DAMA TA BIYU HAUSA NOVEL

“Kai kana Ina?…” Was tambayar da alhaji yayi mashi
“Gida…” Fajz ya fara fada Bai Karasa ba alhaji yace
“Ina Fatima..” alhaji ya fada mashi Kai tsaye, ji yayi gabanshi ya mugun fadi,
“Hospital…” Ya amsa mashi
“Hospital?…Kai Kuma kana gida?…are you mad or something…hauka kake zaka Kai Yar mutane hospital barta Chan kaman Mara galihu ka koma gida?… gaskiya sai nayi maganin ka…”alhaji ya fada sounding so angry, faiz shuru yayi Bai San abinda zai fada mashi ba, kawai he wondered how he knows, it’s that mum dinshi ta fada mashi, he can swear iyami won’t do that at all,
” sai ka bar yarinya a hospital kaman Mara gata a kirani?… hauka kake?…so in Bata da number kowa sai dai ta mutu wajsn?…Anya kana da hankali kuwa…are you human?…am so ashamed to call you my child…” Alhaji ya fada sounding so angry,
“Did you know what…she did…” Fajz ya Fara fada thinking of how bintu have changed, before Bata son laifin shi, Bata son abinda zata fada yasa dad dinshi yayi fushi dashi Amma yanzun ya lura she’s different, wato ta hadashi da alhaji,
“I don’t care about what she did…how zaka har yarinya a hospital Babu kowa… nobody to pay her bills… nobody to take of her… wallahi sai ranka ya mugun baci…ka Bari in Kira hospital din in few minutes baka wajsn…” Alhaji ya fada
“Daddy… cikina…fa ta zubda..”faiz ya fadawa alhaji, alhaji da Bai Ida kashe wayarshi ba shuru yayi Jin abunda faiz yace, he can’t just believe bintu will do what he said, zubda ciki, abortion kenan,
“Ban son rashin hankali… just go to the hospital…” Alhaji ya fada mashi
“Daddy..she aborted…” Faiz Bai karasa ba alhaji yace
“Naji…go to the hospital…Kar in kuskura in Kira ace min baka Chan…” Alhaji ya fada mashi
“Daddy am tired…”
“Wai gardama zakayi min….hope baka Fara shaye shaye ba…ya zaayi inayi kanayi…hope you’re not taking something…”alhaji ya fada sounding so furious
“Daddy am sorry…zanje yanzun…” Ya fada ba don yaso ba, alhaji Bai Kara cewa komai ba ya kashe wayarshi, bangaren alhaji Kam he was so angry at abinda faiz ya fada mashi, in har ya bincika yaga da gaske ne she will really be dealt with, he sees no reason or what so ever da zaisa ta kashe Dan cikinta, Kiran hajiya kadijatu yayi Bayan ya kashe wayar tazo, he asked her what happened to bintu, shuru hajiya tayi har Saida ya sake magana tace
“Yace…Wai ta zubda cikin jikinta…” Hajiya ta amsa mashi
“What warrant that?…me yasa tayi hakan…” Ya fada sounding very angry
“Nima ban sani ba..sai ka tambayeshi…” Hajiya ta amsa mashi.
Fajz Kam ba don yaso ba ya Mike ya shjga bathroom ya sake wata alwallah don maganar shj da Amira ta Watsa mashi Wanda yayi dazun, sallah ishai yayi Yana zaune yana adua yaga wayarshi ta kawo haske, Amira kasa hakuri tayi, she was replying other but praying he calls back, Tana jin Shuru yayi yawa sai ta Kira shi, cikin second guda kuma ta samu ta kashe Tana tunanin what will she say when he picks the call, hakan yasa tayi Saurin yanke Kiran, she just pray it didn’t enter don tasan tana dailing tana Kashewa, she’s just restless.
Fajz na idar da sallah ya fita rike da wayar da mukulin motarshi, Shiga cikin wayar don ganin why wayar ta kawo wuta sai yaga miscall dinta, murmushi ya saki Yana redialing number, Yana Fara Ringing daga Chan Bangaren Amira ta zaro idanuwa tana cewa
“MTN Baku kyauta min ba….” Amira tana kallon wayar dake Ringing, she couldn’t let off, picking tayi
“Which kind flashing be this naaa…” Fajz ya fada Yana fita daga falo, Dariya Amira tayi tace
“Sorry… mistake nayi na kiraka…wata Zan Kira…” Tayi mashi karya
“Why must you lie…” Ya fada Mata
“Gaskiya nake Fadi…tell me what did daddy say…” Ta tambayeshi
“Ai bintu ce ta fada mashi na kaita hospital nayi abandoning dinta…so now am going back to the hospital…” Ya fada mata,
“Ok…hakan ya dace ai…Bai kamata ace ka bar ita kadai ba…” Ta amsa mashi”
“Then…meet me wajen Mana…kou Baki Shiga ba sai mu tsaya a waje ki tayani Hira…” Ya fada mata Yana bude kofar motarshi,
“Rufa min asiri…am not coming near that area….ni tsoro ma nakeji…” Ta amsa mashi tana dariya, Dariya faiz yayi yace”
“Otondo…Ashe kina da tsoro…as you stubborn reach you dey fear your fellow woman…” Ya fada Mata Yana Dariya, Dariya itama tayi tace
“Ba komai…ai ya Zama Dole in ji tsoron ta…Kuma kou ban jin tsoron ta ya zaayi in bar gjda yanzun in fita… it’s not possible ai…” Ta fada mashi
“Ai sai ki ce company ake kiranki it’s urgent… remember you’re a working class lady so you can be anywhere at anytime…” Ya fada Mata
“Nidai sai anjuma…ka gaidata…” Ta fada
“Zan fada Mata kince a gaidata…” Fajz ya fada Mata
“Wayyo Allah….Kar ka fada Mata Komai…she shouldn’t know we talk…concentrate on making her better…” Ta fada mashi, Nan dai sukayi sallama ya fada Mata in ya Kai hospital zai kirata ta amsa mashi da Kar ya Kira shi Kuma yace sai ya Kira ta, Yana zuwa hospital ya Tambayi wata nurse inda take aka nuna Mashi dakin da aka kwantar da ita, Yana shjga ya tarda mom dinta da Kuma yayarta, tana kwance Ana Mata karin jini it seem she looses lot of blood don Saida yasa Maigadi ya wanke mashi Mota daya dawo gidan shi, yanda suka hade Rai yasa shima ya hade nashi, kou gaidasu baiyi ba, zama yayi sai yaji Babu Dadi hakan yasa ya gaida mum dinta Amma sai Bata amsa mashi ba Kai tsaye ta Fara cewa
“Daman faiz baka da mutunci…Daman baka da hankali Ana maka kallon ka iya sallah ka kasa alwallah?…why will you dump my daughter at the hospital kaman wata Mara galihu…me yayi zafi Haka…at Least you should have drop her at home zaifi…kan wannan cin mutunci dakayiwa yata…” Hajiya ta fada mashj sounding so angry as sanda bintu ta farfado ta Fara Kiran alhaji sannan ta Kira family dinta da waya wata nurse,.
“Am sorry… but it’s her fault…tace zata zubda ciki…Kuma she did…why zan zo inyi zaune Kan wacce hates me so much to kill my unborn child…” Faiz ya fada face Dinshi daure
“Kai ka cika tantarin dan iska…” Yayar bintu Mai suna sakina ta fada mashi Jin abinda yace, she knows how much bintu loves fajz, they all know she loves him more than he loves her, she have lot’s of suitors Amma tace fajz, many people came and go Amma she said sai faiz, so it’s so unacceptable when he said she killed his child, wani irin kallo faiz yayi Mata alaman Kar ki Kara zagina, she’s his elder so he won’t say anything than to look at her
“Kowa yasan bintu Loves you… you don’t have to insult her integrity….ba dole sai kaci Mata mutunci ba…munsan baka son bintu Amma kaddara yasa ta aureka…bintu Bata son kowa kaman yanda take sonka…why will you take her love for granted…ya zaayi kayi Mata Haka… you dump her at the hospital kaman Bata da gata…” Sakina ta fada making it be all his fault, Baki faiz ya tabe before yace
“So you think am lying… you think karya nake Mata…ya zaayi inyi Mata karya…and point of correction…I have never taken her love for granted…in ban sonta Babu Wanda yaisa yasa in aureta… she’s evil…she killed my child.. ” faiz ya fada sounding very bitter,
“Enough dallah…ka fita ka bamu waje…zuwanka Nan Babu wani amfani… she’s my sister…and she’s her daughter…we can take care of her…” Sakina ta sake fada sounding more angry than he is, nobody will believe what he is saying because for sure sun San she’s the victim here, sun San he is at fault because she loves him, sakina will never believe him kou da kuwa kowa na duniya zasu yarda da abinda yake cewa, ba don komai ba sai don she knows how excited bintu is with her pregnancy, she’s always telling sakina her elder sister about how it’s going to be when she have that child and now he is telling her she killed it, she will never believe him,
“Daddy yace inzo…”fajz ya fada in I don’t care tune
“Then tell him…”sakina ta Fara fada Bata karasa ba faiz yace
“Ke ki fada mashi Mana…ni ban iya rashin kunya ba…” Ya fada Yana Dora kafa daya Kan daya, wajen karfe Tara bintu ta bude idanuwa, lokacin an Gama Mata Karin jinin, kallon mutane tayi sai ta sauke idanuwa zuwa Kan faiz ta kalleshi, shima kallon ta yayi before yace
“Hope you’re so happy now….hope you’re satisfied that you aborted him…kinji Dadi ai kou…Allah yayi maki sama da abinda kikayi min…”ya fada putting all the blame on her, Daman Haka issue suke, the moment Baka iya ba sai komai ya koma kanka, yanda ya fada he made it look as if she’s the only one with fault, it’s as if shi baj da laifi, it’s like he didn’t do anything at all, irin kallon da sakina take Mata is a questionable one, irin kallon dake tambayar did you do it din Nan, duk matsalar Daya zo maka in baka bi right approach ba sai komai ya juya maka, sai abinda ya kamata a baka gaskiya sai a baka laifi, wnanan ya koyawa kowa lesson, when someone hurts you make sure you handle it with care if not rashe zai iya juyawa da mujiya
“Sai ki zuba ruwa kasa kishi bintu…kin cuceni…kin zalunceni…I never knew Haka kike… you’re so evil…Allah yaisa ban yafe maki.ba…”faiz da ranshi ke Kara baci ya fadawa data fara hawaye, sakina kallon ta tayi don taga if he is saying the right thing or not, mum dinsu ta tafi gida leaving only her da faiz sai Kuma bintu data tashi yanzun, bintu was just staring at faiz dake Mata magana ciki kiyayya,
“I begged you to let it live….na baki hakuri…I even told you if sakinki zaisa ki barmin Dana…I will..why did you do this…” Faiz da ganinta made him feel so much pain ya fada kaman zaiyi kuka
“Kar dai ace he is saying the truth…” Sakina ta Tambayi bintu datayi shuru hawaye na zuba daga idanuwanta, she’s not really sad about loosing her pregnancy but she’s angry that he is making her look bad, yanda yake magana yake magana he made it look kaman he is totally innocent, Mikewa yayi don the more he looks at her the more he hates her, barin dakin yayi yayinda ita Kuma sakina ta dage da asking bintu da Bata iya magana sai hawaye, Saida ta girgiza Kai Kan cewa she’s innocent sannan sakina ta barta don she won’t take it likely with her at all.
Faiz na zuwa gida ya Kira Amira sai yaji layinta Yana busy alaman she’s on another call.
The following day faiz slept like a baby, it’s Saturday and he is resting don he won’t go to the office today, duk sanda ya tuna da abinda ya faru jiya sai ranshi ya baci,yasan very soon. Bayan sallah jumaa ahmed ya Kira faiz don Yi mashi barka da dawowa, Nan yaji voice Dinshi so low
“Wai…meke damunka… you sounds dull…” Ahmed ya tambayeshi
“Hmmm ahmed…kasan…I loose my baby…bintu ta samu miscarriage… yanzun ma tana hospital…” Fajz ya fadawa Ahmed
“Inna lillahi waina ilaihi rajiun….ya akayi Haka…ku dawo jiya…Kuma tayi bari?… it’s bad…”
“Eh… stress din jirgi ne…” Faiz ya fada regretting why he told him
“Allah ya kawo rayayyu…take heart…” Ya fada mashi. Dan Hira sukayi da ahmed yaga faiz is sad sai ya rabu dashi kawai. Daga Nan ahmed ya Kira Amira, tana picking ahmed da Dole yasa ya koma gidan jiya Suka Sha Hira sannan daga baya yace
“Dazun I spoke to your boss,…Ashe matarshi ta samu miscarriage…” Ahmed ya fada Mata, .
“Ayya…ni…banma sani ba…” Ta amsa mashi,
“Ok… yanzun ki shriya…na tashi daga office…zanzo mu tafi mu gaidata…” Ahmed ya fadawa Amira, Idanuwa Amira ta zaro tare da dafa chest dinta, she’s so scared
“Yaya…na…gaji…sosai… why not kaje…Kai …kadai…” Ta fada cikin rashin gaskiya na gaske, ahmed is a very smart somebody and he feels there’s something don yanda tayi magana alone says it all,
“Gani Nan zuwa…make sure you’re ready…” Ahmed ya fada Mata atakaice tare da kashe wayarshi because Bai son any gardama daga gareta.