DAMA TA BIYU HAUSA NOVEL

DAMA TA BIYU HAUSA NOVEL

Wajen karfe 8 da rabi Ismail ya isa gidan grandparents dinshi inda yayi parking Amira ta sauka gabanta na faduwa, she’s just shy telling them he screws her, tasan abjdna suke son ta maimaita masu kanen, motar dad dinta ta Fara ganewa,
“Zan jiraki cikin Mota…” Ismail ya fada Mata Yana relaxing cikin Mota, ahankali Amira ta Shiga, dare ne Amma gidan da akwai haske sosai kasancewan su yaran suna Kula da gidan dukda babu iyayen su ciki sai babban yayansu da iyalanshi, kowa sau Magana yake da shigan Amira sukayi shuru suka amsa sallamar ta, alhaji Muhammad Kam is not saying anything sai girgiza kafa kawai yake, gaidasu tayi suka amsa, already tana da courage din magana a gaban manya tunda tana haka a wajen aikinta, tana yawan yin presentation,in har zaka iya magana a gaban alhaji haruna then a gaban kowa zaka iya, he is a man da yake da wani irin kwarjini fiye da tunani, Kuma in kana magana zai kafe maka idanuwa don yaga courage Dinka, hakan yasa she’s willing ta Fadi abunda ya faru, the deed have been done, tafi minti goma da Zama sannan Habib ya shigo da sallama shima, yanayin shi alone ya nuna he has been messed up, sallama yayi wayanda suka gandama amsawa suka amsa, alhaji Muhammad kafashi yayi da Idanuwa Yana Kallon shi, he is just looking at him with no single word out of his mouth, Daman ba mutum bane Mai don hayaniya dukda shi ba kanwar latsa bane, babu wasting of time babbansu ya kalli Amira yace
“Fatima…kinsan kiran da akayi maki Nan??.” Ya tambayeta, ahankali Amira da kanta ke kasa ta girgiza mashi kai, Alaman aa
“Well kin Fadi wata magana dazun..most of us here bamu ji abinda Kika fada ba.. bamu San if it’s true kou Kuma karya ba…muna son ki maimaita what happened tsakanin ki da Habib…Kar ki Saya komai… Tell us abinda ya faru…” Babban yayansu alhaji Mai suna alhaji abdulrahaman ya fada Mata, ahankali ta daga kanta ta kalli inda Habib da kanshi ke zaune sai ta Fara hawaye, cikin kuka ta fada masu yanda ya yaudareta, duka babu abinda suke cewa sai Inna lillahi waina ilaihi rajiun, wani daga cikin su ya Fara cewa
“Amma gaskiya Fatima ilimin addini baiyi maki amfani ba…we know Habib is a devil in human skin Amma Kama da naki kason, …duk yanda ya nuna Yana sonki Yana son jikinki inda Baki bashi dama ba hakan bazai faru ba…inda kilan kina sharing irin abubuwan da yake fada maki da kilan an Baki shawarar Kar ki yarda….” Ya fada Mata sounding so angry at her, skuka kawai ta dingayi,
“Habib abinda ta fada da gaske ne?…” Wani ya Tambayi habib da these days babu abinda yake son yazo ya wuce kaman wannan ranar, yasna in har ya dawo da maganar son Amira da akwai matsala and irin wnanan most come in, yasan hakan zai faru, lot more zai iya faruwa,
“Eh.. ” ya fada, ai Bai karasa ba baban Ahmed ya tashi ya haushi da duka, atakaice wajen su uku sukayi mashi ligis, sai kace Dan Karamin yaro, shi dai alhaji Muhammad is still speechless, Amira enjoys this, she’s having fun when she heard this hot slap from nowhere, in zaa kasheta Bata San Wanda ya mareta ba
“Duk laifin ku ne… you’re at fault Also…an San Mata da wayau da kaifin basira….ya zaayi ki zauna such abu ya dinga faruwa bazaki fadawa kowa ba….ya zaayi bazaki fada ba!!!” Wani Wanda suke Kira da uncle Usman ya fada Yana dukanta, kuka kawai take sosai
“Kaci ubanta….Yara su zauna suna kinsan mugun Abu cikin gida?…did you think bamu da asali da zaku lalata mana suna…” Wani ta fada cikin wayanda ke dukan Habib, sai da aka zanesu Amma fa na Habib is beyond words, sai shesheska kawai yake kanshi kasa, the good part is ansan ba laifin Amira kadai bane, right now alhaji Muhammad hates her for keeping such huge secret, yanda yake jin haushin habib Haka yake jin haushin Amira, wato su ta Rainawa hankali da take cewa raping dinta akayi, Amira sai kuka take har da majina, she cries like a baby, tasan he is not only at fault har da nata laifin Amma she takes it as love, kowa yasan we always do things to make our love ones happy, that’s what she did, Bayan kowa ya zauna babu abinda ke tashi da shesheska Habib da Kuma kukan Amira,
“Wallahi zaku ci ubanku….Kuma let me tell both of you something…sai kun auri juna kunje kun zauna da juna da danku…”alhaji abdulrahaman ya fada out of serious anger, ai Nan Amira ta Shiga wani irin matsiyaci tashin hankali, duk Basu San Yana da aure ba, babu Wanda yasan he is married,
“Yana da aure!!!” Amira ta fada out of control,
“Mahaukaciya kawai.. ” inji Daya daga cikin uncles dinta
“Kuma akace zaa hadani dashi…kashe kaina zanyi…” Ta fada cikin matsanacin kuka,
“Ki rataye kanki…” Wani ya amsa Mata, ai kowa na fadin albarkacin bakinshi, baa Dade ba akace Amira ta tashi ta Basu waje, Habib na kwance kasa sai Nishi kawai yake ,he can’t move an inch, nishin shi na Neman daukewa, he just pray it’s all, Tana kuka ta Mike ta fita tana zuwa ta bude motar Ismail ta shiga ta zauna Tana kuka, she just pray Wasa suke don in akace zaa hadata da Habib an Gama daita,
“Ka tashi ka bamu waje…” Wani ta fadawa Habib, ai kasa Tashi yayi, Daya daga Kai sai ya sake langabewa ya Fadi kasa, da aka gan da gaske ne aka sa Daya daga cikinsu ya kaishi hospital, Ismail tambayar abinda ya faru take kuka Haka yayi tayi Shuru ta kasa magana.

Saida koina ya nutsu uncle abdulrahaman yace
“Yanzun meye abunyi…wane shawara kuke ganin ya dace…don tunda an San he is responsible Bai kamata ace ya barta haka Nan ba…kowa yasan cewa babu Wanda zai bar danshi yace zai aureta…. duk inda zata ma zagi zata jawa family dinmu…Amma yanzun na Bari kowa ya Fadi abinda ke ranshi.. ” ya fada Yana kallon kowa da kowa har da alhaji Muhammad da tunda yazo Nan Babu abinda yake cewa sai kallon su kawai yake
“Ai kawai a hadasu…babu wani two ways about it.. ” wanda ya fara magana Bai karasa ba alhaji Muhammad yace
“Baa hadamin ya da wannan shaidanin…” Ya fada breaking his silence,
“Why?…”alhaji abdulrahaman ya tambayeshi
“Because I said so…Baku ganin yaron Nan Baiyi min hallaci kou kadan ba… it’s better yata ta zauna a gidana har tsawon rayuwarta da ta hada zuria da maciyin Amana irinshi…yaron da nayi nurturing baiji kunyata ba…baiji tsoron Allah ba…yayiwa yata Haka….” Alhaji Muhammad Bai Karasa ba wani yace
“The mistake is from both of them…ba Habib kadai yayi laifi ba…ita Amira data boye abinda yayi Mata taki Fadi fa?… both of them have to be punished…ba Habib kadai zaa hukunta ba…” Still wanda ya fara Magana Bai karasa ba alhaji Muhammad ya sake cewa
‘”ban damu da duk irin hukuncin da zakuyi mata ba…kawai dai banso hada zuria da Habib…”
“We understand your pain.. ” wani ta Fara fada Bai Karasa ba alhaji yace
“Non of you will ever understand my pain.. ” ya fada cikin muryar dake Nuna he is in so much pain and agony
“Babu Wanda zai Gane halin da nake fiki ace yadon da na Raina ya rasa wacce zai lalata sai yata..” ya fada Yana dafe goshinshi Yana tsayar da maganar Da ya farayi as kuka na neman kufce mashi
“We understand…yaran zamani sai hakuri…kana naka suna nasu…all of us sun San kayi kokari da Habib, ai ni na raini Yar uwarshi Amma we all know you gave Habib what is I didn’t give saudatu,..kayi hakuri…”
“Nayi hakuri….in banyi hakuri ba ya zanyi?…will that change anything?..” alhaji ya fada Yana murza idanuwa, ganin alhaji Muhammad is in a very bad mood yasa alhaji abdulrahaman yace
“Yanzun dai kowa ya tafi… Muhammadu kaje ka huce… zamuyi magana Nan da sati guda…”
“Aa…I don’t need Time to heal…bana bukatar time to heal…kawai bana son jin maganar hada Amira da Habib…abinda ya faru is destined to be…”
“We know…” Alhaji abdulrahaman ya fadawa alhaji Muhammad cikin rarrashi, don yanda yake magana kasan dannewa kawai yake Bai kuka but he is broken to the core, it’s like it happened today and not More than 4 years ago, inda wani Chan yayi zaifi mashi sauki sosai Amma kasan cewa Wanda is ciyar ka shayar ka tufatar sannan ka bawa muhallin da all the necessities of life yaci amanarka da zafi
“Yanzun dai zamu samu haduwa next week sai a San abunyi…” Alhaji abdulrahaman ya fada, Nan sai aka rufe taron da adua.
Amira Tana zuwa gidan ta fadawa mum dinta abinda ya faru da Kuma abinda taji uncle abdulrahaman ya Fadi, Idanuwa lumshe hajiya tace
“Hakan is the only way ai….in bashi ba ina Zaki samu mijin aure…kawai hakuri zakiyi…” Bata karasa ba Amira ta zube kasa tare da rike mum dinta Tana cewa
“Dan Allah mummy Kar ki ce Haka…Kar ki yarda a hadani dashi… ranar dayazo ya fadamin Yana da matar da zai aura a Lagos…nasan yayi aurenshi… wallahi I will rather die than to be married to him…” Amira ta fada cikin matsanacin kuka
“Hmmm kimayi adua ya yarda ya aureki…ai yanzun you’re not like every lady out there…he is the father and the person beyond all this mess…so Baki da zabi…da ya wuce kije ki aureshi… you have no choice my dear…” Hajiya ta fada Mata atakaice tana goge face dinta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177Next page

Leave a Reply

Back to top button