DAMA TA BIYU HAUSA NOVEL

Faiz na fitowa daga bathroom yaga haske Kan face din wayarshi, ahankali ya Isa wajen wayar sai yaga babanshi ne kiranshi, irin faduwar gaban dayaji inda weak heart gareshi ya isa ya samu heart attack don wani irin faduwar gaban yaji lokaci guda, Saida ya dafa chest dinshi for some seconds ya lumshe idanuwa before ya bude idanuwanshi, ajiyan zuciya ya saki before yace
“Allah yasa Bai sani ba… help me Allah…”ya fada Yana daukan wayar a hannunshi Yana nufan kofar fita, bakinshi ya bude yayi breathing out yayi smelling breath dinshi yaji it’s Normal sanann ya fita, tunda aka kawo Mashi file din suke ta wasan boyo da alhaji, Bai yarda su hadu don Kar yayi mashi maganar, kou bangaren Bai zuwa gaidashi, tamkar he is going to the lion’s den Haka yakeji, Bai tsoron kowa Amma Yana tsoron fadan mahaifin shi,. Sai tafiya kaman yake sabye da kayan baccin dake jikinshi, Yana zuwa kofar bangaren alhaji saida ya tsaya yayi adua sanann ya Shiga da sallama, falon babu kowa, tsayawa yayi sake sallama gabanshi sai faduwa kawai yake, he just pray ba maganar lost dinsu zai fada mashi ba, jin shurun yayi yawa yasa ya nufi kofar daya San
It’s his bedroom, Yana zuwa ya tarda kofar bude Yana jin kukan mom Dinshi kasa kasa, da sauri ya karasa bakin kofar yaga mamanshi zaune bakin gadon alhaji yayinda shi Kuma Yana zaune saman gadon, daga Kai alhaji yayi ya watsa mashi wani irin kallo,
“Assalamualaikum…” FaiZ ya fada kanshi kasa, amsawa alhaji yayi kaman Bai son yayi magana yayinda yana kauda kanshi gefe alaman kou kallonshi Bai son Yi, ita Kuma ta daga kai ta kalleshi ta cigaba da hawaye abunta, kaman Mara bones a jiki ya taking steps kaman uku zuwa dakin wondering why his mom is crying like this da sanyin safiyar Nan, gefe daya ya tsaya yace
“Daddy….ka…kirani…Ina.. bathroom…” Ya fada kanshi kasa.
“Am going to ask you a very straight forward question and how you reply zaiyi determining next action Dina….kake Kai min kudin company…”alhaji ya tambayeshi Kai tsaye, faiz sake dafa chest yayi cikin tashin hankali as he knows shikenan babanshi ya San what happened, yanda ya dafa kirji ta kasa magana alhaji ya kalla before ya tabe Baki yace
“Ai dole kq kasa magna….look at how stupid and useless you’re…. you can’t even defend yourself…duk manager knows how to make a statement when ever something like this happened Amma ka kalli kanka….wato ka maida kudin company Dina kudin holewa da bushasha kou…” Wnanan maganar da yake yasa faiz Fara hawaye as kou kadan ya rasa abinda zai fada mashi iyaka yayi Shuru, it really hurts him, in an zageshi Kan something that he knows it won’t hurt like this,
“You’re such a huge disgrace to your kind….Ina da abokai da dama wayanda yaransu at 20s suke Fara yin aiki a company din mahafiinsu suna fiddo Excellent results…am gaka…34 going to 35…common company you can’t manage…” Alhaji ya sake fada mashi sounding very better yayinda shi Kuma Yana tsaye inda yake sai wasu irin very hurt tears ke zubo mashi, baka taba sanin he is crying don no single sign, saidai mamanshi dake kuka sabida bakin ciki, duk uwa will cry if the father of the child is talking like this,
“If you know ka ajiye min kudi a account Dinka wallahi return my money… there’s no way da ban ci riba ba Kuma in Fadi Haka…in my 40 years of business ban taba witnessing such nonsense ba… bring back my money kou Kuma I handle you in a way you never expects….I will treat you the way I treat any thief in my company…”
“Am…not…a thief….I didn’t…take… anything…” Faiz ya fada cikin shesheska, kallonshi mamanshi wondering Wai fazi me ke kuka kou waye, shima alhaji kallonshi yayi Amma kou kadan Bai ji tausayinshi kou kadan ba,
“Kayi kukan jini if you like….but give me back my money…kasan millions nawa na zuba a wajen… you knew it…and Bai taba yuwa in barka anyhow….kawai ka maidomin kudina…If you like go anywhere ban da matsala…kawai maidomin kudina… period…” Alhaji ya fadawa crying fajz
“Wallahi ni ban San what.. happened ba…. wallahi daddy believe me ban taba kudin company ba….ban amsar koy sisi a cash…Kuma ka Tambayi mr bamaiyi if na taba fada mashi kou kobo ya turamin ta account…. wallahi daddy ban taba kudin company ba…. salary da allowance diba kawai nake amsa…” Ya fada mashi cikin hawaye, tsoki alhaji yaja before yace
“Oh wnanan it’s your problem…ai tunda you’re the head kou me ya faru it’s on you….kayi tunanin Ana Zama shugaba saboda warming chairs?…when you’re a leader any thing comes to your and from you…so ba ruwana da wani baka amsar komai or whatever… it’s entirely your business…ai you’re the Head…Bai yuwa sabida your mismanagement a lalata min company…” Alhaji ya fada mashi cikin fushi, sadda Kai kasa faiz dake hawaye yayi before yace
“Nidai…tunda ban iya management ba…kawai….na bar aikin…” Bai karasa ba alhaji yace
“Ai daman I know it’s your plan…nasan abinda kayi planning kenan…wato you embezzled my money sai daga Baya ka bar wajen…tou in har it’s your plan you fail woefully… wallahi ka Fadi kasa… listen and listen attentively…kou koranka bazanyi ba… wallahi na baka shekara guda. .to get back my company on it’s feet….in yaso you’re Free to leave…Amma wallahi baka Isa ka kwace min kudi kace zaka bar aikin ba…” Mahaifin shi ya fada sounding very serious than ever, faiz kallon mamanshi data ji sanyi saboda second chance da aka bashi yayi yace
“Mummy…ki…saka…Baki a wanann alamari…Dan..Allah tell him..ya amshe company dinshi…” Aikam Bai karasa ba mamanshi ta Mike tayi mashi wani irin wawan Mari, zai bude maki yayi magana ta Kara mashi another one,
“Just keep Shut Dan uwarka…. wallahi aikin Nan kou kaki kou ka so sai kayi shi…and wallahi you do it well kou kuma fita daga cikin yarana….Bai yuwa ka dinga jamin tozarta.. it’s never happening… never…” Ta fada jikinta na rawa, faiz data dafa both cheek dinshi zaro idanuwa yayi not knowing what to say, he is so surprised by her statement, wato because of aikin da Bai yiwa shi wants to disown him,
“Haba…iyami… it’s unfortunate…” Hannu ta sake dagawa zata bugeshi alhaji yace
“Enough… enough…” Ya fada Mata Kai tsaye,
“Wallahi alhaji i meant anything I said….in har wannan Yaron bazai maida hankali yayi aiki yanda ya kamata ba wallahi billahi saidai ya nemi wata year…. before ya kunyata ni cikin family da ake ganin ban chanchanci what I get ba it’s better ya fita daga rayuwata… wallahi I mean..it.. ” ta fada tana barin dakin cikin zafin mama, now faiz knows she’s so fucking serious, bai taba ganinta Haka ba tunda yake, he knows she’s a very hot tempered person Amma Bai San it’s up to this extend ba, kallon babanshi yayi alhaji ya watsa mashi harara Yana cewa
“Shame on you sakare….kaji haushi wallahi…ai na fada maka…if you think Zan barka ka cinye min kudi ka bar company kayi karya…sai kayi working ass dinka ka maida Mani company on it’s leg sai ka tafi duj inda kakeso…and ka sani am not adding dime to what it’s in that account…shi saka juya har sai ka samu kudina yanda yake….Kuma ja sani wallahi kudin siblings dinka na wannan shekaran it’s on you….now get out…kafin inci ubanka…” Mahaifin shi ya fada a harzuke.