama matarsa ko km sun rabu …”ba zaka zo ba kenan ?”yes of course banzo wawiya kawai maciya amana ke auren ma na fasa inga uban da zai sani aurenki …ta saki wata razannaniyar k’ ara tare da durowa daga saman gadonta tana furta “what?
“Abinda kunnenki yaji shi na fad’a na fasa aurenki kibar rayuwata simple as that “
Muryarta na rawa tace” Dan girman Allah Allah fu’ad kar ka fasa au..sai kuma kiyi ya katse kiransa tare da shigewa motarsa ya bar gurin aguje..
**********
Yau takama Monday Wanda ko bature na tsoron ranar da girmamata rana ce da duk wani ma’aikaci ke jin tsorota da taka tsantsar daita ,me’ad tana zaune acikin motarta kmr koda yaushe tana tunanin yadda xata bullowa wannan matsalar da ta addabe ta , taji an kwankwasa glas din motarta da sauri ta d’ago kanta, tare da bud’e murfin mota ,daya daga cikin staff din company ne ya bayyana agabanta bayan sun gaisa yake fad’a mata cewa chairman yana son ganinta a office din sa.
A sanyaye ta fito daga cikin motar tare yiwa motar key , da sallama ta shiga office din tare da neman kujerar da ke ajiye a gefe ta xauna gabanta na wani irin fad’uwa , bayan sun kammala gaisawa da chairman ya shiga jefa mata wasu tambayoyi.
“Har yanzu na kasa ganin wani canji daga gare ki me’ad ,dan Allah ki fad’a min abinda yake damunki bana so ki boye min komai, Ni dai nasan da ba haka kike ba sam ban sanki da sakaci ko wasa da aiki ba, me yasa Yanzu abubuwa suke neman tabar’barewa Company? Ina jiran amsa daga gare ki kuma bana so ki boye min gaskiyar abinda ke faruwa da ke.
Kuka mai tsanani me’ad ta shiga yi, sai da tayi kukan da ya ishe ta sannan ta zayyana mishi dukkan halin da take ciki.
Ya tausaya mata sosai kuma yayi alƙawarin insha Allah matsalar da take ciki da mahaifinta yazo ƙarshe godiya tayi masa, yacigaba da mgn yana duba file din su ma’aruf “kinsa cewa wannan rashin zamamki cikin office dinki , sammu akayi miki ?
mead ta d’ago kanta a matukar firgice tana dubansa cike da mamaki da matsanancin tsoro, “kina mamaki ko ,?tayi saurin d’aga masa kai alamun Eh “karkiyi mamaki mead akan samu irin haka .
bakinta na rawa tace ” ni kuwa wa nayi laifi da har zai min samu akan aikina ?
Chairman yace “kina son sani ko su waye ?
Jikinta na rawa tashiga girgiza masa alamun eh”
“okay ina zuwa “ya d’auki wayarsa ya kira messenger cikin minti biyu yashigo jeka ka cewa acp ya shigo min da yaran nan kafi ya wuce dasu “okay sir ya fita da sauri ..
Ahankali taji an bud’e kofar gabadaya ta kasa juya saboda jikinta daya d’auki rawa har sai da charman yace “ki juya mana kiga yan iskan da suka miki aika aika da kokarin rabaki da hanyar abincinki “
jikinta na cigaba da kyarma ta soma juyawa ahankali har ta juyo gbdy idanunta ya sauka akan tahir da mudansir da ma’aruf dukanindu hannunwansu da handcuff, take gabanta yayi wani irin dukan uku uku yashiga fad’uwa tashiga nunasu da hannunta bakinta na rawa “ku..ku ne kuka min sai kuma ta rushe da kuka “laifin me na muku da kuka shirya min wannan munakisar?
“A halin yanzu ba sai kayiwa mutun komai ba zai nufeka da sharri inji cewar chairman “wasu mutane suna nan su kawai basa son ganin cigabanka ,sun fi so kullun suganka kana bara akan titi ‘acp a wuce dasu sannan ayi musu azaba me rad’ad’i har sai sun gaya muku malamin dayayi musu wannan aiki, if possible ma a asakasu a under ground har sai sun fad’a Dan babu yadda banyi dasu ba, alokacin Dana kamasu suna tad’in Dana takurasu ne ma sukace tare da tahir akayi komai ”
Acp yace”Karka damu kana zaune zamu zo maka da good news. “Okay nagode sosai tare da mikawa acp hannu sannan suka juya suka bar office din .
Wani irin kuka me’ad take kmr ranta zai fita chairman nacigaba da bata hakuri”ba kuka yakamata kiyi ba illa ki godewa Allah da asiri ya tono if not ,hk kina ji kina gani aikinki zai bar hannunki “nagode nagode har bansa kalar godiyar da zan maka ba ,a yau na k’ara sani duniya ba’akin komai take ba, nasan watakilla sunyi min hk ne saboda yadda nake takura musu akan aikinsu ,kuma fa ni ina yi musu hkn bada wata manufa ba sai Dan su tsaya akan aikinsu kar ya subuce musu Amman babu komai nagodewa Allah daya nuna min su a tafin hannuna ……
Tun daga wannan lokaci chairman ya nemi manyan mutane wad’an da yasan suna muamula da mahaifin me’ad Sannan ya nemi mahaifin sajeeda domin shine kan gaba a komai agurin mahaifinta,domin a zauna da shi a bashi hakuri a roke shi gafara a kan laifin da me’ad tayi masa.
sunje kmr yadda Chairman ya bukata sai dai da kyar alhj ediris ya yarda me’ad tashigo masa gida .
Bayan sun gama gaisawa suka soma magana akan abinda ya kawosu”alhaji jabir yace “alhj ediris abinda ya kawo mu akan batun yarinyarka me’ad ne..
Dady yayi sauron katse masa maganar ta hanyar cewa “ni bani da wata yarinya me’ad arayuwata ,yarinya daya gareni kuma sunan suhailat Dan hk kayi wata mgnr ban da wannan”
da sauri me’ad tashiga Jan gwiwowinta tana kuka “Dan girman Allah dady kayi hakuri ka yafe min ,kayi hakuri wallahi nayi nadama ka daina cireni acikin ya’yanka …kuka take sosai tana bashi hakuri “Dan Allah ku bashi hakuri ya yafe min wallahi na tuba bazan sake ba, ku gaya masa duk abinda yake so zanyi masa bazan sake ketare zancesa ba, na tuba dady nabi Allah da manzonsa nabinka ka taimakeni ka taimaki rayuwata banida kamarka ,kaine ubana, bani da wani uban dayafika kamin komai arayuwa ka inganta rayuwata ka gatantani kayi min komai ,kayi hakuri nasan ban kyauta maka ba …..