DAMA TA BIYU HAUSA NOVEL

Faiz Kuma Sha yayi ta baje bayab sallah ishai, wace gari Vai tashi ba sau wajsn karfe 11, kafin ya shirya ya tafi office Sai wajen karfe 12,
“Wato dai an zuba min Ido kenan…” Ya fada yana fita zuwa cikin Motar shi da sauri kaman wani mahaukaci, yasan inda sanda mum dinshi ta damu dashi ne da tuni zata Shiga ta tadashi, Amma yanzun Kam vabu Wanda ya damu dashi, hakan Kuma Sam Bai mashi dadi, for someone to show they care about you is something really huge. Haka ya tafi office Yana zuwa Saida ta tambaya kou babanshi yazo akace Bai zo ba
“Shima ya zuba min Ido yaga iya gudun ruwana kenan…I pray he isn’t planning how to deal with me..” yafada Yana Shiga office dinshi
Amira Kam tana tashi da asuba tayi sallah ta Mike ta fita don ta gaida mum dinta, it has been long since she greeted her ba don komai ba sai don she have warned her Kan cewa duk ranar da tayi Mata magana sai ta sumar daita, hakan yasa ta hakura da Shiga inda take ta gaidata Amma tunda tayi Mata magana jiya she feels maybe if taje ta gaidata she will answer her, it’s the part of her happiness that her mother talked to her without beating or shouting, she is so happy, tana takawa zuwa kofar dakin mum dinta tana fargaban Kar ta sauya raayinta, cikin dakewa ta bude kofar ta ganta zaune Kan praying mat, juyawa hajiya dake azkar tayi ta kalli Amira, da sauri Amira ta durkusa ta gaidata, Kai hajiya ta daga Mata tare da daga Mata,, Zama Amira tayi gefe hajiya ta nuna Mata hanyar ta fita, Babu musu Amira ta Mike ta bar dakin, it’s far more better than before, she’s so happy for the new change and it’s all because of Ahmed, Sam Bata San ya zata dingayi mashi biyayya to show she really appreciate what he is doing in her right now ba. Komawa ciki tayi ta kunna datar ta ta duba if there’s any conversation kan WhatsApp kou anything dake neman attention dinta, wayanda sukayi Mata magana tayi replying ta ajiye wayarta ta kwanta bacci.
Ahmed Kam sauran kadan daya makara Amma he rushed don kou breakfast baiyi ba ya tafi office, yana aiki ya Kira Amira Bata dauka ba, lokacin lunch yau Bai tsaya koina ba sai wani school dake about 20 miles away from organization dinsu yaje ya tambaya If suna amsar Yan Yara kanana da Kuma kudinsu sai yaji kudin kusan 80k, yasna his salary is huge Amma the school fees and registration of above him sai ya bar school din ya koma office, Yana Kan hanya sukayi da Amira inda ta fada mashi Batayi bacci ba kou kadan shi yasa tayi bacci da yawa har da Rana. Bai fada Mata komai game da school din dayaje ba, Bayan ya tashi daga office ya wuce wata mall dake cikin gari, jallabiya ya sayawa Amira guda biyar akalla he spent kusan 80k a jallabiya din kadai dukda ba masu tsada sosai ta saya Mata ba don da akwai Yan 50k each, ya samo Mata wayanda zata dinga managing kafin ta samu kudin sayan wasu, right now ya maida kanshi tamkar shi kadai gareta dukda he knows komai Ana iyayi Mata If iyayen sun so Haka Amma he is giving her most of his time and money right. It’s what he wants to do and he is doing it, yasan inda Yana da millions a account Dinshi yanzun da har Mota zai Saya ta danka Mata yanda duk ranar daya makara Bai zo daukan ta ba ta dinga Hawa Tana zuwa wajen aiki Amma yanzun Bai da kudi sosai Kuma dad dinsu ba Mai bawa Yara kudi anyhow bane sai if kace zakayi business kuka sai ka kawo business plan dinka Amma Haka Nan Bai taba baka kudi anyhow but he will make sure bakayi lacking komai ba Balle kayi kwadayi waje. Bayan ya nufo gidansu Amira ya lura da another school dake kusa da gidansu Amira, school din is like 15 miles away daga gidansu Amira, yaga a signboard dinsu yaga da akwai play class da kindergarten, parking yayi ya tsaya ya Gama karewa school din kallo yace
“Allah yasa you’re affordable…”ya fada Yana kallon how neat the school is, ahankali ya nufi school din, it’s past 5 Amma the school adminstration are still around, office dake bude ya nufa sai Kuma ya lura da akwai inda da akwai Yara da Kuma wasu Mata guda hudu looking at yaran da masu wuce six ba, sai some classes are still open ana karatun alquran,
“Oh Allah this should be affordable…”ya fada Yana heading to the office, it seem har islamiya ake a school din, office din ya Shiga da sallama aka amsa mashi suka gaisa da Wanda ke cikin office din who seem the director na school din, Nan Ahmed ya tambayeshi Kan school din Nan mutumin yayi mashi bayanin school din and it’s exactly what Ahmed is looking for in school, .
“nawa…” Ahmed ya tambayeshi Bayan ta Gama mashi duk bayaninsu
“For first timers it’s 46k Amma daga baya the school fees is 30k and the form is 2k…” Idanuwa Ahmed ya lumshe as it’s ok to him, Nan yayi requesting a bashi form aka bashi form da Kuma teller na bank da zai biya kudin school din. Mikewa yayi tare da mashi godiya. Daga Nan Bai tsaya koina ba sai gidan su Amira in da ya fito da Leda hannunshi, bangaren babansu Amira ya ajiye ledar shi kofar part dinshi ya Shiga ciki da sallama, Nan alhaji ya amsa mashi with a smile, durkusawa Ahmed yayi ya godewa alhaji for the trust, shima alhaji gode mashi yayi for still standing by amira despite what happened. He spent few minutes a Chan inda alhaji yace ya zo ya zauna yaci ya zauna yaci abinci ya koshi sanna ya fita zuwa bangaren hajiyarsu Amira, Nan ya wuce bangaren Amira yayi knocking sai yaga her door is not closed today unlike before da always her door is closed.
“The door is open …” Ta fada Tana kallon kofar don ganinw Wanda zai Shigo, Yana bude kofar tayi Saurin mikewa with a very lovely smile Kan face dinta,
“Yaya… welcome…” Ta fada Tana tsaye tana kalloj huge lader dake hannunshi, .
“Yauwa sis…how was your day…” Yafada Mata Yana shigowa tare da Kallon yanda take washe Baki, .
“Splendid…” Tafada tana kallonshi, ledar ya Mika Mata ta amsa Tana ajiewa tare dacewa
“Bari in dauko maka ruwa da abinci before you requested for it…” Ta fada tana kokarin fita da sauri yace
“Come back here ni na koshi…daddy ya bani abinci naci koshi…so nagode…” Ya fada Mata.
“Yanzun kou ruwa baka Sha?..” ta fada mashi
“Shima ya bani na Sha…”ya fada Mata Baki ta tale , tana cewa.
“Da gangan ka ci abinci wajsn daddy don kace na hanaka…ai ka kyauta…” Ta fada cikin shagwaba, kura Mata ido yayi Yana kallon yanda ta wani marairace mashi, murmushi ya saki yace
‘yanzun dai hope you’re not angry…”
“I am…” Ta fada kaman zatayi kuka
“Ok ai da kiyi fushi Dani gwanda ciki ya kumbura da abinci ya fashe don Haka je ki kawo inci…” Ya fada mata Yana kallon ta
“Aa…ni banson cikin yayana ya fashe…kawai shikenan…” Ta fada mashi
“Aa dauko kou spoon daya ne inyi…banson kiyi fushi Dani…”
“Yaya ban fushi da Kai… seriously…”
“Aa nidai kawo kou spoon dayane inci…hurry…” Ya fada Mata atakaice,babu musu ta Kama hanyar waje ya bi bayanta da kallo, Nasir dake zaune ya kalla ya kura mashi Ido for moment yace
“Kai baka sanin mutane sai mahaifiyar ka kou…ko oyoyo baka iya yiwa mutum…”ya fada mashi, yaron sai kallon shi kawai yake without saying a word
“Taso…”ya fada mashi Yana mika mashi hannu, kafe shi da idanuwa Nasir yayi shima Ahmed ya kafe mashi nashi idanuwa ya kura mashi Ido Yana kallon face Dinshi, shidai Yana mugun ganin resemblance din Nasir da Habib, asalima yafi ganin kamannin yaron Nan da Habib kan yanda yake kama da amira, kallo daya zakayi mashi kace he is like his mother Amma in zaka kafa shi da idanuwa zaka gan he is so much like Habib, deep down sai ya dinga tunanin yanda Habib is a chronic Casanova anya Haka Nan ta bar Amira kuwa, don duk cikinsu da suka fita waje karatu sunsan halin Habib, Yana Nan kasar baa San aihanin halin shi ba sai da suka bar kasar inda Basu da masu Yi masu fada kou Mai saka masu Ido halinshi na gaske ya fito. Shigowan Amira yasa ya dauke Ido daga Kan Nasir ya kalleta ya saki murmushi, abincin ta kawo Mashi yaci kaman spoon biyar yasha ruwa yace
“Ki duba kayan Nan in sunyi…” Ya fada Mata, sai lokacin ta tuna data shigo da ledar, da sauri ta sauka zuwa wajen ledan ta Fara budewa taga jallabiya kala kala cikin ledansu, Idanuwa ta zaro ta kalleshi, Ido daya ta kashe Mata tayi Saurin sauke idanuwanta zuwa Kan Kayan, da sauri ta dauki blue one with lots of glittering stones ta Mike tana cireshi daga cikin Leda tare dacewa
“Wow Yaya…Haka mukayi da Kai…”ta fada cikin so much excitement, murmushi kawai ya saki Yana kallon ta,
“Yaya they’re so beautiful…Yaya how can I thank you for these whole joy you’re bringing to my life…”ta fada tana ajiye daya Kan gado ta Kara dauko another one, each one she carries is more beautiful than the last one, abun ya Bata mamaki, excitement is all over and she wonder why this guy is so kind to her Haka,ta Gama fiddo kayan sai ya Mike Mata form din Nasir tare dacewa
“Gashi kiyi filling form din school…” Bai karasa ba kawai yaji wani irin tight hug kaman daga sama.