DAMA TA BIYU HAUSA NOVEL

Wajen karfe biyu alhaji haruna ya Kira faiz a waya, picking yayi ya Dora a kunne, the first thing dayaji is
“Kana trying Dina kou….” Daure face faiz yayi yace
“Daddy if ni am not good enough for your office ka saka wani kawai…” Bai karasa ba alhaji haruna yace
“You’re very stupid for saying that… maganar danayi maka kenan…”ya fda kana jin fushi a cikin maganar shi
“Ai daddy na Lura da hakan… why will you set a spy a cikin workers Dina….nidai in baka son….”
“Dalla rufamin Baki….ai it’s all your fault …Sam baka daukan responsibility….baka yin the right thing…yau daka rigani fita mutuwa kayi… just be careful…”alhaji ya fada mashi tare da kashe wayarshi,
“Oho dai…”ya fada Yana ajiye wayarshi ya koma Kan duba file da aka kawo Mashi dazun Yana tunanin this is not good at all as instead su samu karuwa da gain sai yaga kudin da suka samu a production dinsu Bai Kai abinda suka kashe ba, he wonders what is happening,
“Is it my fault?…” Ya fada cikin matsanacin damuwa, shi dai yasan bai cin kou sisi a cikin kudin wajen, he is not extravagant, Bai daukan extra money a cikin kudin company don nashi ma ba kashewa yake ba, the only thing da yake yi is Bai monitoring in and out and products din, Bai taba zuwa Site din da ake kawo production din ba, iyaka ya zauna Nan office yasa ayi komai, he knows ba karamin tashin hankali babanshi zaiyi ba in har yaga wannan file din, last year yace ribar is too small compared to what they spent and now babu riba at all, that means something is really wrong somewhere, he is trying to point fingers at it Amma Sam he couldn’t, Sam Bai iyawa,ya kasa gano where the problem is, for the first time dayaji ya damu da matsala company din, ba don he cares about the out come ba saidon Bai son mom dinshi ta dingayi mashi fada tana cewa Bai damu da Daman da aka bashi ba, he doesn’t want anyone to feel kilan Yana kashe kudin company ne alhalin ba Haka bane, he hates sunanshi ya fito a Harkan kudi, Bai son abinda zai sa a dinga ganin he is spending the money, yasna quite alright he is not the only child, another thing he is afraid of is da akwai kudin da ake fiddawa family dinsu duk karshen shekara and it’s coming from the company, da wnanan company din ake badawa, Ana bawa yayyanshi kannenshi Mata dake gidan aurensu 100 thousand each sai yaran Kuma 50k each, now wnanan shekara Bai San how it’s going to be ba don last year kudin da aka Basu Bai Kai hakan ba Kuma sai da sukayi complaining, yasan dad dinshi ba zai taba rufa mashi asiri yace ya abasu daga cikin nashi company din don nashi jariri ne Kan sauran company. Tsoki yaja Yana cewa
“Nidai I didn’t touch any money…” Yafada Yana wurga da file din gefe tare da yin tagumi.
Yau kwana uku kenan da Amira ta Fara samun farin ciki as a result of wayar da Ahmed ya Saya Mata, babu Wanda ya San tana da waya gidan sai Ahmed da Ismail, subscription na data yayi Mata tayi downloading WhatsApp da Kuma Facebook, WhatsApp din is not fun at all don babu Wanda ya San number ta balle ta samu Daman viewing status din mutane Amma Facebook is a total joy as tayi recovering old account dinta Bayan ta saka email dinta, duk wasu abubuwan datayi saving a email sun dawo har da pictures dinta, batawa kowa magana Amma tana kallon picture din kawayenta da yanzun sunyi graduating, she really feels that, it really hurts kaga mate Dinka taking good step to life yayinda ita Kuma she’s at him with no hope of anything, har hawaye tayi tana kallon picture din, duk da akwai number dinsu a account dinsu, she feels like talking to them Amma tana fargaban taji kunya, she feels kilan sun San tayi ciki ne ta Diana zuwa makaranta, kafin a amshe wayarta she lied to them telling them she travels ne shi yasa Bata zuwa, tasan daga Bata kilan sunji gaskiya lamarin kou Kuma sun dinga nemanta Basu samu ba, she wants to talk to them Amma Sam Bata da Wannan courage din,. One of her best friend is even married, taga tayi posting picture din mijinta da Kuma new born baby, kallon date datayi posting ta duba taga duka batayi wata uku da haihuwa ba, taga many messages daga friends dinta Amma Bata iya amsa masu, she’s thinking they knew what happened to her, duk message data duba babu Wanda yake maganar abinda ya faru saidai a dinga
“Amira…Ina Kika shige…pls reply when you see this message…” take gani kala kala, wasu Kuma suce
“Nazo gidanku akace Baki nan….pls Ina kikaje…” ajiyan zuciya ta saki ta sauka daga online ta ajiye wayar gefe guda.
Ahmed Kuma Bai da abinda yake nema yanzun like ya nemawa amria hanyar samun kudi from home, he knows it’s possible, it’s really possible,. She can be home tana business dinta babu Wanda ya sani, he have asked around, wata sister Dinshi ya tambaya Kan online business because Yana yawan ganinta tana Dora Kaya Kan status dinta always, har gidanta yaje yake tambayarta how she’s doing it, Nan take fada mashi she have someone da kayanta ke sauki sosai,
.”kaga nayi Mata magana and kayanta na saukinl sosai don saids nayi surveying dinta Naga duk abinda zata ce 5k then wani wajen is 6k kou fin Haka, Bata dorawa kayanta kudi da yawa…asalima ba Nan kasar take ba Amma suna da manyan shaguna a kano da Lagos, sanann when it comes to international abubuwa ma zaka samu wajenta…sai nayi Mata magana nace inason Ina tallata kayanta in har na samu costumers Zan saya …I told her ta karayimin discounts Nan take fadamin kayanta Bata does masu kudi sosai Kuma I believe her…kaga shikenan na Fara…” Ahmed was so looking at her with confusion face,
“Wait a minute…ni Sam ban gane ba…Baki Bata wasu kudi kou wani Abu ba?…and kayan ya kike turawa wayanda suka Saya….” Ya tambayeta cike da mamaki, Dariya sis dinshi tayi before tace
“Ai Yaya ban Fara da kou sisi ba….dayake Ina cikin group dinta and a very huge Costumer of hers…kuma in aka saya iyaka kawai in tura mata kudin kaya in bada number Wanda zaaturawa da Kuma garin da mutum yake that’s all,…”
“Wow…” Ahmed ya fada Yana Mai jin dadin abinda ke faruwa yanzun don he sees amira in this business already,
“Wai Yaya why are you asking…” Ta tambayeshi tana kallon how excited he is,
“Ai abun ne da ban mamaki…Wai dame dame take saidawa don hq dukan status dinki nake dubawa ba…at times Dana bude daya naga kayane ban Kara duba sauransu…” Ya fada with laughter,
“Nidai Yaya in lefe zaka Fara hadawa just tell me I got you covered…” Inji sister Dinshi,
“Ai ba wannan zancen…pls fadamin…” Ta fada Mata
“Ai komai tana saidawa when it comes to to atampopi, laces, jallabiya, shadda manya da kanana, gadaje na waje, Kuma kayanta are very affordable don dukda Nima Ina Dan Dora abinda baa rasa ba cewa ake kayana da sauki….” Ta fada mashi,
“Oh madallah… gaskiya ki bani handle dinta in duba abubuwa in gani…” Ahmed ya fada Mara, Nan tace
“Kaje Instagram ka duba pretty-collections.1 kou Facebook ka duba hadiza ibraheem kou ka kirata ta +6013-350 7479 kou WhatsApp ta 08179324917,…” Ai tana Fadi yayi Saurin searching dinta Kan Instagram yayi following dinta ya Fara duba irin abubuwan da take dashi, he is so happy sosai, at least wannan zai taimakawa Amira sosai, daga cikin daki zata iya sanaarta ba tare da kowa yasan She’s into business ba, daman this is what he wants, ba sai ta fita ba Balle ace Tana zuwa yawo,
“Dear …pls ga number Nan…ki fada mata tayi adding agroup dinta…” Ya fada Mata,
“Number wacece Yaya…kou dai munyi inlaw bamu sani ba…” Kanwar tashi tafada mashi tana dariya.
“Lallai…nidai kawai don’t be too inquisitive… just help tell her to add the number…Allah yasa Bata wulakanci…”
“Aa Yaya Bata da wulakanci…kawo number…” Ta fada mashi, Nan ta karanta Mata number Amira yace ta ta sakata a cikin group din, tanbayar sunanta Ahmed yace
“Aisha…”yayi Mata karyar don Kar ta gano it’s amira,he wants it to be a secret don Bai son maganar ya Kai kunnen mamanshi tace he is not respecting him anymore, Nan dai sister Dinshi tayi saving number da sunan daya Bata, Yana komawa gida ya kirata ya fada Mata what he have planned,she was so excited Amma sau tace Bata da account number,goshi ya dafa before yace
“It’s alright…Ina da wata account da ban komai dashi…sai ki dinga amfani dashi before ki samu Daman bude naki…” ya fada Mata, Amira that his kindness yasa ta Zama so speechless tace
“Yaya…Kana kaunata da yawa…ban iya gode maka…” Bata karasa ba yace
“Pls ki daina….”
“Ok Yaya…Amma in na Fara posting Kaya a Facebook mutane zasu San nice…Kar mama ta kwace wayar pls…” Ta fada mashi cikin sanyimurya,
“Kar ki damu…zanzo gidan sai muyi magana…na bada number ki zaayi adding dinki cikin group din Kaya. .and incase wata number ta kiraki don’t pick..” ya fada Mata atakaice, Bata nemi jin why ba tace mashi
“Ok…”