DAMA TA BIYU HAUSA NOVEL

Fajz Kam tukin shi ahankali sabida Yana cikin damuwar da ba zai iya gudu ba Kar ya Samu matsala, yasan in har yayi gudu komai Yana iya faruwa, kaman Mai koyan tuki Haka ya dinga tuki, Yana zuwa gida yayi parking ya fito ya shiga bangaren hajiya, sanda ya Shiga har bedroom dinta ya tadda Bata Nan Amma yaji motsi a bathroom so yasan she’s inside, Zama yayi Nan Kan kujera Yana hawaye, fitowa hajiya tayi ta ganshi zaune Yana kuka cikin tashin hankali ta nufeshi
“Ayo… subhanallah… meye Haka. Kilode.. ” ta fada cikin matsanacin tashin hankali don tun Yana yaro abinda zai sakashi kuka is something very serious, tasan kou meye yasa yake kuka Haka ya Kai makura, bakinshi sai shaking yake ya kasa maganar wato this discovering is the worst he have ever made,
“Ayo!!!meye Haka kiloshele…” Ta fada cikin damuwa, ahankali ya daga Idanuwa ya kalleta yace
“Na…bincikowa…kaina…” Ya fada cikin hawaye
“Me ka tonowa kanka…me ka binciko…” Ta fada Yana daga kanshi don kallon idanuwan shi,
“Iyami… you won’t believe what Zan fada maki…” Ya fada Yana goge face dinshi
“Ya akayi kasan I won’t believe you…say it first ” ta amsa mashi tana tsaye gaban shi,
“Ba last time na fada maki maganar yaron da ke kiranta da mamman ba”
“Yes I remember…what about it.. ” ta fada atakaice, hannu faiz ya sa ya goge new tears before yace
“Iyami…he is her son…” Ya fada cikin damuwa, wani irin kallon takaici dayasa ya Dan ja baya yayi, sai da ta Gama Kallon shi tace
“Ya akayi kasani.. “
“Iyami… gidansu naje na Tambayi Maigadin Gidan
“Congratulations…sai da nace Kar Kayi Mata bincike Amma baka ji ba.. anyway ba wani Abu bane ai…kanka farau soyayya da bazawara?…hope Dan Daya ne…” Ta fada not taking the whole thing serious and she’s surprised her idiot son is crying because of this
“Iyami batayi aure ba… she’s a single mother…” Bai karasa ba iyami tace
“Yeeyyy!!!!” Ta fada cikin mamaki da Kuma tashin hankali.
Alhamdullilah
3/15/21, 9:12 AM – Ummi Tandama: 61
“Wai wannan Yarinyar….Kash….wato ance don’t judge book by it’s cover….am so disappointed…” Hajiya kadijatu ta fada cikin damuwa Sosai da Jin abinda ya fada Mata, she never expected to hear such from such angle, ahankali ta koma ta zauna tare da dafa goshinta, ta Dade Bata ji abunda ya tada Mata hankali Haka ba, shima faiz ya sake shiga sabuwa tashin hankali with her reaction, ta nuna hakan Sam Bai dace da ita ba and he feels ya kamata hakan ya dameshi
“Wai are you sure Bata da aure…this things doesn’t happen a Nan arewa… girls are decent…most girls Ana sakinsu in aka gano Basu da virginity dinsu balle Kuma ace yarinya tayi ciki tayi aure a gidansu…” Hajiya ta fada sounding so disturbed,
“Iyami that’s why am crying…abun yayi min tsaye a Rai…. it’s so unbelievable…” Ya sake fada Mata cikin damuwa
“Ai sai ka rabu daita…” Bata karasa ba yace
“Anya Zan iya…one thing I realized is that… cousin dinta ne yayi Mata ciki…” Ajiyan zuciya hajiya ta saki tace
“Allah ya raba yaran mu daga sharrin cousins… they’re the most dangerous being in family…zaka saki jiki dasu suna Shiga suna fita a gidan ka ka Basu ci ka Basu Sha Amma still Bai hanasu suyi maka barna…shi yasa wasu daga cikin families dinku suke ganin kaman ban da kirki sosai….I know how dangerous some family members are…” Ta fada kaman tana da experience kan issue din, you never know.
“Iyami ya zanyi…pls advise me…”
“Ka rabu daita… thank Allah Bata wani baka hankalin ta balle kaji wani iri…. that girl doesn’t deserve you… kaje ka zauna da matarka…in kana bukatar wata matar ka nemi wata ka Kara…Amma not her. ” Ta fada mashi atakaice feeling down about what she’s saying Amma it’s the right thing, kowa yasan Babu uwar da zata yarda danta ya tashi ya auri single mother, faiz was looking at her with eyes full of tears, idanuwa ya lumshe yace
“Iyami…Zan iya…” Ya tambayeta cikin ruwan sanyi
“Ya Zama Dole ka iya ai…who will let you marry her….me?…ok in na yarda…what about dad dinka…kasan kou giya yasha he won’t let that union…so just let it be….” Ta fada mashi, faiz dafe goshinshi yayi Yana jin kan shi na harbawa, it feels so hurt sosai, shi kanshi yaji feeling da yake ji kanta ya ragu sosai Kan few hours back, the thought of her being in same bed with another man yasa duk yaji Babu Dadi, duk ta fita ranshi, kawai jealousy yasa ta tsire mashi daga zuciya, ahankali ya Mike yace
“It’s alright…iyami….Bari in koma gida ..” ya fada Mata Cikin sanyimurya
“Ok…make sure you behave yourself…Kar kaje ka fadawa Bintu abinda ya faru.. alright?..”
“Yes iyami… nagode…” Ya fada Yana ficewa daga dakinta, he feels so sad that yau sai da ya koma gidan jiya wato siyan giya before going back home.
Habib Kam wanda ya dauko shi na direshi a hospital ya dawo Wajen reception, he had deep cuts a bakinshi da yawa don yanda yake magana ta datse mashi Baki da kwalba duk inda fatar bakinshi ya taba hakoran shi sai da ya yanke, sai da akayiwa hannunshi dinki, magani aka bashi yayar shi sai Kallon shi take Ana bashi treatment, wayar shi sai Kara take yasan matar shi ce don Ringing tune dinta daban, Bayan an Gama aka rubuta mashj magani ya biya da card dinshi, waje suka fita da yayarshi, ta kalleshi taga yanda yanayin shi ya sauya lokaci guda bakinshi ya kumbura sosai
“Pls ka fadamin…da gaske take?…Kai kayi Mata ciki…”
Habib kasa amsawa yayi ya samu waje ya zauna, kou kadan Bai bakin cikin abinda zai biyo baya da family Dinsu suka San he is responsible for the baby, he is willing to stay and apologize, Daman yasan ya Zama Dole su sani tunda ya Riga yayi Wasa da Daman shi, yasan inda da farko daya dawo ne ya aureta Babu Wanda zai Sani saidai kawai a gani kaman so da kauna yasa ya aureta despite her son, kawai abinda yayi mashi tsaye a Rai is the fact that Amira ta daga abu ta bugeshi and she’s still saying she’s going to kill him, wannan kawai ne ya tada mashj hankali, he knows she’s the softest person he have ever met, kou last time Daya Kirata ta dinga mashi magana da zafi zafi Dariya kawai yayi, Bai San she can hit him ba da har zata Dora mashi kwalba, she breaks his mouth
“Da Kai nake…nace are you responsible Habib…”yayarshi ta sake asking Dinshi, ahankali ya daga idanuwanshi da suka sauya kala saboda zafi da Kuma bakin ciki tare da tashin hankali ya kalleta, he have this looks of regret,
“Subhanallah!!!!!!…” Yar uwarshi ta fada Tana kallon shi,
“So da gaske ne… Habib ..why…” Ta fada Tana kuka tare da dafe bakinta, Habib Yana son Magana Amma yanda aka Kama mashi Baki da dakin is making it difficult for him to talk
“Inna lillahi waina ilaihi rajiun…wane irin mutum ne Kai…wane irin mutum ne zaiyi irin abinda kayi?…kasan Kai kayi Mata ciki Amma I speak ill about her Amma kou sau Daya baka taba yunkurin fadamin gaskiya ba…”ta fada cikin kuka, sake kallonta yayi yace
“Am… sorry…” Ya fada kaman bashi ba, yanda yake magana kaman Yana koyon magana
“Sorry kace… sorry…baba Muhammad yayi maka komai…ya baka kulawa fiye da yanda aka bani a gidan Dana tashi…Bai bsmbamta ka da kowa ba…he loves you fiye da yaran shi…sai kuma ka saka mashi da Haka…Habib why…ai Ina ganin kou Amira zatayi zindir a gabanka Bai kamata ka kusanceta ba in har ka San halaci ba…” Yar uwarshi ta fada Tana kuka Sosai not minding wayanda ke wucewa suna Kallon ta, she feels so disappointed, she’s so hurt,
“Sor..ry…shar…rinn….Shai….Dan…ne…” Ya fada ahankali saboda tsoron bakin ciki
“Shaidan….Amma gaskiya wannan shaidan ya cuce ka…ya Gama damu….bamu da uwa bamu da uba…dangin da suka damu da harkokin mu Kuma ka lalata muamular mu…” Ta fada cikin kuka tana Zama kusa dashi a inda yake zaune, hade Kai da gwiwa tayi tana kuka Sosai, she’s hurt beyond words, sai da taci kuka ta koshi ta Mike tana Cewa
“Yanzun zamu je Chan gidan baba Muhammad…” Da sauri Habib ya kalleta with fear, abubuwan sun mashi yawa sosai
“Yes..” ta fada mashj tare da Kara dacewa
“Duk abunda zaayi maka ayi… wallahi kou kasheka sukace zasuyi Basu da laifi…” Ta fada tana goge face dinta
“Pls…aa…” Ya fada sounding so calm kaman ba arrogant Habib ba, abinda Bata sani ba is neman Mata a jikinshi yake, kou a yanzun inda zai samu mace he will go for her dukda his system have been compromised, he loves women Kuma Haka Allah ya halliceshi
“Dallah tashi mu tafi…” Ta daka mashi tsawa, ahankali ya mikr, Yana fargaban abinda zaayi mashi yanzun that duk family are available har wayanda ke nesa suna cikin gari because of auren nazifa, ahankali ya Mike suka fita ta tsaida adaidaita.