MUTUM DA DUNIYARSA 63 – 64

*_????MUTUM DA DUNIYARSA….!!????_*
_(ya dace ya gyara kansa)_
*_Bilyn Abdull ce????????_*
*_[63➖64]_*
…………..“kala-kalar abincin dake samar da karfin maza/mata (sperm), da
kuma kuzari a jikin ango da amarya”.
*_“HATSI:_* 1 Alkama ko kuma duk wani dangin abinci da ake samarwa daga gareta. 2 Shinkafa. 3 Wake. *GANYE*: 1 Albasa, Galik, Karas, Dankali, Kwakwa. *ƳAƳAN ITATUWA*: Ayaba, Mangoro, Tuffa, Abarba, Kankana, Lemo, Goba, Yazawa. *DABBOBI*: Tsuntsayen da suka halatta aci, Ƴan shila, Naman kifi, Agwagwa, Naman shanu, Hanta. *ABINDA DABBOBI SUKE SAMARWA*: Madara, Yogot, Ruwan zuma, Kwai, Bota”.
“HaƘiƘa su waɗannan dangogin abincin na kara ruwan maniyyi a jikin ɗan Adam, kuma suna motsar da sha’awar jima’i tare da samar da kuzari ga uwargida ko amarya ko shi kanshi angon. An samo daga sayyidina ALI KARAMALLAHU WAJAHAHU WA RIDIYALLAHU ANHU yace: wani mutum ya gayawa MANZON ALLAH S.A.W cewa bashi da ƴaƴa saboda rashin abinci mai sanya kuzari, sai MANZON ALLAH S.A.W ya umarce shi daya rika cin ƙwai”.
“Shawara ta farko kada ka taba yaudarar kanka da cewa dole sai kaga ( gaban ka ko azzakarin ka ). yayi girma cikin Gaggawa. kamar yadda Baka Iya komawa young boy haka azzakarin ka, Duk yadda ALLAH yayi halittar Sa, ka hakura da yadda ka samu kanka. Girman azzakari ba shine matsalarba, ka fahimci ya zaka Iya gamsar da Matar ka. Akwai hanyoyi da yawa ta yadda zaka gamsar da Matar ka. Akwai Matar da kalaman soyayyar ka kawai ya gamsar da ita. Akwai Wanda kiss kawai ya gamsar da ita. Akwai Wanda sai kayi da gaske sanna zaka gamsar da ita. Bari mu dauki matsala ta Biyu da kuma ta uku mu tattauna”.
“(Wato kiss & jima’i ) Kiss yana da matukar muhimmanci a rayuwar ma’aurata, Idan Baka taba kiss ba yana da kyau ka dauki 40minutes kana kiss da Matar ka. Amsar tana nan zaka bani. Jima’i yana bukatar wasa sosai ta yadda zaka Saki jikin ka kayi Mata wasa sosai, kada ka saka girman Kai zaka samu matsala. ka tambaya Matar ka, dan ALLAH Inaso Ki gayamin gaskiya menene Idan Na taba miki kikejin Daɗi. Idan kuma bata Baka amsa ba ka rubuta Mata a takarda ???? ta Baka amsa”.
“Akwai Wanda abinda takeso farko ka fara taba Mata (N+Ɗ) (kuyi haƙuri abinda zai amfanemu ake taɓowa, amma wlhy duk kunyarku ta lulluɓeni????), Akwai kuma Wanda kalaman soyayya zaka dinga Mata kawai su gamsar da ita fiye da zatonka. Duk waɗannan matsalalolin Ku da kanku ya kamata Ku zauna domin gyarawa. gaskiyar magana kusan 80% Na mutuwar aure a yanzu jima’i shine matsala. Duk mace Mai lafiya sosai, ta rasa jidaɗin jima’i gaskiya duk soyayyar ta ga namiji zata Iya rabuwa dashi. ka daina shan kowanne magungunan Saboda girman azzakari”.
*“MAN ZAITUN- ORIGINAL*: Idan zaka kwanta ka Shafa ko ba sex zakayi ba sannan kasha cokali???? 2. Yana taimakawa wurin karfin gaba. *MAN KWAKWA* yana taimakawa sosai ka dinga sha cokali daya ko cikin abinci ne. Waɗannan abubuwan Suna taimakawa sosai ka gwada”.
“Abinda muka faɗa dai-dai ALLAH ka bamu ladansa, wanda mukayi kuskure ALLAH ka yafe mana, ALLAH ya sakama malaman mu da alkairi damu gaba ɗaya.
سُبْحَانَكَ اَللَّهُمَّ وَبِحَمْدِكَ، أَشْهَدُ أَنْ لاَ إِلَهَ إِلاَّ أَنْتَ أَسْتَغْفِرُكَ وَأَتُوبُ إِلَيْكَ.
*Subhanakal-lahumma wabihamdik, ashhadu an la ilaha illa ant, astaghfiruka wa-atoobu ilayk.*
_Tsarki ya tabbata a gare Ka, ya Allah, da yabo gare Ka. Ina shaidawa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Kai, ina neman gafararka, kuma ina tuba izuwa gare Ka._
*(Wanan Addu’ar Tashi daga Majalisi ce, (Domin Neman Yafewa Ga Abin Da Ya Gudana A Cikin Majalisin. A’isha, ALLAH ya yarda da ita, ta ce: MANZON ALLAH, tsira da amincin ALLAH su tabbata a gare shi, bai taba zama a wani majalisi ba, ko ya karanta Alkur’ani, ko ya yi wata sallah face ya cika da wadannan kalmomi. (Sai A’isha ta ce: Ya MANZON ALLAH! Na lura cewa ba ka taba zama a wani majalisi ba, ko ka yi karatun Alkur’ani, ko kayi sallah face ka fadi wannan kalmomi. Sai ya ce; “Kwarai. Duk wanda ya fadi wani alheri sai waɗannan kalmomi su zama kamar hatimi ne ga alherin da ya aikata, wanda kuma ya faɗi sharri, sai su zama kaffara ne gare shi)*.
Tuni Sheikh Aliyu ya sulale yabar massalacin, yabar mutane da tattauna wanan lecture ta yau, koda yaje yima malam sallama ma sai wani sunkuy da kai yake tamkar yana gaban surukinsa, shi malam ma dariya ya bashi, amma saiya danne baiyiba, yasan dai wannan lecture ɗince ta yau takawo wanan sinne kan, haka Aliyu yake da tsananin kunya, ALLAH ya bashi sani kuma bai gazaba wajen bayyanama mutane, sai dai ko faɗar yake zaka sameshi mai tsananin jin kunya a garesu. Shiyyasa inhar malam yasan Aliyu zaiyi wa’azi a wajen da zasu kasance inuwa ɗaya to bayama kallon inda yake, dan kuma sakashi a wata kunyar zaiyi, yauma fitowa yay daga massalacin tunda Aliyu yafara bayanin magungunan can, daga soro ya zauna yana saurarenshi yana murmushi.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Kasan cewar cikin Maimunatu ya tsufa sosai sai dukkan kulawar Aliyu da jiddah suka koma kanta, yanzu haka kowanne dare a sashenta yake kwana bisa amincewar Jiddahn, dan koda ranar girkintane idan yazo wajenta zai kusan raba dare, idanma yana da bukatarsa daya samu nutsuwa zai tsaftace jikinsa yakoma wajen Maimuna ya karasa kwanan. Bawai dan Jiddah batajin damuwar hakan bane ta hakura, a’a a ganinta wannan adalcine, dukda har yanzu bata san raɗaɗaɗin koda laulayin cikiba Maimuna na bata matuƙar tausayi, tanada tabbacin da ace itace a wanan yanayin babu abinda zai hana Maimuna sadaukar mata da Aliyu harta haihu, dan ayanzu hakanma ranar girkin Maimunan idan yakasance ranar batajin daɗi sosai, kuma bazata iya karɓarsa ba, Aliyu kuma yanada buƙata takan amince masa yaje ga jiddah ya samu nutsuwa, haka itama idan Jiddah na al’adah Aliyu yanada bukata kuma lafiyar Maimuna ƙalau takan yarje masa yaje ga Maimuna ya damu nutsuwa, wannan adalcin nasune ke ƙara dasa masa ƙaunarsu mai yawa a cikin ransa, shiyyasa kullum burinsa ya faranta musu da soyayyarsa da kuma abinda ALLAH ya hore masa, sanan ya tsare musu mutuncinsu bisaga haƙƙoƙin da ALLAH ya ɗaura masa.
Randa kuma ALLAH ya kawo saɓani a tsakaninsu sukan zauna su fahimci juna wajen warware abin, dan kowa dai yasan zama na yau da kulkum sai ALLAH, tsakanin harshe da haƙorima ana saɓawa balle zaman kishi kona mata da miji. Amma idan aka sanyama zuciya salama sai kiga komai yazo da sauƙi, to hakane ga zaman su Jiddah, Saɓani yakansha gittawa harma Aliyu ya fahimta ya zaunar dasu yamusu nasiha da sauraren tushen lamarin, atake kuma zaibama mai gaskiya haƙƙinsa ya nunama mai laifi kuskurensa, shima kuma yakan samu daɓanin tsakaninsa dasu, wanan kam daduk wadda yasamu sukan yitane a ɗaki su kaɗai batareda ƴar uwar zamanki tajiba kota sani, kuma ko afusaka bazata saninba, saboda kowanne ya iya takunsa daga Aliyun har matan nasa.
Lokacin daya iso gidan saiya iske Jiddah na kuka rungume da Maimuna daketa murƙususu. Hankalinsane sosai ya tashi, bai wani zauna jan jikiba ya ɗakko hijjab ya sakama Jiddah da Maimunan suka fiddata mota, asibitin dake kusa dasu wanda Maimuna keshan kwanci sukaje.
Haihuwace gadan-gadsn dan haka suna zuwa aka shiga da ita ɗakin haihuwa, kasancewar asibitin na kuɗine baya rabo da ma’aikata.
Jiddah sai kuka take, tama kasa tsayuwa waje ɗaya, ganin a rikice take Aliyu ya kamota ya sakata jikinsa ya rungume yana lallashinta.
“Addu’a take buƙata Jiddah, kiyi hakuri kibar kukan, muyi mata fatan ALLAH ya sauketa lafiya kinji”.
Kanta kawai ta iya ɗaga masa, tareda ƙara lafewa a jikinsa tana sauke tagwayen ajiyar zuciya…………✍????
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*????????????