DAMA TA BIYU HAUSA NOVEL

Karfe shida da Yan mintuna faiz ya dawo gida, yaga motocin dad dinshi a parking lot,
“Ya dawo kenan…” Ya fada Yana parking shima, barin brief case dinshi yayi cikin motar ya fito rike da suit dinshi da tie dinshi a hannu, bangaren dad dinshi ya nufa Yana aduar Allah yasa babu wani case a kasa because that old man Never lack reasons to nag, Yana Shiga ya hangi mom dinshi da Kuma Co wife dinta a falo, da sallama ya Shiga duk suka amsa Amma Banda mum dinshi that seem to be angry with him, har kasa ya durkusawa yayi har kasa before ya gaidasu
“You’re welcome son…ya kake…kwana biyu ka manta Dani kou leko ni bakayi…” Hajiya Fatima ta fada mashi with a smile, Zama faiz yayi inda ya durkusa before yace
“Ai mummy ban da lokaci…aiki yayi min yawa…” Ya fada kaman da gaske,
“Kai…karfe nawa kazlje office yau?..” alhaji haruna dake zaune da jallabiya Kan kujera ta alfarma ya tambayeshi Babu Wasa face dinshi,
“Daman I know…” Faiz ya fada under his breath before saying
“Daddy…” Bai karasa ba alhaji yace
“Don’t daddy me….I asked you a question… answer me…” Ya fada Kai tsaye
“Karfe Tara…” Bai karasa ba alhaji yayi amshi dakuwa gami dacewa
“Kaci gjdanku da karfe Tara…. wallahi ka kiyayi bacin Raina… wallahi ka bar ganin ban da manyan Yara maza Kai kadai ne in har ka kaini makura Zan dauko bare in Dora a wanann kujeran Dana baka…kuma I will force you to work under them… it’s not a threat it’s a promise….ka cigaba…” Ya fada atakaice, faiz kumbura yayi kaman zai fashe, kallo daya zakayi mashi kasan he is angry, ya lura da akwai masu fadawa daddy Bai zuwa da wuri, wato Basu sonshi, he will make sure kafin shi yabar wannan office din babu sauran munafuki kou daya a office din. Hajiya Fatima Kam is really happy,. Kawai a amshi company daga hannunshi kou ma was aka bawa Bata da case dashi, ita Kuma hajiya kadijatu shuru tayi tana faman hararan faiz ta kasan Ido cike da takaicin halinshi, she wonders irin wnanan yaron that doesn’t value what he has, tasna many people will be happy to have such huge gigantic position Amma she kou a jikinshi, another annoying thing is family din mijinta will be happy if Bai wnanan position din ba don komai ba sai don ba bahaushiya ta haifeshi ba, har yau some of the illiterate a family din doesn’t love her, wasunsu suna ganin har da asiri take mashi,
“Ai alhaji kayi hakuri yaro ne….one day sai labari…” Inji hajiya fatima kaman gaske
“Ai Baki San wnanan Dan rainin hankali ba…Bai sati Bai Kori mutum ba… kullum cikin kawo new faces yake a company Dina kaman dashi muja Sha wahalan neman arzikin…. wallahi Zaki ubanka… just continue….I will teach you lesson of a life time…”alhaji haruna Ya fada mashi cikin matsanacin bacin Rai, mikewa faiz yayi
“If baka zauna ba na tashi ranka sai yayi mugun baci…” Hajiya kadijatu ta fada cikin bacin Rai, ahankali ya koma ya zauna Amma face dinshi yayi ja sosai don shi a rayuwa he hates a dingayi mashi fada kaman karamin yaro,
“Aa ya tafi…ai na Gama Magana…. leave…” Alhaji ya daka mashi tsawa, mikewa yayi ya bar suit dinshi da tie dinshi Nan kasa ya bar falon,
“Ode!!” Hajiya kadijatu ta fada cikin takaici da Bakin ciki, a rayuwa Babu abinda ke da ban haushi kaman naka ya Zama abun magana a kai kuma.maganar ba na alkhairi ba sai na takaivi da baci, hakan Yana Bata Mata Rai matuka.
“Come back ka kwashe kayanka…” Hajiya kadijatu ta fada mashi da karfi sosai, kaman baiji ba ya bar dakin not even turning back to look at them, a zuciye ya bar dakin ya nufi inda ya bar motar shi, ba abinda yayi sai budewa ya dauki briefcase dinshi ya nufi nashi bangaren sai tafiya kawai yake kaman zai tashi sama, Yana Shiga bangaren shi tun falo ya Fara cire Kayan jikinshi daga shoes Yana direwa Yana tafiya, before ya Isa bedroom ya Gama cire komai nashi daga shi sai socks da Kuma boxer, bathroom ya wuce yayi wanka, gaban fridge da alcohol dinshi suke ya tsaya feeling kaman ya Sha kawai and forget all the anger he is feeling Amma sai ta tuna in har yayi hakan ba lallai ya iya zuwa sallah ba, hakan yasa ya dawo bedroom dinshi daure da towel, kayan jikinshi ya sauya zuwa Jean da Riga wayanda suka amshi skin dinshi ya zauna Kan kujeran dake Nan cikin bedroom dinshi, Nan ya hangi wayarshi dake Kan bedside locker dinshi, mikewa yayi ya dauki wayar ya dawo ya zauna Yana budewa dom ganin wayanda suka kirashi, miscall din bintu ya gani rututu
“Senseless fellow…” Ya fada Yana kallon yanda ta bashi over 30 miscalls, sai wani cousin dinshi daya kirashi and miscall from unregistered number, bintu ya Fara Kira asking her yanda suka Isa gida ta amsa mashi da lafiya Lau, Hira suka Sha for about 5 minutes before ya kashe tare da fada Mata zasuyi Magana later, Kiran cousin dinshi yayi sukayi magana for few minutessai Kuma wanann number da baiyi storing Kan wayarshi ba, ringing ya farayi Yana jiran a daga, Saida ya kusa katsewa aka dauka da sallama, amsawa yayi
“Omo yoruba…” Was abinda aka fada from the other side, faiz cire wayar yayi daga kunnenshi ya kalli wayar ya maida wayar kunne shi thinking of who is calling him don yasan wayanda suke kiranshi da wnanan sunan Basu da yawa and dole Mai kiranshi must knows him well Amma sai dai sam Bai gane Mai magana ba,
“Who is this?..” ya fada calmly,
“Oho… you guest…” Ahmed ya fada mashi from the other side
“Aa..am not good at that…pls waye…” Faiz ya sake fada mashi,
“Hmm wato Kai baka da Nigeria line Dina Amma ni na ajiye naka…ka kyauta ai…” Ya fada kaman Yana fushi dashi,
“Am sorry about that…Ina kokarin daukan murya Amma Sam na kasa….pls waye…” Faiz ya fada
“It’s Ahmed…” Bai Karasa ba faiz yayi Saurin cewa
“Wai you mean Ahmed Abbas?…oh my goodness…when did you return home….yaushe ka dawo…” Yafada cikin ihu da so much excitement, sai abun ya zaka wani iri because it seem ba kullum yake Samun such excitement ba, daga ganinshi kasan da akwai wayanda he feels loose and free around them yayinda wasu Kuma he behaves kaman stranger when with them,
“Yes it’s me…nimq am home…no more kwalelen gani Nan Ina hutawa da su mumcy…nima gani Nan gida…” Ahmed ya fada from the other side of the phone,
“Wow am so excited right now… yaushe ka dawo…” Faiz ya fada cikin farin ciki sosai
“Tun last week na dawo …”
“Oh shine baka nemeni ba ?… ka kyauta ai…” Faiz yafada kaman he is mad at him
“Sorry pls …na huta ne….kou family dinmu ba kowa yasan ba dawo ba…am just at home enjoying myself… enjoy masa and lots of what I missed…” Ya fada mashi
“Ka kyauta… yanzun yaushe zamu Hadu… inshort gani Nan zuwa gida yanzun Nan…Daman am bored…” faiz Ya fada mashi, Dariya Ahmed yayi yace
“Ok Ina jiran ka…sai kazo…hope dai baka manta address dinmu ba…” Ta tambayeshi Yana Dariya
“Otiyawere….orire daru… you’re not serious…” Faiz ya zageshi da yarbanci Yana Dariya, cikin matsanacin Dariya Ahmed yace
“I just can’t wait to see you omo yoruba…I miss you sosai kou don zaginka…”ya fada shima yana dariya Sosai
“Wato zagi kawai yasa kayi missing Dina… gaskiya you’re not a good friend…”
“Am sorry… hearing fake Yoruba in your mouth amuses me…”
“Wai fake Yoruba…da akwai fake Yoruba ne…ai kasan kou ban iya yaren ba Dole in koyi zagi sabida yanda iyami ke hitting Dina hard dasu…” Ya fada cikin serious laughter daya Dade Bai Yi irinshi ba,
“Ai Kai din ne dole Saida atomic bomb yanda baka ji…pls am waiting sai kazo…” Ahmed ya fada cikin matsanacin farin ciki,
“Ok gani Nan zuwa…give Me 40 minutes top…” faiz ya fada Yana Mikewa
“Kace insha Allah…” Inji Ahmed
“Yes ooo… insha Allah…sai nazo…” Ya fada Yana kashe wayar tare da daukan mukkulin motar shi, Daman this house is something else, Bai Bata lokaci ba ya bar gidan. Yana Kan hanya akayi sallah magrub, kou da yazo gidansu Ahmed direct ya wuce cikin, Ahmed was in the compound waiting for him, da sauri Ahmed ya bude mashi kofa ya fito da sauri sukayi hugging junansu cikin so da kaunar juna, da ka gansu kasan suna da kusanci sosai, abokai ne na first class,
“Wai ya Bayan saduwa.. ” inji Ahmed
Bayan sun Shiga ciki sunyi relaxing ta kawowa faiz drink,
“Alhamdullilah…gamu Nan…” Ya fada mashi
“Wai ya magnar auren ka…when are you getting married…” Inji Ahmed
“Soon…Kai fa…why are you still single after too years Dana baroka chan…” Inji faiz
“Haba ni kasan why ai…”inji Ahmed, faiz zaiyi magana sai Kuma Ahmed ya katse shi dacewa
“Well forget about me and tell me about yourself and what you have been doing at home…” Nan faiz ya fada mashi he is heading daya daga cikin company na dad dinshi and Kuma Yana da chewing gum babe that doesn’t let him rest, dariya Ahmed yayi inda shi Kuma yayi interview a wani NGO Yana jiran sakamako, Nan faiz yace
“Ai da kazo company na samo maka something Todo before the results will be out…” Tsoki Ahmed ya buga before yace
“Hauka nake zanzo under you inyi aiki…ai it’s better in dinga amsar na kashewa wajen mamana da inzo ka dinga kwashe min albarka da Yoruba…” Dariya sukayi har da kashewa,
“Am not that bad and ai duk haukata na San aboki…” Ya fada mashi,
“Kar ka damu tun kafin in iso nayi interview a online and Daddy yayi assuring Dina da Zan samu shi yasa ma na dawo….the results will be out tomorrow…” Ahmed ya fada cikin kwanciyar hankali, Haka dai sukayi Hira sosai sukayi sallama.wajsn karfe Tara faiz ya dawo gida, kwanciya yayi reflecting about his life, kawai sai yace
“Wai for instance in nabi umarninsu and make them happy will that be bad?..” ya fadawa kanshi Yana kwance Kan gado ya kashe wayarshi don Kar bintu ta damehsi da Kira as he feels he have talked alot for today, kawai Yana tunanin why not yayi quiting drinking habit dinshi yanda zai iya tashi da wuri yaje office, yasan the most problem da yake dashi da babanshi is coming late to work and he always run late because when he drinks zai Dade Yana bacci,
“Let me try not to drink today…” Ya fada Yana daukan pillow ya Dora Kan cikinshi tare da lumshe idanuwa sallama akayi a Bakin kofar shi and it’s his mom,, Mikewa yayi zaune, Haka takeyi duk sands she have something important to tell him, she normally calls him don suyi magana Amma still sai yayi repeating Same act, inda tasan the kind of battle he is going through don ya daina shaye shaye da ta tausaya mashi, he is facing his own battle privately, babu Wanda yasan why if ya kwanta bai tashi da wuri, kilan if she ask why Yana iya fada Mata sabida yasan Bata taba Tina mashi asiri, yasan kilan she have called his line Bai shiga ba so she have to come herself,
“Iyami…” Ya fada cikin sanyimurya Yana gyara zamanshi, Bata ce komau ba ta zauna gefen gadonshi, in her traditions tasan uba kou uwa suna magana da yaransu cikin dare when everywhere is silent, it is Said that magana na shiga kwalan wanda kake mashi magana, it’s not too late Amma tasan yanzun he is calm, hannunshi dake Kan legs dinshi mamanshi ta Kama ta farayi mashi Tana fada mashi Kar ya Bari taji kunya kou ya kunyarta da family dinsu da sauran su, she pleaded with him Kan he should be a good child yayi aikinshi, she is just begging him today and not commanding him,
“Iyami….Baki gane yanda nake kokarin to be a good boy…kawai sai being a good boy is not easy at all…”
“No you’re not trying at all… “
“Yes mummy am trying….Ina trying Sosai…kawia dai bazaki Gane ba … you don’t know the kind of battle am fighting alone…” Bai karasa ba tace
“Ni ba wani aiki na sakaka ba Balle kace I give you a very difficult task….all I ask of you is to try and wake up early and go to work…” Ta fada mashi,
“Ok iyami…I will try….” Ya fada Mata sounding so real,mikewa tayi tana cewa
“Surprise me tomorrow pls…” Ta fada mashi,Kai ta daga Mata alaman ok Sannan ta fita daga dakin leaving him a hakan, tunani kawai yake, yau Kam dagewa yayi Kan he won’t take it today amma har karfe biyu idonshi biyu ya kasa samun sukuni as he is already addicted to drinking, kaman an mintsineshi ya Mike ta shige bathroom ya dauki kwalban wani vodka guda daya ya kafashi ga Kai, Bai sauke shi ba sai da yaga ya shanye shi tas..Yana Sha ya maida kwalban ya ajiye ya dafe bango yaje ya wulla kanshi Kan gado a birkice sai bacci.