JIDDATUL KHAIRNOVELS

JIDDAHTUL KHAIR 10

💖💖 Jiddatul Khair*💖💖

By khaleesat Haiydar📚✍🏻

10….

Washegari da asuba bayan an idar da sllh Ahmad ya fito rike da karamar jakarsa, dakin Ummansa ya shiga ya gaisheta tace “Da asuba xaka tafi Ahmad?” Yace “Ehh kar nayi missing train din ne” Umma tace “To kun yi da drivern ya xo da asuba ne ko wa xai kai ka train station din??” Yace “Aa Abuturrab xai kai ni” Umma tace “Abuturrab kuma? yana garin ne? Lafiya bai koma aiki ba” Ahmad yace “Ehh satin nan yana nan yace min” Umma tace “Toh Allah ya tsare, kayi addu’a dai” Yace “Ameen Umma, in sha Allah” Har ya kai kofa tace “Har xaka tafi gashi ka mance da drugs din nawa” Juyowa yayi da sauri yace “Oops, kiyi hakuri Umma Abuturrab xai kawo maki anjima in sha Allah” Tace “Toh Allah ya kai mu, Allah ya kiyaye hanya” sallama ya kara mata ya fita dakin, yana fita compound ya dau wayarsa ya shiga kiran Abuturrab, Abuturrab ya daga yace “Gani na shigo layin yanxu” Ahmad yace “Alright” Sai da suka yi nisa Abuturrab ya d’an kalli Ahmad yace “Medical report din da nace xaka min din fa?” Ahmad yace “Idan aka yi how will it reach you?” Abuturrab yace “The plane coming from Abuja to kano, xan yi ma pilot din magana abokina ne, sai ku hadu ka basa” Ahmad yace “Flight din karfe nawa ne?” Abuturrab yace “karfe uku” Ahmad ya tabe baki, Can ya kalli Abuturrab yace “Toh wai ma me ya hanaka komawa gun aiki kake neman medical report din karya Captain?” Abuturrab yace “That is none of ur interest, kai dai kawai kayi min medical report” Ahmad yace “Toh baxa ayi ba” Abuturrab bai kuma ce masa komai ba har suka iso Station din, Ahmad yace “Yauwa pls captain i will text some drugs now to you, na umma ne, xaka siya ka kai mata, i forgot to do so yesterday” Abuturrab yace “A hakan xan siya magani in kai mata? Kana ganin babu kaya jikina” Ahmad ya kallesa, Jallabiya ce milk color jikinsa, Ahmad yace “Shi kuma wannan bargo ne a jikinka kenan, beside ni bance da safe ba, wani pharmacy xaka samu a bude this early, kaga dole dai sai anjima” bude motar Ahmad yyi ya sauka yace “Thank you” Daga haka ya rufe motar ya shiga cikin tashan, Abuturrab ya bi sa da wani irin kallo, bayan few minutes ya ja motarsa ya bar wajen, Abuturrab ya na isa gida text din Ahmad na drugs din ya shigo, lkci daya alert din kudin drugs din ma ya shigo, tsaki Abuturrab yayi ya cire jallabiyan jikinsa ya shiga bathroom. Karfe goma saura Abuturrab ya fito dakinsa, bangaren step mum dinsa ya fara shiga ya gaisheta, tana gyara press dinta tace “Ina xuwa da sassafen nan haka, kai da nake tunanin ka dau hutu ne don ka huta” Yace “Xan je siya ma Umma drugs dinta ne” tace “Tohhh, Ahmad din fa?” Yace “Ya koma gun aiki” Tace “Toh nima ka siyo min Panadol night…” Yyi murmushi yace “Toh in sha Allah” Ya juya xai fita tace “Captain shiru shiru kuma baka turo abun ba, kada a siye wajen ne fa” Yace “Ehh ina son in sanar ma Ummi ne….” Da sauri tace “Sai ka sanar mata captain? Ina ce yanda ka dauketa haka ka daukeni?” Ya d’an yi shiru, sai kuma yyi murmushi yace “Toh nawa ne kika ce?” Tace “1.7m” yace “Toh xan tura in sha Allah” Tace “Yauwa ko kai fa, idan ka dawo anjima ka shigo da akwai wata maganan kuma” Yace “In sha Allah” daga haka ya fita, bangaren Ummi ya shiga, waya ne kare kunnenta, hakan yasa ya jingina da kofa ya jira har ta gama sannan ya risina ya gaisheta, tace “Lafiya lau…” yace “Jiya na shigo kin yi bacci” Tace “Ehh da wuri na kwanta” Yace “Ohk, sai na dawo” Daga haka ya fita dakin ta bi sa da ido. Abuturrab na shiga mota yayi ma Ahmad transfer din kudin da ya turo masa, sannan ya nufi wani babban pharmacy, ya siya duk drugs din, bai mance na Stepmum dinsa ba, ita ma ya siya mata pack har uku na drug din da tace sannan ya dau hanyar gidansu Ahmad, Sallama yyi bakin kofar parlon aka amsa masa sannan ya shiga, Umma na xaune parlon da Maman Abdallah dake xaune kasa Jiddah na gefenta alamar gaisheta suka shigo yi, daga kai Jiddah tayi suka hada ido da shi ta sunkuyar da kanta, karasowa cikin parlon yyi ya xauna yace “Ina kwana Umma” tace “Lafiya lau Aliyu, ashe kana garin” Kallonsa Jiddah tayi jin sunansa a karo na farko, ya shafa kai yace “Ehh ina nan Umma, ya karfin jiki?” Tace “Ah Alhmdlh sauki ya samu” Mikewa yayi ya karasa kusa da ita ya ajiye mata ledan maganin hannunsa yace “Ga drugs din naki Umma” tace “Toh nagode son, Allah yayi albarka” komawa yayi ya xauna yace “Ameen” tace “Ya su yaya?” Yace “Suna lafiya…” Tace “Toh a kawo maka breakfast?” Tana fadin haka ta mike, yace “Aa umma nayi breakfast a gida” Umma tace “Toh ga awara da Maman Abdallah da mai sunan yaya suka yi da safe, u will like it” Ya d’an kalli Jiddah da kanta ke kasa, Umma ta mike ta nufi kitchen, Abuturrab ya girgixa kai da sauri xai yi magana sai kuma yyi shiru ya sauke boyayyen ajiyar xuciya, Maman Abdallah na kallonsa da fara’a tace “Ina kwama abokin Dakta” Babu yabo babu fallasa yace “Lfya lau” Jiddah bata dago ba ita ma tace “Ina kwana” yace “Lafiya lau” Umma ta fito kitchen, sai ga mai aiki rike da karamin tray me dauke da awara da sauce da pepper soup din naman rago a rufe a wani warmer din, dinning ta kai ta ajiye, Umma na kallon Abuturrab tace “Gashi can a dining area son” Ya d’an yi murmushi yace “Nagode Umma” Tace “Ko a kawo maka nan?” Ya bi dining area din da kallo sannan yace “Ohk” Nan kusa da shi mai aikin ta kawo ta ajiye sannan ta wuce, Maman Abdallah ta mike cike da ladabi tace “To Hajiya xata maki gyaran ne yanxu??” Umma tace “Eh to, ko kuma ta bari gobe ai tana nan, ko ba kwana biyu ta xo yi maki ba?” Maman Abdallah tace “Tana nan tukun wllh Hajiya, don bata ma sa ranan tafiya ba” Umma tace “Toh shkkn gobe sai tayi min gyaran” Maman Abdallah tace “Toh shkkn Allah ya kai mu Hajiya” Mikewa tayi tana kallon Jiddah tace “Toh mu je gobe sai kiyi aikin ko” Umma tace “To ki bar ta tayi kallo mana, tunda ke ba kallo kike ba” Maman Abdallah tayi dariya tace “Ehh kuma haka ne, tunda xan je maki kasuwa yanxu, ina fita hijabi kawai xan sa in tafi dama” Umma tace “Toh ki bar mata Abdallah ko baxai xauna ba” Maman Abdallah tace “Baxai xauna ba Hajiya, kiwuya ya gallabesa ai” Umma tayi murmushi tace “Toh sai kun dawo” Ko kadan Jiddah bata so haka ba duk da ba wai tana da niyyar bin ta kasuwan bane saboda tsoron kada wani da ya santa ya ganta a hanya amma xaman parlon ma bata so, Umma na lura da ita taga alamar she isn’t comfortable, hakan yasa tace “Ko kuma ku tafi kasuwan kawai tare kada ta xauna shiru” Maman Abdallah da har ta nufi kofa tace “Dama tare nayi niyyar xa mu je, da kika ce ta xauna tayi kallo ne yasa nima nace ta xauna Hajiya” Sosai gaban Jiddah ya fadi, Maman Abdallah tace “Toh taso mu tafi kasuwan” Abuturrab dake xaune parlon yana sauraronsu yace “Tunda kallo take yi ki bar ta tayi kallonta mana” Kallonsa Umma tayi da mamaki, that’s very odd of him, shi mutanen cikin gida ma baya shiga sabgarsu yayi masu magana balle wanda bai hada komai da su ba, Jiddah ta dago kanta amma bata ce komai ba, Umma ta d’an yi murmushi tace “Toh tayi xamanta” Maman Abdallah ta fita parlon bayan ta ce ma Umma sai ta dawo, Mikewa Umma tayi ta tafi kitchen sae gata ta dawo da karamin flask da mug ta ajiye ma Abuturrab tace “Kilan ta manta ne bata kawo maka ba…” yayi murmushi yace “Nagode Umma” Tace “Kana son madara?” Ya girgixa mata kai, tace “Yauwa nayi tunanin hakan, Ahmad ma bai fiye shan madaran ba” Sama ta nufa tace “If u are done ina daki” Yace “Alright” Bayan few minutes da tafiyarta ya daga kai ya kalli Jiddah, kanta na kasa tana wasa da hijab din jikinta maimakon kallon da aka barta tayi a parlon, ya bude flask din gabansa ya xuba ruwan Lipton cikin mug, wanda ya xuba ko rabin mug din bai yi ba, sae kamshi ruwan shayin ke yi, Calmly yace “Baki da wani damuwa a inda kike?” Ta dago ta kallesa sannan ta girgixa kai, bayan few seconds a hankali tace “Sai dai Baabarmu xa tayi ta nemana a gida” Kallonta yayi a takaice yace “Toh a mayar da ke wajenta kenan?” Shiru tayi tana kallonsa, can ta sauke idonta cikin sanyin murya tace “Iliyan xai iya sake biyo ni, ita ma xata iya kai ni wajensa” Abuturrab ya hade rai yace “Shine kuma xaki ce min Baabarki xata nemeki?” Bata ce komai ba, ya fara shan shayin hannunsa a hankali, tv ya dinga kallo kafin murya can kasa yace “Amma idan aka sauya maki shi wanda xai aureki yanxu da wani daban xaki amince da auren?” Kallonsa take babu ko kiftawa, yace “Ko baxa ki amince ba?” a sanyaye tace “Toh ai ban san waye shi ba” yace “Toh ni nasan sa” Tace “Toh in dai baya shaye shaye” Ya dinga kallonta sannan yace “Kina dai son kiyi aure kenan dama?” Hawaye ne ya kawo idonta tace “Baabarmu ce ke son inyi auren, kuma ai ba makaranta nake xuwa ba kawai sana’a muke yi” Bai kuma ce mata komai ba ya ci gaba da shan shayinsa, ta goge hawayen idonta, ya d’an kalleta yace “Wanda xan hada ku baya shaye shaye” A hankali tace “Toh” bude warmer din awaran yayi yana kallo yana d’an yatsine fuska, sai kuma ya bude na pepper soup dinma, lkci daya duk ya rufesu yace “Ki dauka ki kai maku can ki ci” Da sauri ta kallesa tace “Aa mun ci namu ai, kai dai ka ci ai naka ne” Ganin babu spoon a wajen tace “Bari in kawo maka cokali” Tana fadin haka ta mike tayi hanyar kitchen ya bi ta da ido sannan ya sake kallon warmer din awaran, ba a dau lkci ba ta dawo ta iso kusa da shi ta durkusa ta ajiye spoon din, sai kuma tace “In xuba maka?” Bata jira yace komai ba ta fara dibar masa awaran a plate sannan ta mika masa, calmly yace “Kwashe su nace baxan ci ba” Sauke idonta tayi a hankali sannan ta juye ta mayar cikin warmer din ta dau tray din ta mike ta wuce kitchen. Tana fitowa ta nufi kofa xata fita ya bi ta fa kallo yace “Kee, ina xaki?” Ta juyo tace “Xan xauna a waje ne” Authoritatively yace “Dawo nan ki xauna” a hankali ta dawo parlon ta koma ta rakube inda take xaune da farko ta xauna, ya ci gaba da shan shayinsa har ya gama ya ajiye mug din ya kalli agogo dake nuna sha biyu saura, mikewa yayi ya nufi kofa ya fita parlon, sai da ya shiga motarsa sannan ya kira Umma yace mata ya tafi. Yana cikin driving wayarsa ya fara ring, kallon wayar yayi ganin me kiransa ya nemi suitable place yayi parking sannan ya daga wayar, Daga daya bangaren aka ce “Captain da kansa barka da wuni…” Abuturrab yace “Ya kake Mu’axxam?” Mu’axxam yace “Alhmdlh Oga, Kayi scarce kawai wannan satin, daxu nake tambayarka Umar ke cewa ai baka shigo ba satin nan baka jin dadi” Abuturrab yace “Ehh ina kaduna” Mu’axxam yace “Toh ya jikin Captain!” Abuturrab yace “Alhmdlh” Mu’axxam yace “To maa sha Allah ranka shi dade” Abuturrab ya jinginar da kansa da kujeran motarsa a hankali yace “Kana ji na Mu’axxam?” Mu’axxam yace “Ina jin ka Oga” Abuturrab yace “Kana da mata ne?” Mu’axxam yayi dariya yace “Aa tukunna dai Oga Allah bai kawo lkcn ba” Abuturrab ya gyara xamansa yace “Ohk, wata yarinya na sama maka ko hakan yayi maka?” Mu’axxam yace “Ikon Allah, Oga ai baxa ka min xabin da xai cutar da ni ba nasani wllh” Abuturrab yace “To kar ka damu, in sha Allah xan maka duk wani abu da ya kamata na auren tunda nasan kilan ba wai ka shirya bane yanxu ae” Mu’axxam yace “Allah sarki Oga, amma wllh nayi farin ciki da wannan labarin naka, naji dadi sosai, dama tuntuni nake son yin auren amma babu halin yi sbda kasan komai yanxu tsada, shi kansa auren tsada, duk da iyayen nawa sun ma riga mu gidan gaskiya sai kanni da yayyi, da dangi, amma ginin da nake yi a kauyenmu shi ke cinye min kudi wllh….” Abuturrab yace “Babu damuwa, Allah xai rufa asiri, amma xuwa ranan alhamis ko Juma’ah ka dau leave din kwana biyu ka xo kaduna, a nan yarinyar take, but before then ma xa mu yi magana” Mu’axxam yace “In sha Allahu kuwa Oga, Allah ubangiji ya saka maka da alkhairi, ya biya maka bukatunka na alkhairi, ya ji kan iyaye da kakanni, wllh nayi farin ciki sosai Oga” Abuturrab yace “Maa sha Allah, xa mu yi magana” Daga haka ya katse wayar, wani ajiyar xuciya ya sauke… this is now almost settled saura mutanen Hayi kuma yanxu, tada motar yayi ya ci gaba da driving din nasa. Kawu Jibril sai muxurai yake daga inda yake xaune jin abinda Abuturrab ke cewa, Hansai ta marairaice tana wuri wuri da ido tace “Ni kuwa Alhaji sai nake ga fa kamar idan mun koma gun ‘yan sandan nan maganar nan babba xata xama, Iliya fa bai bari mun yi baccin kirki ba daren jiya a gidan nan, ni har na sadakar jiya xan mutu, saboda ka sanar min da xuwanka yasa na koma can gida karfe goma nayi ta jiranka sai gashi ka xo bayan azahar sannan na kawo ka wajen kawun nawa” Abuturrab yace “Ae baraxanar da yake maku ne dalilin da yasa xa aje police station din yanxu ba wani abu ba…” Abokin Kawu Jibril dake xaune tare da su yace “Ni da xa aji ta nawa kawai a tafi wajen me unguwar yankin nan gaba daya, naga yana fada aji, idan abun ya gagaresa shi sai mu koma gun ‘yan sanda don gaskiya wannan yaro Iliya d’an iska ne wllh, iyayensa ma ba isa suka yi da shi ba balle wani, amma gwara a fara sako mai anguwa a lamarin nan sannan ya kai mana gaban hukuma koko ya ku ka ga?” Hansai tace “Wallahi haka ma yafi, mu je aji ta bakin me anguwan tukunna” Kallonsu kawai Abuturrab yake with surprise, su fa ko damuwa da 6atan yarinyar basa yi, damuwarsu da tashin hankalinsu Iliya da ya sako su gaba, Kawu Jibril yace “Ko ya kace Alhaji??” D’an murmushi yayi yace “Ehh hakan yayi, aje wajen nasa” Hansai ta mike tana gyara takurarren mayafinta tace “Ba sai mun sha wahalan neman abun hawa ba da motarsa ya xo babba ce duk xata kwashe mu” Abuturrab bai ce komai ba ya mike shi ma duk suka bi bayansa xuwa kofar gida, sai bayan da suka shiga motar, Hansai tace “Ita Jiddah ganinta me sauki ne wllh, nasan tsoro ne yasa ta buya wani gun, amma ko ni daya sai in samota ai, bari dai a gama da tantirin nan” Ta madubi Abuturrab ya kalleta yace “Kinsan inda take kenan?” Da sauri Hansai tace “Aa amma nasan tana nan cikin hayi babu inda xata, kasanta da shige shige da yawace yawace tunda ba jin magana take ba, baxata rasa wanda xai boyeta ba na kwanakin nan kam” Abuturrab bai kuma cewa komai ba har dai suka isa gidan mai unguwar, xuwansu ya sa shi fitowa xuwa kan tabarmansa dake shimfide a waje da wasu dattijai uku ke xaune, Bayan an gaisa Kawu Jibril yace “Toh gashi dai mun xo gareka mai unguwa….” Sanin kawun nata bai iya magana ba yasa Hansai ta amshe bayan ta maka masa harara, ta marairaice tace “Mai unguwa muna cikin tashin hankali da fargaba wallahi, don a gaskiya bamu da wani tsaro xaman mu a hayi” Mai Anguwa yace “Ikon Allah, me ke faruwa? Har kin fita takaba ne Hansai?” Hansai ta sinne kai taki basa amsansa na karshe, Nan dai ta kwashe duk abinda ke faruwa karya da gaskiya ta sanar masa tana matsar kwalla da kyar, kallonta kawai Abuturrab ke yi da mamaki don maganganu da yawa ta canxa a kan yanda shi ta gaya masa, Mai Anguwa na jinjina kai yace “Ikon Allah Iliya dai guda, d’an gidan Malam Kabiru?” Hansai na shessheka tace “Shi wllh” Yace “Toh yanxu ke kin tabbata yarinyar na nan cikin garin nan, don lafiyarta shine babban abin dubawa yanxu…” Hansai tayi saurin cewa “Tana nan anguwar wllh Mai anguwa, ai nasan babu inda xata, kawai tsorata tayi yasa ta buya, yanxu idan na dage na kwalo mata kira xata fito wllh, kawai dai a gama da xancen yaron nan iliya tukun” Mai Anguwa ya girgixa kai yace “Toh yanxu xa a min kiran shi mahaifin Iliyan da shi kansa iliyan” Hansai ta xaro ido a mugun tsorace, Mai anguwan yace “Amma ke kika haifi yarinyar?” Hansai tace “Ehh ‘ya ta ce” Yace “Yanxu ki rasa wanda xaki yarda ya nemi auren yar ki sai wannan takadirin Iliya? Waye bai san halinsa ba a garin nan, garin yaya har kika amince ya auri yar ki, duk uwa ta gari ai baxata so ma yar ta wannan yaro ba” Hansai ta fara matsar kwalla tace “Wallahi mahaifinta ya rasu, yarinyar nema take ta gagareni, baxan boye maka ba wllh bin maxa take, to shi nan rufa mana asiri yayi xai aureta, bayan haka kuma da tsohon bashi tsakaninsa da mahaifinta ina jin, kuma ni bani da halin biya gaskiya shi sa kawai na sadaukar ai ba a cire ran shiryuwar d’an mutum, ni ban cire ran shi ma xai shiryu ba sannan ai gwara shi kiriniya kawai yake yi, ita fa bin maxa take wllh, duk iya bakin kokarina kan yarinyar nan ya ci tura, tsoro nake kada ta jajibo min abun kunya shi sa da ya billo da xancen aurenta bani da yanda xan yi na hakura, don kowa tsoronta yake sbda halinta, sannan yana da xuciya yaron, me yi ne shi wllh” Sake baki mai Anguwa yyi yana kallonta, Abuturrab ma kallonta yake ko kiftawa babu with shock, ta sharce majina tace “Amma tunda abu ya xo da haka in da wani shawara da taimakon da xaka mana kawai kayi mai anguwa mun baka wuka da nama don a gaskiya muna cikin hatsari” Ya sauke wani ajiyar xuciya yace “Ikon Allah, to yanxu dai xan sa ayi kiran mahaifin yaron da shi kansa yaron sai a san abun yi, idan naga sulhun baxai yiwu ba sai kawai ku tafi wajen yan sanda su ma idan abun baxai sulhuntu a gunsu ba kotu xa su tura ku, amma abu me sauki a mayar ma yaron nan kudadensa ita kuma yarinya a nema mata mai hankali wanda yaji xai iya ya aureta….” Hansai ta fashe da kuka tace “Duk ba sai an kai ga haka ba wllh, Allah xai dubemu maganar ta mutu cikin ruwan sanyi, banda ta lalata rayuwarta idonta ya bude da maxa me xai sa in yi sha’awar yi mata aure bayan abinda xan kai ta da shi ma bani da shi, duka duka shekarta fa sha bakwai, har nawa take xan dage sai na mata aure banda ta lalace” Kawu Jibril dai ba baki sai idanuwa, sauran dattijan dake xaune gun sai kallon Hansai suke wasun su na tirr da ita a xuciya, don ko min lalacewar naka baxa hadasa da lalatattce ba da yayi fice a gari, Abuturrab ya d’an yi murmushi shi dai bai ce komai ba yana kara jinjina halin Hansai a ransa. Sai da suka yi la’asar Mahaifin iliya ya iso, sai ga iliya ma da abokansa yan daba irinsa sun iso wajen, Mai anguwa ya dakatar da abokan dake kokarin xaunawa kan takalmansu don tabarman ya cika yace “Ku yi hakuri yan samari kuyi jiransa ga benchi can” Suna gunguni suka bar wajen, Abuturrab ya kafe iliya da ido, ba lebbensa ba hatta fuskarsa ya dafe saboda xuke xuke…..

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button