DAMA TA BIYU HAUSA NOVEL

Kaman kullum yau ma karfe hudu da Yan Kai Ahmed yazo ya dauketa, before Ahmed yazo har faiz ya bar office din, he asked her what is the file for and she replied with
“Yace inyi accounting dinsu….”
“Toufa…hope he knows you’re just his secretary and not his PA kou accountant…” Ahmed ya fada Yana kallon uban girma files din
“Yaya…ba komai…I need it…I need something to stop me from thinking…so ba matsala…duk aikin da zai bani I won’t complain…I will do it…” Ta amsa mashi tana Shiga Mota, Bai sake cewa komai ba Saida suka hau hanyar kalli yanda tayi relaxing tare da lumshe idanuwa yace
“Dazun hajiyar su faiz ta kirani…Wai In kawoki…” Da sauri Amira tabude Idanuwa tare dacewa
“Ni Kuma?..why Yaya… lafiya?..” ta fada cikin total confusion as it’s unexpected to her
“Gaskiya Babu matsala…kawai tunda kike hospital taso zuwa ganinki…sai Kuma Allah Bai yarda ba…so now she wants to see you… maybe she have some words of wisdom for you…” Ya fada Mata Yana tuki,
“Toufa Yaya…” Ya amsa mashi
“Kou dai baki son zuwa…sai in fada Mata kinki zuwa…don ni Allah na gani I can’t tell her bazan kawoki ba…”
“Yaya ba Wai ban zuwa ba ..kawai umya San fadawa su mummy…kasan I ba fita nake ba sai wajen aiki…kana ganin zasu yarda in fita?..” ta fada kanta kasa.
“I don’t think they will deny you anything…kawai tell them Kuna da meeting with board members a company dinku… that’s all…” ya fada Mata.
“Ok… shikenan…” Ta amsa mashi, suna da Hira ya kawota gida, yau Basu tsaya daukan Nasir ba as mum dinta have made it clear zata sa a dinga Kai shi Ana maidoshi, so gida ya kawota ya direta yayi Mata sallama Kan zai kirata anjuma. Tana shjga gida ta fara wucewa bangaren dad dinta, he looks so happy to see her like irin ya Dade Bai ganta ba,he asked her ya office da Kuma komai, she replied with komai lafiya Lau, Nan ta samu Daman fada mash suna da board meeting ranar Saturday Kuma Bai Bata lokaci ba ya amince mata, tambayarta yayi file din hannunta na meye ta amsa mashi da it’s office work. Part din mum dinta ta shiga ta wuce directly zuwa dakin mamanta, hajiya na ganinta ta fara
“oyoyo oyoyo…” Tafadawa Amira, nazifa da asiya gaidata sukayi ta amsa cikin sanyimurya Tana Zama, .
“Kije kiyi wanka kici abinci sai ki gwada kqyan dake dakinki…in da akwia waynda ke da matsala let me know sai a maidawa tailor…” Hajiya ta fada mata, ahankali Amira ta Mike Babu single excitement dake tattare daita ta shiga dakinta, Kaya ta gani Kan gadonta masu uban yawa, duk a dinke Kuma sunsha guga, ahankali ta Ajiye file din hannunta Tana cewa
“I wish this will take my pains away. .” tafada tana Shiga bathroom, wanka tayi ta fito da ablution. Kaya ta saka ta Yi sallah sannan ta dawo Kan kayan tana gwadasu, she knows the tailor, wata it’s zee dee mon don sune kayansu ke Zama very beautiful and elegant kou da kuwa baa saka kayan dinki ba, kayan sun danyu Mata Kaya Amma it’s ok, she knows they use her old measurements, ta fi da ragewa sosai especially these few days, these days that have been the worst days of her life. Laces guda hudu, atampopi shida sai Kuma materials kala biyar. Sannan da akwai Vail kala 7 Wanda kusan duk kayan da akwai Wanda zai Shiga dasu, duk abubuwan Nan da akayi Mata Bai sakata wani farin ciki ba,. She just wish zata iya fada masu they should stop trying to make it up to her don they’re not the cause of her sadness, duk abinda zaayi yanzun Bai burgeta and nothing makes her sad like what Habib did to her. Fita tayi ta Shiga dakin mum dinta tayi Mata godiya
“Dear Baki son kayan ne…sai a Saya Maki wasu…” Hajiya ta fada as she sees no single excitement tattare daita,
“Aa…Ina sonsu mummy…” Amira ta fada tana kanta kasa
“Ok… shoes dinki will be coming tomorrow…” Ta amsa Mata,
“Nagode mummy ..”
“Toufa… stop saying that… you’re making me feel kaman nawayi stranger Abu…” Hajiya fada Mata sabida how she feels yanda Amira ke yawan godiya Kam duk abinda akayi Mata kaman wata bakuwa ba Yar gida ba,
“Hmmm…mummy…muna da board meeting ranar Saturday…anason dukan mu mu hallara ..” ta fadawa mum dinta
“Ok…allah ya kaimu…and I was hoping to tell you that inason ki dinga zuwa islamiya ranar Saturday da Sundays kafin ki koma school…’
“Yauwa mummy thanks…” Amira ta fada mata.
Faiz na zuwa gida Bai tsaya koina ba sai bangaren shi, wanka yayi yayi sallah ya kwanta, karfe shida ya Shiga bangaren mum dinshi sanye da very light jallabiya Wanda zaka iya ganin short knicker dake jikinshiz Yana zuwa ya wulla kanshi kan kujeran ta
“Abeh am not ready to buy new sofa…” Ta fada mashi Kai tsaye tana kallon yanda ya saki jiki kaman Mara lafiya,
“Hmmm sai in Saya Maki sabo ai…” Ya amsa Mata with his two eyes closed
“What’s wrong with you?..” ta tambayeshi
“Nothing…kawai want to sleep Kuma ga sallah magrub around the corner…” Ya amsa Mata, shuru tayi taba kallon shi Tana inspecting Dinshi,
“Nayi magana da Ahmed fa…yace zai kawota…ranar Saturday like I requested…”
“Wonderful…” Ya fada Kai tsaye before mum dinshi ta Kara wata maganar har yace
“Iyami kin duba kayan Dana tura maki kuwa…”
“Wane Kaya kenan…” Ta tambayeshi tana kallon yanda yake magana kaman he is being forced to talk
“Check your phone ki kunna datanki…”
“Dauko min wayata…” Ta fada mashi, mikewa yayi ya dauki wayar ya kunna datan before ya Mika mataz, Nan Hajiya ta dinga yaba kayan da ta gani Amma one thing is Clear data kawo maganar Amira sai yayi Saurin kaucwa Yana kawo another thing, she sees it clearly, he is not interested in her matter and it’s so obvious, tare suka zabi kayan faiz ya koma bangaren shi ya Yi Mata tagging wayanda suka zaba ya rubuta Mata tayi calculation kudin kayan. A bangaren Amira Kam tana khnna data tagan abinda ya rubuta ta turawa hadiza CEO na pretty collection kayan da suka zaba ta tabbatar Mata da akwai su sannan tayi calculation making Total of kusan 750k ta tura mashi. Wajsn karfe 8:30 Ahmed ya fada Mata ya turo kudin kayan, she gained about 40k gain dinta ,fadawa Ahmed abinda zai Tura account din Mai Kaya tayi ya bar Mata sauran cikin account dintaz
“Ai duk mugun halinka in har zaka dinga irin wnanan shopping din ai naji dadi…” Tafadawa kanta bayab an Gama transaction.
Amira is fun of checking those viewing her status, since her incident Bata Yi posting kaya a status ba sai yau Friday and the thing is boss is Among her first viewers, now she knows he have saved her number. Ranar Friday suna tashi da wuri daga office so suna tashi Ahmed yace zai kaita salon a wanke Mata Kai, bata son Yi mashi gardama but Sam she doesn’t want any disturbance at all, Haka ta bishi ya kaita cikin gari aka wanke Mata gashin kanta, it was looking so silky and beautiful, data kallo Ahmed sai su hada Ido dashi, he waited for her har aka Gama mata, irin kallon da yake Mata is making her feel uncomfortable because in suka hada Ido sai dai ita taji kunya ta dauke Kai Amma kou blinking ba yayi. Kan hanyar su ta dawowa gida yace
‘amira you’re very beautiful…kawai dai I Wish…”ya dada Mata sai yayi Shuru sabida Bai San yayi rushing dinta at all as he knows he have his mother’s heart to win when it comes to her case, Amira kallon shi tayi na second guda ta dauke kanta not minding duk abinda zai fada Mata as it’s gets her angry, she will prefer Kar yayi Mata maganar so kou relationship if not she might end up not liking him at all don yanzun Bata da enemy a duniya like love, love din Kuma from a man, her wound her not heal Kuma Bata San Ranar da zatayi healing ba, yanda ta daure face yasa kou single magana bai Kara Yi Mata ba ya ajiyeta. Wace gsri which is Saturday yazo gidan wajen karfe 11 na safiya. Amira that is feeling a little bit nervous ta shirya cikin daya daga cikin laces din da aka kawo Mata, she’s not good in daurin Dan kwali so Bata daura ba, kou kwalli Bata shafa ba Balle ayi maganar shafa powder, she’s all natural and beautiful, dakin mom dinta ta Shiga taga Nasir that mum dinta is taking away from her cikin dabara Yana zaune Yana Wasa , these days daya dawo daga school zata sa suyi Mashi wanka ya zauan wajenta, she sees him with new dresses but halin da take ciki Bai barta ta maida hankali kanshi ba, sallama tayiwa mum dinta Nasir na ganinta ya Fara kuka alaman Yana son ya bita, Nan Hajiya ta kirashi ta bashi chocolate yayinda ita Kuma ta fita, kayan jikinta sunyu Mata Kyau sosai as her Vail na tsakiyar kanta, gashin ta sai daukan Ido yake daga nesa, babu earrings kou any jewelry a jikinta, kawai dai gata Nan, she’s going don Kar ace Bata da kunya or don Kar Ahmed yaji Babu Dadi Amma sam Bata son zuwa koina, she feels she’s not going to see boss dinta as she thinks Yana nashi gidan and ba lallai ya fito yau ba tunda it’s week end, he will be with his wife or better still in zai fito kilan kafin yazo sun bar gidan, she have never think so much about him Amma tana tunanin suna da Yara kuwa, is he a father?, Then how will he behaves with his children don wasa ma Bai mashi kyau. Ahmed Kam sai kallonta kawai yake har ta Shiga Mota ta gaidashi ya amsa mata,. Nan ya tada Motar ya ya bar wajen ,