NOVELSUncategorized

BARIKI NA FITO (BOOK 2) 9

BOOK 2
                      PAGE 9
Bariki bata farka ba sai da asuba, jin kiraye kirayen sallah shine yasa ta farka, kuma bata tashi da ciwon kai dinba, tashi tayi ta fad’a toilet, alwala tayi tazo tayi sallah, tare da ro’kan Allah akan ya shiga lamarinta……

 Koda ta idar kasa komawa bacci tayi sai kayanta na sawa data fara sawa cikin karamin akwatinta domin zuwa wajan iyayenta na bariki danta d’an Fara kwana a can, gashi yarima yace ta koma yau dinma.

Bayan ta d’iba kayanta na kwana biyar tasa cikin akwati ta rufe tare da ajiye akwatin a gefe, kwanciya ta koma amma ta kasa bacci domin ba komai take ba sai tunani, a duk lokacin da taso ta fad’ama Yarima gaskiya saita kasa, sai kuka yazo mata in tayi kokarin ta daure ta fad’a mishi saiya kashe mata Giwa da fad’in bazai auri mazinaciya ba…   Wani hawaye ne ya zubo mata Mai zafi, Tana son Yarima bata son rasa shi, lallai Indai tana son samun Yarima a matsayin miji shine ta boye mishi labarinta har abada…..  Da sauri ta girgiza kai tare da fad’in labari na bazai taba boyuwa ba domin komin daran dad’ewa sai gaskiya ya fito, lallai fad’ama Yarima gaskiya shine mafita amma sai bayan na aureshi, zanyi kokarin in fad’a mishi gaskiya ranan daya aureni Nasan May be yayi min uzuri, tunda ba haka nake ba, kaddara ce ta fad’amin wanda nida kaina bazan iya cewa ga abunda ya faru ba, koda za’a samun wuka a wuya ban San yanda Abun ya faru ba……
***
Haulat ce take jan akwatinta daka gani tafiya za tayi….
Hjy habiba tana bayanta tana fad’in yanzu sai yaushe kuma?
Haulat tace mum sai dai munyi waya, kawai
Farhan ne ya fito tare da fad’in muje in kaiki train station…..
Hjy habiba tace farhan ka Bari driver ya kaita mana,
Yace no mum Bari in sauketa
Babu yanda hjy habiba ta iya, dole farhan da haulat suka fita.
Haulat na gaba farhan na mazaunin driver, ta kalli farhan tace plz mu biya ta gidan Hjy Umaima zan amsa sa’ko…….
Farhan yace ok, amma zaki missing train din 8, sai na 10 zaki hau,
Tace babu damuwa
Juya motar yayi sukai gidan Hjy Umaima, haulat ce kad’ai ta shiga…..  Ta d’an jima Sosai ban San mai suka tattauna ba sai gata ta fito ta shiga motar ta kalli farhan tana y’ar murmushi wanda shima din ita yake kallo tace muje…..
Mai yakon suje din saiya kama hannun Haulat yana fad’in haulat dagaske aure za kiyi????
Tace aure kuma? A’a
D’an shuru yayi yana nazari, toh tace a’a Bayan mum dinshi tace aure za’a Mata…..
Katse Mai tunani haulat tayi da fad’in, farhan zanyi aure Indai na samu Mai sona kuma wanda nake so, da an taba son had’ani da wani Wanda bana so…..  Wanda shine silan fad’awa ta cikin k……  Da sauri tayi shuru domin taso tayi baran barama.
Farhan yace inaji haulat
Tace andai fasa auren nawa
Wani irin ajiyan zuciya farhan ya sauke, tare da kallonta cikin ido  yace haulat zaki aureni???
Da sauri ta kura Mai ido, tare dajin bugun zuciya, lallai farhan ya had’u ba tun yau take sonshi ba, tunda ta Fara ganinshi, domin yanda yake nuna mata kulawa, wanda ko wace mace tana son taga ana nuna mata caring…..  Sau da yawa rashin nuna halin ko in kula da maza suke nuna ma matansu suke sa su Fara neman mata y’an uwansu, misali namiji ya fita office, ko kasuwa, kodai wajan da yake Sana’a, bazai kiraki ba, may be in kin kirashi bazai d’auka ba, namiji inya auri mace babu kalaman love duk sai ya daina, in baki da lafiya babu sannu koya jiki, inya biya kud’in magani shikenan, maza kuma kuna da laifi Sosai wajan fadawan wasu matan halaka, mace tana son Mai kula da ita Sosai, yau koda auren dole akama mace bata son miji…..  Indai yana kyautata mata wlh sai kuga ta Fara sonshi…..  Amma kai miji babu kyautatawa daga tayi abu sai hantara……  Idan tana da k’awa taga tana kyautata mata in bata da lafiya, bini bini ta kirata tana ya jiki kaza da kaza, in kawar Tana bin mata haka zatai ta janta a jiki in aka samu Mai raunin imani ganin yanda kawar tata take mata inta fito mata da kudirinta saita yarda ta amince Mata……  Wlh maza kuma kuna da laifi Sosai, damme bazaka dunga nuna ma matarka soyayya da kulawa ba,bayan aure shikenan daka anyi aure sai a fara d’aure fuska haba haba maza ya kuke haka, sannan saika gama d’aure fuska in dare yayi ka lallabo kana Kai hannu ko kunya babu????……..
 Farhan ne ya Katse ma haulat tunani da fad’in…. Haulat why r you silent and stare at me lyk this????
Murmushi tayi tare da fad’in nothing, kawai Ina mamakin abunda kace ne……
Farhan yace mamaki kuma? Kodai bazan samu karbuwa bane? Haulat tun ranan dana ganki Allah yasa min sonki, Wlh haulat so nake na aureki inhar kin amince Kece mace ta farko dana Fara ji ina burin in aura…….
Haulat wani irin murmushi ta saki tare da fad’in farhan zanyi tunani akai, yanzu dai muje train station Kar in makara…..
Tada motar yayi suka wuce kabuwa station, koda suka je saida suka zauna bayan yasai mata ticket, zama sukayi suna jiran lokaci,
Haulat ba komai take tunani ba, sai abunda suke aikatawa da hjy habiba, Uwar farhan gashi d’anta yau yace yana Sonta, in kuma tace bata son farhan tayi karya, tashin hankali uwa da d’a…….  Ido ta lumshe tare da fad’in Anya wannan abun zaiyi kuwa? Maganan farhan bai kamata in daukeshi da muhimmanci ba, domin ba Abu bane mai yihuwa naga tsiraicin mum dinshi na cita….. Yanzu kuma sai kawai inzo in auri d’anta Kai no way…….
Farhan ne ya Katseta tare da fad’in when zaki dawo? Koni inzo kaduna?
Dariya tayi tare da fad’in mudai yi waya kawai….. Dai dai lokacin aka fara fad’in su tashi train yazo…..
Tashi haulat tayi tana kallon farhan tare da fad’in sai munyi waya
Kai ya d’aga alaman ok tare da bata Wani karamin Leda daya ciro cikin aljihun shi,
Amsa tayi tana fad’in ngd tare da tafiya….. Koda haulat ta shiga jirgi tunanin farhan tai tayi wanda ta rasa dalili…….. Bud’e ledan daya bata tayi taga wani kwali karami anyi raping dinshi bud’ewa tayi taga wani zoban zinari Mai shegen kyau, bata san lokacin data saki murmushi ba……..
***
Yarima Aliyu ne zaune gaban iyayenshi yana mi’ka musu gaisuwa, mai martaba yace yaushe zaka Fara aiki a asibitin ka?
Yarima Aliyu yace Abba duk sanda ka bani umarni Niko yau zan iya Fara aiki….
Mai martaba yayi murmushi domin duk cikin yaranshi babu wanda yake so kaman Aliyu bawai dan yana d’a namiji ba kawai, a’ah harda irin biyayyan da yake mishi… Mai martaba yace saika shirya cikin satin nan ka Fara  sannan akwai wani fili da nake dashi a u/sarki saika Fara ginawa tunda a can zaka Fara aiki, Nasan wata rana iyalanka zasu bika can din in aiki yayi yawa …….
Mum din Yarima tace Kai Masha Allah, ina taya Yarima godiya
Mai martaba murmushi yayi tare da fad’in kin ara bakinshi kenan kinci Mai Albasa
Yarima yace Abba na gode Sosai Allah ya kara girma, Allah ya biya dan gidan Aljanna
Mai martaba ya amsa da Ameen tare da fad’in waziri zai baka takardun filin sannan zai nuna maka filin,
Mum dinshi tace sai ka Fara ginin mata biyu koh?
Yarima kasa magana yayi, sai mai martaba da yace ginin mata biyu kuma? Aure yace miki zai K’ara?…..
Mum tace eh gashi nan ya fad’a maka da bakinshi….
Mai martaba ya kalli Yarima Aliyu tare da fad’in ina jinka??
Yarima ya fara magana da fad’in Abba dama dama akwai dama….
Murmushi mai martaba yayi tare da fad’in dama me?  Gaba d’aya ka kasa magana, mai martaba yaci gaba da fad’in Aliyu inaso ka sani bazan hanaka k’arin aure ba, amma sai dai Ina Mai baka shawara kayi hakuri nan gaba domin baka dad’e dayin aure ba ko sati d’aya bakayi dayin aure ba, inaso kayi hakuri nan gaba kad’an sai a taso da maganan auren da kake son yi, amma fah shawara ce ba umarni ba…..
Yarima Aliyu yace Abba umarni ko shawara duk abunda kace min a matsayin umarni yake a wajena…. Abba kayi hakuri a kullum nafi son kaban umarni domin Ina Mai biyayya ga duk wani abunda kacemin
Mai martaba yace Allah yayi maka albarka, kaima Allah ya baka masu yi maka biyayya
Yarima ya amsa da Ameen Abba,
Mai martaba yace yarinyar y’ar inace????
Yace Abba a cikin kaduna suke, a u/kanawa ,sannan Abba mahaifinta bamai karfi bane….
Mai martaba yace babu damuwa, ya tarbiyan gidan yake??
Yace Abba Alhmdlh gidan akwai tarbiya domin yarinyar yau kwana hud’u data sauke AL’QUR’ANI Mai girma kuma hadda….
Mai martaba yace Alhmdlh, lallai gidan akwai tarbiya, Allah yasa na tsoran Allah ne sannan duk Wanda yake da ilimin addini yaji dad’in duniya da lahira zai iya zama da kowa, dukiya ko mukami bashi bane Abun dubawa tarbiya itace Abun dubawa, kaje zansa Ayi bincike akan gidansu……
Yarima tashi yayi yana mai yima mahaifin nashi godiya sannan ya fita cikin murna yana K’ara godema Allah da har mahaifinshi ya yarda yanzu tunda Mai martaba ya amince toh ya Gama samun Zainab insha Allah, lallai Allah Abun godiya bai taba tunanin zai samu amincewan mahaifin nashi cikin sauri haka ba……  Gefenshi ya nufa na da, koda ya shiga rufewa yayi tare da nufa bedroom dinshi ya fara kallon hotunan Zainab din, Wanda ya zana, tunani ya farayi Mai Zainab take son fad’a mishi wanda take tsoron fad’a???  Kodai in tambayi habib?? Nop bai kamata ba ita ya kamata ta fad’amin koma miye, and d way yanda take kuka yana nunamin abunda take son fad’a Kaman ya shafi rayuwanta? Toh mai take son fad’amin ido ya lumshe yana tunani…..  Na farko dai bata da wani aibu balle yace ga abunda take kokarin fad’amai, to Mai Zainab take boyemai??…….  Kai ban tunanin abun serious ne inda serious ne data fad’amin….  Wata zuciyar tace mishi kaika sani ko nauyin Abunne yasa ta kasa fad’ama? And kuma Inba serious bane mai yasa take kuka haka in tayi kokarin fad’a Mai? Ganin duk iya tunanin da yayi ya kasa gano komai yasa ya cire abun a ranshi tare da fad’in koma miye Indai Mai muhimmanci ne zai sani, yanzu dai ya kamata in mata surprise inje in ganta….
Bariki na kwance taji ana mata nocking, tashi tayi ta bud’e kofar da sauri ta saki kara tare da rungume haulat Tana fad’in mutanan abuja sai yau, ko waya babu…..
Dariya haulat tayi tare da fad’in kiyi hakuri bariki Wlh wayata ce ta fad’i bani da number d’inki yanzu, sai yasa ina dira kaduna Wajanki na fara zuwa Kinga ko d’akina banje na ajiye akwati ba nazo Wajanki…..
Bariki tace shigo mana
Haulat shiga tayi tare da zama tana fad’in Kai nasha abuja
Bariki tace gashi kin kara kyau da k’iba kaman bake ba, kai zama waje d’aya yayi
Murmushi Haulat tayi tare da fad’in dan bani wayarki in tura hotuna na tare da number d’inki, banda pic dina dake ko d’aya a phone dina
Bariki mi’ka mata wayar tayi tare da fad’in yunwa nake ji wlh Bari in duba habib
Haulat tace ok, haulat ta d’auki abunda take so cikin wayar bariki, sannan tayi murna da abunda ta samu a game da bariki din……
Bariki bata dad’e Sosai ba ta dawo, cikin d’akin tare da fad’in habib ya cika yawo kaman yaci kafan Kare….  D’aukan iPhone dinta tayi ta Fara kiran habib harya tsinke bai d’auka ba……
Haulat tace ashe kinyi iPhone ga Samsung ga iPhone gskiya bariki kina jin dad’i…. Tashi haulat tayi tare da mi’ka ma bariki wayarta Tana fad’in Bari inje inyi wanka in huta anjima nazo
Bariki tace ok but nima zanyi tafiya sai dai munyi waya
Haulat tace ok tana murmushi ta fita
Bariki ganin data dinta a bud’e yasa ta shiga whatsapp da message keta faman shigowa ganin Alh madu ya mata message yasa ta bud’e nashi ganin hotunan daya d’aukesu tayi,  tsaki taja tare da shiga gallery ta goge dan in an turo Mata hoto shida kanshi yake bud’ewa bata rufe ba, harda na Hon salis duk ta goge su Wanda ya tura mata kwanaki, duk wani hoto data d’auka wanda bai dace ba ta goge a cikin wayarta…… Kiran Alh madu ne ya shigo cikin wayarta kaman Karta d’auka saita tuna da hotunan daya turo Mata Wanda hakan ya tabbatar mata yana son Mata wani tuggu sai yasa ta d’auka tare da fad’in lafiya?
Dariya yayi tare da fad’in hotunan sun d’auku da kyau koh?
Tace tir da hali irin naka
Yace na baki awa biyu kizo inda nake ko yanzu ki ganki a internet ansa hotunan da mukayi kuma da fuskan wani ba nawa ba danna biya kud’i anyi min aikin , babu wanda zai gane an canza fuskan domin kwararru sukamin aikin kuma ba y’an kasar nan bane…..
Bariki k’asa tayi tana hawaye wayar ta sulale a hannunta……
MARYAM OBAM

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button