DAMA TA BIYU HAUSA NOVEL

DAMA TA BIYU HAUSA NOVEL

Amira na gama cin uncontrollable kukanta bacci ta dauketa with her son on her chest, kaman cikin dream taji Ana buga kofar ahankali, idanuwanta da suka kumbura ta bude ta kalli kofar to make sure she’s not dreaming sai taji yes it’s not a dream it’s real, ahankali ta Mike ta kalli abincin ta dake gefe da har yau Bata ci ba Sannan ta nufi kofa, she thought it’s Ismail dukda mostly kaman yanzun Yana wajen aiki, tunda ta kulle kofar dazun gata Kara budewa ba, da sauri ta sake komawa gaban mirror don kallon face dinta because he have warned her Kar ya sake ya ganta with swollen eyes don yasan kuka ne ke jawo swollen eyes. Tana dubawa taga idanuwanta sun kumbura beyond words, ajiyan zuciya ta saki ta nufi kofar da aka dan buga for like the forth time bayan tashin ta,
“Gani..Nan Yaya…” Ta fada heading to the door again, Ahmed daina bugawa yayi ya tsaya as he heard her talk, ahankali ta saka hannu ta bude kofsr, tana ganin Ahmed tsaye tayi Saurin sadda kanta kasa tana cewa
“Yaya…Ashe…Kaine…Ina.. kwana.. ” ta fada kanta kasa voice dinta Kuma na rawa, murmushi ya saki before saying
“Yes… it’s me…” Ya fada taking step into the room Bayan ta koma gefe don bashi daman wucewa
“Alhamdullilah…how are you…” Ya fada Yana Shiga dakin gami da maida kofar ya rufe,.
“Lafiya lau…” Ta fada Bata kalleshi ba sai jin wani irin kunyar shi kawai take, Bai Bata lokaci ba ya gane she have been crying don dukda Bata yarda ta daga Kai ta kalleshi ba ta Kira da yanda voice dinta ya shake,
” Ya baby…ya sunanshi…” Ya fada Kai tsaye Yana kallon yaron dake kwance yayinda shi Kuma ya zuane Kan stool dake kusa da mirror,
“Nasir…” Ta fada calmly,
“Wow… wonderful…Amira ta Zama mama…” Ya fada Yana Dan sakin Dariya, kasa daga Kai dai tayi,
“Don’t worry…dukda it doesn’t come in the way we all wanted we still celebrate the addition of life to our family… although nasan very few will understand that…” Ya fada cikin natsuwa, Shuru tayi Bata ce komai ba,
“Amira…” Ya Kirata calmly
“Na…am…” Ta amsa mashi finding it difficult to talk to him saboda kunya
“I know you have been through a lot….I feel it…Amma did you know it’s not the end of the world?… such things happens everyday…the good thing about mistake shine you get to learn from it…kowa yasan na farko is always a mistake na biyu Kuma ganganci…so I know what ever happened is a mistake and I want you to be strong…” Ya fada Mata, shuru tayi kanta kasa cikin ranta tana tunanin inama kowa will say what he just said Amma it’s kind of impossible,
“Look at me…” Fada Mata, ahankali ta daga Kai yaga idanuwanta kumbure Sosai, ahankali ya lumshe idanuwa yayinda ita kuma ta sauke kanta
“Me akayi…dukanki mummy tayi Naga idanuwanki Haka?..” ya tambayeta trying to be friendly so that she will confide in him, ahankali ta girgiza mashi Kai, .
“Then why the tears…why the swollen face…”
“Ba komai…Yaya…” Tafada mashi
“Aa… tell me…why kike kuka….nasna day ba yau abun Nan ya faru ba…in ma da wani kuka ya kamata ace by now kin Gama…”
“Hmmm…Yaya…baka…ganewa. “Bai Bari ta karasa ba yace
“No…Ina ganewa….tell me…I really want to help…dake na kwana cikin Raina…I want to help…” Ya fada Mata sounding very serious
“Yaya…ina cikin kunci…Ina cikin Bakin ciki….” Tana magana new tears na taruwa idanuwanta
“Ban da kowa yanzun…I feel lonely…if feel downgraded…I feel pain Yaya…kannena call me names …suna kirana da sunan da Ina ganin in sune suka Shiga irin wanann wallahi I won’t be hard on them.. Kuma.. ” sai ta Fara kuka sosai, Ahmed tagumi yayi Yana kallonta, it seem ta gaji da kuka, she looks so tired and fed up with the situation, kukan da take ne yasa yaron dake kwance motsi alaman zai tashi, Ahmed Kam cikin ranshi Banda tsinewa Wanda yayi Mata hakan babu abinda yake, yasan the person that did this is somewhere enjoying maybe, nikam nace you so much knew the person behind this, sanin ma ba just sani ba but friends and brother, close cousin, the cousin that suka sani da Mai idon Mata don tunda Suka bar kasar babu Wanda suke samun matsalar Mata dashi say wannan cousin din, shine zasu dawo su tardashi da mace rend handed, he will beg Kar su fadawa kowa, he will beg Kar a fada a gida don Kar a samu matsala da karatun shi, fada mashi suke shi kilan in ba Mata hudu ya ajiye ba Bai samun nutsuwa yanda he loves anything in skirt, duk yanda turawan Nan suke annoying skin color Bai ganin su Bai latsa ba sai indau Bai samu Daman ba, Amira daina kuka tayi sai shesheska kawai take don Kar yaron ya tashi Amma sai ya Mike zaune Yana murza idanuwa, Yana Gama bude idanuwan ya Mike tsaye zuww inda mamanshi take zaune tana kuka ya haye legs dinta, rikeshi Amira tayi tana kuka tana cewa
“I am in pain… nothing hurts…kaman… Kanin bayanka…ya bude baki ya zageka kuma… kayi magana…a goyi bayansu a Kara Maka wani zagin.. ” tafada cikin matsanacin kuka yayinda yaron dake hannunta ya dage sai kallonta kawai yake Yana tura yatsanshi cikin baki shi kuma Ahmed yaji wani irin radadi cikin ranshi sosai that idanuwnshi Suka kada sukayi ja sosai, kallon yaron dake hannunta yayi yaga he’s just like his mother, he is so handsome,
“Ki bar kukan Haka nan….”. Amira that still wants to talk about her pain ta cigaba dacewa
“Wai na jawowa gida Nan kunya…as if it’s in my plan to ruin my own youth…as if I enjoy being a slave and a prisoner in my own house….” Ta fada cikin kuka Sosai, Ahmed jin kanshi yayi so restless,
“Don’t worry… insha Allah everything will be alright…nasan you have been through a lot…I don’t want to give you so much hope but believe me it’s going to be alright….” Yafada Yana bude ledan daya kawo the first thing daya fiddo wayar daya sayo Mata sabuwa fil, Amira da face dinta ke cike da hawaye zaro idanuwa tayi gami da sa hannu tana goge face dinta da Bayan hannunta, sim din ya fiddo Yana cewa
“You’re not going to be so lonely anymore…” Ya fada Yana Mika Mata wayar da sim daya sayo Mata,
“Yaya…nawa..ne?..” ta fada cikin matsanacin mamaki
“Yes… it’s yours…jiya na Kira old line dinki sai Bai Shiga ba…so I called Ismail sai ya shaida min baki da waya tuntuni…I don’t want boredom to kill my little cousin ..so gashi.. ” ya fada Mata with a smile as she’s so surprised by the gift,
“Yaya…mummy…zata amsa…” Ta fada Tana kallon katon wayar that looks so huge to her,
“Ya zaayi ki barin ta San kina da waya… you shouldn’t let her know… don’t let anyone know…ya zama a tsakanin mu Dani dake da Kuma Ismail…”, Yafada Mata, batasan sanda ta saki murmushi ba, she feels so happy now, so so happy,
“Yaya… nagode…sosai…” Ya fada cikin voice dinta da Bai fita sosai. murmushi jin dadi shima ya saki before saying
“Ki bar thanking me… you’re my sister…” Kallonshi tayi tace
“Ya Zama Dole in gode maka… you don’t know what this means to me…. it’s like ka bani rayuwa… it’s like you have taken me out of prison…oh my God…” Ta fada cikin so much happiness.
“Pls it’s nothing…kawai just promise me you will be ok….ban son wannan kukan da kike…duk abunda zasuyi maki Kar ki damu…wata Rana zakiga kaman baayi ba…ok?..” ya fada Mata Yana kallon yanda ta amshi wayar daga hannunshi tana jujjuyashi with so much excitement, da sauri ta daga mashi Kai tana cewa
“Tou Yaya… nagode…” Bai Bari ta karasa ba yace
“Pls stop saying thank you…kin wuce kokai wajena…”ya fada Mata, Kai ta daga cikin matsanacin farin ciki, her happiness is written all over her,
“Duk abinda kike bukata don’t hesitate to ask me…” Ya fada Mata, da Sauri tace
“Tou Yaya…” sauran ledan ya Mika Mata Yana cewa
“Wanann is for my handsome Nasir…” Ya fada Yana Bata ledan da aka zuba su kayan da ya sawa danta, da sauri ta ajiye wayar tana kallon abubuwa kala kala, kallonshi tayi ta Kuma sauke idanuwa with so much happiness, she wants to say thanks for a million times Amma since yace she should stop thanking him ta daina,
“Dan bani sim pack dinki in dauki number ki…” Ya fada mata looking at how happy she is and he is so glad he is the cause of the smile, da Sauri ta Mika mashi sim park din, amsa yayi ya dauki number ta daga jiki ya Mika Mata pack din Yana cewa
“Kiyi charging wayar…. insha Allah later zanyi contacting dinki…” Ya fada Yana mikewa,
“Ok Yaya…tafiya zakayi yanzun…” Ta tambayeshi itama tana mikewa rike da yaronta dake makale daita Yana Shan hannunshi as he use to, kusa daita yazo ya Kama hannun Nasir dake bakinshi Yana cewa
“Ki hanashi shan hannu Kar ya Saba…” Yafada Mata Yana kallon yanda take tsaye a gabanshi rike da yaron kawai sai yafata imagining inda ya aureta da wata Rana Haka zata fito rike da dan da suka Haifa,
“Na hanashi…Amma sai ya maida hannun…” Ta fada mashi, kafin ta Ida magana har yaron ya maida hannunshi da aka cire daga bakinshi,
“Ka Bari…babu kyau…” Ahmed ya fada Yana kallon Amira da Babu Wanda take kallo sai danta, Yana fada Yana sake Kama hannunshi sai ya Fara kuka da sauri Ahmed ya sakeshi Yana cewa
“Am sorry ka cigaba Dasha wata Rana Kai zaa dinga Kira da mai Shan hannu…” Ya fada Yana Dariya, yaron kaman yaji abinda yace Sai ya maida hannunshi baki yacigaba Dasha, kallon Amira da Bata kallon shi yayi yace
“Na tafi…sai munyi waya…”
“Tou Yaya… nagode….” Ta fada kanta kasa, har Dan corridor dake tsakanin dakunan su ta rakashi Sannan tayi Saurin komawa ciki tare da kulle kofarta ta ajiye danta ya fara kuka ta Kashi bathroom yayi fitsari tayi mashi tsarki ta dawo dakin da sauri ta jona wayarta ta koma kusa da wayar tana jiran ya Kai hundred percent ta kunna ta Fara using, it’s not as if Tana iya kiran kowa yanzun kou tana da contact din kowa but she have Facebook and she still remembers her details sai Kuma she knows she can get almost the contact of her friends daga Kan face book, dukda Bata ci komai ba Sam Bata jin yunwa sabida yanda farin ciki ya mamaye ta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177Next page

Leave a Reply

Back to top button