DAMA TA BIYU HAUSA NOVEL

“Habib me kake a Nan…what brought you here….kazo don ka gumawa Amira ne or what…” Ahmed Bai Karasa ba yace
“Wai why are you asking such stupid questions…am I visitor a wannan family da zaka dingayi min Irin wannan tambayar?…or meye business dinka da zaka isheni da Such question…” Ya fada kaman Dan iska that he is,
‘you have got nerves…wato after everything da kayi…duk abubuwan da kayi…kazo like human…ba kowa zai San you’re a monster in human skin ba…”
“Pls…” Habib ya fada Yana rolling Idanuwa tare da dagawa Ahmed hannu
“Stay away from This… Babu ruwanka…” Habib ya fada Yana daure face dinshi
“I know why you’re saying this… it’s because kasan baa San muguntar daka shuka ba .. wallahi if har Amira ta Shiga damuwa sabida Kai she’s not going to face it a lot…Zan tabbatar da duk family sun San irin abinda kayi Mata… Casanova kawai…” Ahmed ya fada mashi, Dariya Habib yayi yace
“Wai malam Ina ruwanka….kou you’re the new boyfriend…well let me tell you something…I don’t care if the whole family knows.. it’s like you helping me to say what I want them to know….Amira is mine…I mold her to my satisfaction…I can still do it…” Habib ya fada Yana Dariya, ahmed sake kuluwa yayi saboda yanda yake magana babu kou single remorse kou kunya a maganar shi,
“Let’s see…” Ahmed ya fada mashi,
“Yaya…”sukaji an fada daga gefen su,duk juyawa sukayi sai ga asiya dake rike da hannun Nasir that is so dressed in his best clothes, Habib Bai kou kalli asiya dake mashi magana ba instead sai ya buge da Kallon this little him, last time Daya zo he was so stupid not to see him, Bai ganshi ba because Bai damu ba, he was taken away by fantasy Dake jiranshi a lagos
“Oh my…”Habib Ya fada Yana kallon yaron that run to ahmed, Ahmad daukanshi yayi Yana kallon Habib,
“Yaya… yaushe kazo.. ” asiya ta fadawa Habib Tana kallon shi, bude idonsu gidansu sun sanshi, so seeing him for long is like seeing ismail for long don Haka Dole su nuna jin dadin su if sun ganshi
“Jiya…” Habib ya amsa Mata Yana kallon the cutest kid he have ever seen,
“Yaya…shine baka zo gida ba…nasan su Yaya Amira Basu San ka zo ba…” Asiya ta fda seeing one of her brother,
“Ina Amira take…” Habib ya Tambayi asiya…
“Taje saloon…nasan ta kusa zuwa…kou kuma tazo har ta Shiga ciki…” Asiya ta amsa mashi, kallon yaron dake hannun Ahmed yayi yace
“Ya sunan shi…” Wani irin kallon haushi Ahmed keyi mashi yayinda shi Kuma Nasir ya dage da shafa hulan dake Kan ahmed,
“Yaya Nasir… sunanshi..dan anty Amira ne…” Ta fada mashi cikin sanyimurya, ahankali Habib ya matsa kusa da ahmed dake mashi wani irin kallo, kou kallon face din ahmed Baiyi ba ya mikawa Nasir hannu Yana kallon yaron, he have his eyes, he adores this boy, he very neat, Nasir zuba mashi Idanuwa yayi for a moment ya kalli hannun sai ya Mika Mashi hannu, hannunshi Habib ya Kama ya rike, kawia sai ahmed ya sakar mashi yaron ya koma Wajen shi, faiz na zuane cikin Motar shi looking at them praying he can hear abinda suke discussing, he is watching all moves dinsu, yaga yanda ahmed ke fushi and he wants to know what’s going on, it must be serious don Bai taba ganinshi cikin fushi Haka ba, Habib Kam ajiyan zuciya ya saki Yana kallon yaron hannunshi, wato this is his son, who cares if he is made in halal or Haram way, kawai he is a child and he is adorable,
“Ina su mummy…” Habib ya Tambayi asiya dake tsaye
“Suna ciki…Nima Zan Shiga ciki…naji kaman zas Fara…in bar maka shi kou in tafi dashi…” Inji asiya, ahankali ya mikawa asiya yaron Yana Cewa
“Ki Shiga dashi…” ya fada Mata calmly, har Asiya ta juya Habib ya sake kiranta, ahankali ahankali ta juyo ta kalleshi
“Ki ajiyeshi ki rike mashi hannu mana…he should walk.. ” ya fada cikin sanyimurya Yana son ganin yarom Yana tafiya, babu musu asiya ta ajiye yaron ta rike mashi hannu, Habib tsayawa yayi Yana kallon Yaron, ajiyan zuciya ya saki tare da lumshe idanuwa yayinda yake binshi, faiz was just watching carefully, ahmed na barin wajen Habib ya nufo motar faiz, Yana zuwa faiz yace
‘”pls waye wancan…I see kaman you’re angry at him….” Fajz ya fada yana Aduar Allah yasa ya fada mashi the real fact so that zai samu saukin abinda yake ji a ranshi, he wants to know this guy, why Amira almost killed herself because of him and why he’s is angry at him, ahmed Bai ce Komai ba ya fiddo wayarshi Yana neman layin Amira cikin damuwa, he wants to tell her so that seeing him won’t make her to be so surprised da zai jawo Mata damuwa,
“She haven’t been picking my calls…” Ahmed ya fada Yana dialing number Amira
“Wai what is happening…” Faiz ya sake asking ahmed,
“Kar ka damu…I want to speak to Amira ne….” Ya fada Yana jin wayarta na Ringing Amma Bata dauka, he knows bazata dauka ba, tunda sukayi kaca kaca daita Kan Maganar faiz take fushi dashi, she doesn’t want to speak to him. As he made it clear he knows what’s best for her ita Kuma tace Sam he is not not part of what is good for her, kawai she feels he wants to pass her on to his friend because shi Bai aureta bai Sam Bai san ba Maganar aurene a gabanta ba.
Amira dake sauka daga adaidaita na jin karar wayarta ta dauka sai taga Ahmed ne, daure face tayi ta maida wayar ta cikin bag dinta, kawai Bata son Magana dashi, she wants to show him Sam Bata son maganar hadata da faiz da yake son Yi so that he will stop it, kou kadan Bata son Bata mashi Amma he should know her stand.
Sai tunanin abubuwan da zai faru yau kawaii take, tasan wasu zasu dinga Mata kallon Yar iska, right now daidai take da uban kowa, duk Wanda yayi Mata zata fada mashi daidai da abinda aka Yi Mata, ta Riga ta ajiye wannan innocence din gefe guda, babu Wanda zai sake ci Mata mutunci Kan kaddaran rayuwar ta. Sanda akayi nata kwalliya sai da tace she’s not the one, the make up is casual Amma ba karamin kyau tayi ba, har kunyar shiga cikin hotel din take as she’s feeling she is over dressed, ga gold dinta data saka, hannunta Daya rike da bag din dataje da saloon dashi, sai Kuma Daya Kuma rike da ta rike hand bag dinta, she used small Vail Kan kayn jikinta, tana zuwa aka bude Mata karamin gate, lokacin da ta shjga taga lots of cars,
“Nima dai Zan sayi motar Nan…. wannan uban haduwa keke napep na hau.. ” ta fada tana Dariya under her breath, kou da ta shigo Bata daga Kai ba as tunda take baa taba Mata make up ba so she’s feeling some how.
“Amira… pick up Mana…” Ahmed ya fada Bai Karasa ba sai faiz Daya fara ganinta yace
“Gata Chan taxo…” Ya fada Yana kallon beautiful girl dake tafe wacce take son zame mashi fitina, relaxing yayi cikin Mota Yana kallonta yayinda ahmed ke tsaye a bakin kofar motar da ba rufe yake ba, ahankali ahmed ya juya ga Amira dake tafe with her head down, da sauri ya bar inda yake ya nufeta, shi kam faiz sau Kallon Amira yake saga inda yake zaune cikin Mota, yasan with yanda ta sadda Kai kasa ballai tasan Yana wajen ba har ya wuce, tana ganin ganin ahmed ta Dan sauya face
“Yaya.. ” ta fada as he gets closer to her
“Why are you not picking my calls…fushi kike dani…” Ya tambayeta,
“Aa…kawia I want you to know my stand…” Ta amsa mashi, bag din hannunta ya amsa yace
“Kin kyauta ai…now I want you to know something…muje cikin motata…”‘ ya fada Yana juyawa zuwa inda motar shi take, Amira batayi tunanin komai ba ta bi shi, faiz Kam yasan she won’t happy to see him Wanda hakan yasa ya sake lafewa cikin Mota Yana binta da kallo, Saida suka Isa wajen motar ahmed ya bude ya wulla bag din ciki sanna ya bude ya shjga expecting her to enter the car
“Yaya…what is it?…” Ta tambayeshi calmly
“Ki shigo ina son fada maki wani Abu ne.. “
“Yaya… ka fadamin daga Nan…kasan da akwai mutane da yawa Nan…har da su mummynka….ban son a wulakanta ni…” Ta fada mashj calmly
“Pls come in…maganar serious zamuyi dake…babu Wanda zai wulakanta ki…” Ahmed dake zaune cikin Mota ya fada Mata
“Aa…ban Shiga…am sorry…am trying to protect myself from any sort of assault…” Ta amsa mashi, he begged her to come in ba don komai ba don yasan if she knows Habib is here she will definitely loose her mind and in tana cikin Mota Haka zai sa babu Wanda zai San abinda ya faru Amma kameme Amira tace Bata Shiga, hakan ya Bata mashi Rai yace
“Shikenan…kawai ki tafi…” Ya fada Mata atakaice
“Hope you’re not angry at me…am trying to…” Bata karasa ba ahmed ya daga Mata hannu yace
“It’s alright… just go…. nagode…” Ya fada Mata, ahankali ta juya ta nufi hall din, shi Kuma Ahmed yayiwa fajz hannu ya taho su Shiga, ahankali fajz ya sauka daga cikin Mota yafito ya maida motar shi ya rufe.