DAMA TA BIYU HAUSA NOVEL

A bangaren su Amira da faiz baccin da Basuyi cikin dare ba Suka Rama har karfe 11:30, Amira da Bata Saba irin baccin rana bace ta fara farkawa, she wakes up feeling so empty as she can’t remember the last time she eat, hamma tayi tana kallon face din fajz dake bacci, she stares at him looking at his handsome face, tana zaune tana kallon shi ya bude idanuwa ya zuba Mata,
“I feel your beautiful eyes on me…” Ya fada ahankali Yana matsawa kusa daita, murmushi kawai ta saki, Kanshi ya Dora Kan kafarta Yana kallon agogon dake dakin,
“Oh my goodness…har 11:30 tayi?…” Ya fada Yana mikewa zaune, tunawa yayi da Sam Basu gaisa da Bintu ba dazun, Bai sake wasting of time ba ya sauka daga Kan gadon, bathroom ya Shiga after few minutes ya fito,
“Zanje wajen sister ki…duk yau bamu hadu ba…” Ya fada Yana gyara gaban wandonshi, har ya juya sai Kuma yace
“Or better still tashi ki shirya muje ku gaisa… kece karama…” Ya fada with a smile Yana kallon ta, babu musu Amira ta Mike ta Shiga bathroom itama, Bayan Yan mintuna itama ta fito, she’s feeling somehow, kayan dake Jikinta basu da matsalar komai so all she need was carry hijab data Yi sallah dashi ta saka, simple shoes Wanda it’s nothing less than 20k ta saka hannunta faiz ya kama suka fita, ahankali suke tafiya, they look so good together, kawai kana kallon su zaka Gane they’re meant for each other, falon bintu na farko suka Shiga, the scent dake tashi ba kadan bane ba, Amira da kanta ke kasa Dan Satan kallon falon tayi,
“Pls I want you to feel free around her…. she’s now your sister… kinji kou…” Ya fada Mata, ahankali ta daga mashi Kai, Yana shjga second falo Bintu dake zaune tana tunanin tunda sukayi aure Bai taba dadewa Haka Bai fita ba, yanzun he has gotten what he wants, Tana zaune tana sake sake ya shigo, ahankali ta daga Kai ta kalleshi, da sauri ya ware Mata free hand dinshi Yana cewa
“My baby…” Ya fada with a smile, itama Bintu Dan murmushi ta saki tana zaune tana kallon shi without standing dukda already she knows what he means,
“Come on…” Ya fada Yana Mata hannu ta zo, Amira dai kanta kasa fave Dinta dauke da murmushi cikin ranta kuma tana
“Munafukin… wannan mutumin mugun munafuki ne…” Ta fada, ahankali bintu ta Mike kaman Bata so ta taka cikin kasaita ta isa gareshi, hugging dinta yayi da hannu daya tare dayi Mata kiss a goshi Yana cewa
“How was your night?…”
“Alhamdullilahi…” Ta amsa mashi calmly, ahankali bintu ta daga kanta ta kalli Amira da Kanta ke kasa,
“Sister Ina…” Bata karasa ba Amira tayi Saurin cewa
“Ina kwana…” Ta fada kanta kasa
“Lafiya Lau amarsu ta ango…” Bintu ta Fada with a smile, itama Amira murmushi kawai tayi, Dan dukan bombom din faiz bintu tayi tace
“Ango kasha kamshi…'” ta fada tana kashe mashi Ido daya, hancinta ya rike Yana Mata alaman da ido na nothing happens, falon Suka Shiga zasu zauna fajz yace
“Dayake yanzun baa Sona shine aka dafa abinci aka cinye… scent everywhere…” Ya fada cikin shagwaba hannunshi cikin na Amira sai Kuma dayan hannunshi Kan waist din bintu, Dariya bintu tayi tace
“Kalli Chan.. ” ta fada mashj tana nuna mashi dining,
“I can’t eat ai tunda ku baku ci ba…” Inji Bintu,
Oh my goodness…Mrs faiz kalli Abun arzikin da sister dinki tayi…she made us breakfast…” Ya Fadawa Amira dake sauraron conversation dinsu, daga Kai Amira tayi ta saki murmushi tace
“Wow…” Ta fada tana kallon dining din dake dauke da very expensive casserole,
“Thank you…” Amira tayi adding, kiss faiz ya sakeyi Mata a goshi Yana cewa.
“You’re the best wify… ” Ya fadawa bintu, sakin bintu yayi ya rike Amira har zuwa dining ya ja Mata kujera ta zauna itama Bintu ta karaso ya ja Mata kujera ta zauna sanna shima ya zauna, he didn’t Wait to be served ya fara serving kanshi, Amira mikewa tayi zata zuba masu abinci Bintu tace
“Amarsu ki barshi let me do it.. ” ta fada Tana kokarin mikewa,
“No pls…Bari inyi… you have done it all…” Inji Amira, fajz Kam feels today is the happiest day of his life, Bai taba tsintar kanshi cikin farin ciki irin wnanan ba, it’s like having all you ever wanted, Amira serving din bintu tayi shi Kuma faiz Yana cin abinci Yana Santi, itama Amira tana Fara ci tasan daman abincin bintu ba daga baya ba, she feels she can’t compete with her at all, su biyu suna tunanin abubuwa kala kala, kowacce tana tunanin Yar uwarta ta fita,
“Alhamdullilahi…” Fajz ya furta under his breath cikin happiness, Yana cin abincin Yana kallon Amira then ya kalli bintu, Amira Bata wani ci sosai ba, Bata sake da zata saki ciki taci abincin ba dukda she’s so hungry, inda shi kadai ne data ci sosai ba don komai ba sai don sun Saba da junansu, kanta kasa Amma she feels he is staring at her, fajz ne ya Gama breakfast because he eat fast na she enjoyed every spoon he took, wajen dispenser yaje Debi ruwan zafi ya zuba cikin na sanyi ya kashe Sanyi Sannan ya koma falo rike da cup din Yana Shan ruwan, Zama yayi Yana tunanin what to tell them mom dinshi ta fada mashi he have to seat them down ya fada masu irin gidan da yake so, he waits for them to finish as he thinks of what to tell them and how to say it, Zama gaban Mata kayi magana is somehow, he have never done it before, gashi ya Zama mijin tsala tsalan Mata biyu, he just pray Allah yasa Kar ya Zama sanadiyar bakin cikin wata daga cikinsu, he wants to make both of them happy dukda hankalin shi yafi karkata ga mutum daya and you all know who that is, he feels he will rather die than hurt bintu, she’s his sister, almost same blood run through their vein, sannan she’s his wife, the mother of his first child, sannan a very patient and unique lady, yasan not everyone zai iya abinda take, she’s really trying, he will try all his best Kar son Amira ya rufe mashi ido har ya kaiga Yi Mata ba daidai ba, zai dage a tsakanin su that both will feel very loved, Yana zaune waiting su Gama, Amira ce ta Fara Mikewa ta dauki plate dinta Dana faiz ta tattare wajen ta Kai kitchen, tana fitowa taga itama Bintu ta Mike tana kokarin kwashe plates dinta Amira ta fito tana zuwa ta Kama na hannunta tana cewa.
“Bari in ajiyesu…” Ta fada Mata, murmushi bintu ta saki hannunta Daya dafe da cikinta tace
“Da kin barsu amarsu… you shouldn’t be doing this…” Ta fada mata, murmushi kawai Amira ta saki Amma hakan Bai hanata amsar plates din ba, kitchen ta koma ita Kuma bintu ta sauko falo faiz ya mika Mata hannu, wajen taje ta Kama hannunshi tana Zama gefen shi, cikin zolaya ta Kai Bakinta kusa da kunnen faiz tace
“Amma gaskiya Yaya amaryarka ta Hadu…I have been watching how she walks… it’s Normal… she’s so strong…” Ta fada, Amira data fito daga kitchen tana tsaye wajen dining but she can see them, they look so cute together, she just feel why will he bring her into this home, kallon bintu faiz yayi, itama ta zuba mashi Idanuwa sai ta kashe mashi Ido daya, Bata ankara ba ya rike Mata kunne Yana cewa
“You don spoil finish…see dirty mind ooo…” Ya fada Yana murde kunnenta yayinda dayan hannunshi na zagaye da wuyanta ya turata cikin armpit dinshi, Kara bintu ta Fara saki tana dariya, Amira na tsaye tana tunanin Anya zata iya Zama tsakanin Wannan mutanen kuwa, Idanuwa faiz ya daga ya ganta tsaye, murmushi ya sakar Mata Yana cewa
“Baby…talk to your sister ta fita idona if not I will remove her ears…” Ya fada still Yana rike da kunne bintu dake Kara, murmushin karfin hali amirata saki before ta sauko tana cewa
‘”pls sorry…” Ta fada on behalf of bintu data dage da ihu tana dariya,
“Ai tunda kince sorry I will leave her…but kija Mata kunne…” Faiz ya fada Yana sakin kunne bintu yayinda har lokacin Yana rike da shoulder dinta, free hand dinshi ya mikawa Amira ta zo ta zauna Bata rike hannunshi ba, hannunshi ya Dora Kan shoulder dinta ta Dan janye daga gareshi
“Ke zo Nan…” Ya fada Mata Yana jawota jikinshi, Amira dai she feels she doesn’t fit in, gani take sun fi dacewa da bintu, gyaran murya faiz da hannunshi biyu ke Kan kowacce yayi yana massaging shoulder din Amira Ya Fara Adua sai da ya Kai karshe bintu ta amsa da Amin sannan itama Amira ta amsa da Amin cikin voice din da Sam Bai fita, hannunshi ya maida waist din Amira ya rike Yana shafawa before ya Fara cewa
” Yau Ina matukar farin ciki da Allah ya bani the most beautiful ladies a matsayin matana….yau Ina cikin farin ciki Mara misaltuwa… sannan ina son ku dawwamar dani cikin wannan farin cikin by zaman lafiya….kou kadan ban son hayaniya….ban son fada kou anything annoying…ni na auri both of you Kuma Ina kaunar ku both…ban son kishi…ni bance kowacce tayi kishi kaina ba har ya kaiga hauka kou misbehaving…duk Wacce tayi Mani kan Kara sai nayi mashi na rodi….I want pure zaman lafiya… both of you are age mate…and you share same name…so ku zaka sisters din junanku…. never the less…Amira…” Ya fada Yana kallon Amira da kanta ke kasa tana jin hannunshi har bone din kugunta, Kai ta daga kalleshi
“Kinga Bintu itace uwargida.. she’s now your elder sister…Dole ki Bata girmanta…. respect her….banson Harkan raini…” Ya fada Mata in his real voice ba wani muryar so da kauna, it’s like sanda suke office,
“Kin Gane?…” Ya tambayeta Kai tsaye, ahankali Amira ta daga mashi Kai tare dacewa
“Eh…” Ta fada sounding so calm
“Bintu ke Kuma ki rike girman ki…kinsan duk yanda mutum yake babban a waje in har Baki rike girman ki ba it’s of no use…don Haka respect yourself…kijata a jiki…ni banson kuyi zaman kishiyoyi…na tashi Naga ubana da Mata biyu Amma ban taba jin wata tiny talks tsakanin su tunda suke ba…don Haka kowacce tayi Shirin zaman lafiya…kou sau Daya ban son inga ba daidai ba a tsakanin ku…. you all know I have two sides…now Ina Fatan Allah ya bamu Zama lafiya….ya Kuma Baku Ikon zaman lafiya da junanku…” Ya karasa maganar sounding so at peace at last
“Amin…” Bintu da Amira Suka amsa, kaman daga sama sukaga faiz tsaye tsakiyar dakin Yana cewa
“Sai ni mijin Fatimas….” Ya fada Yana daka tsalle as he normally does when ever he is over excited, rawa ta farayi Yana
“I feel good…”,bintu sai Dariya take yayinda ita Kuma Amira ta sadda Kai kasa ta Dan dafe goshinta tana Dariya.