NOVELSUncategorized
NIDA AMARYATA 3 & 4

Tabbas naji dadin comments dinku,Kuma na Kara samun kwarin gwiwa da karkashin ci gaba da suburbudo muku novels din amaryar Alhaji sani, Oh ni ‘ya su! Gori na jiran fada,to Bari dai inyi shuru,in takarkare inyi kundun bala in sadaukar da
wannan page din a kyauta,zuwa gareka gagara badau 80k,kasha shagalinka da wannan page din yaseen duk na bar maka
3⃣-4⃣
Kana nufin Alhaji wannan ce amaryar taka?Wai Alhaji me kake son zamane? Me kake nema a rayuwarka? Kayi auren Nan bila adadin,amma har yanzu ka gaza hakura! Shin yanzu harta kaika da auro ‘yar cikinka matsayin matarka,to wannan me zaka mora a jikinta Banda…..kinga Hajiya dakatamun! Ya fada cikin Karamar hasala,kike tambayar me nake so,ai kinfi kowa sani,d’a namiji nake so,sannan Kuma inyi kara’in rayuwata,ke yanzu bada bane,na Kara wayewa,Ina son in dinga budawa Nima,saboda yanzu na Kara wayewa,in a baya Ina auren ‘yan ashirin da doriya,to yanzu ‘yan Sha nake nema,Kuma na samu,Dan haka ki Kara kwantar da hankalinki,Dan kin San karshen zancen,ke Kuma wuce mu tafi, ya fada Yana kokarin Jan hannun Nihila dake tsaye tana kallon bakin kowa tunda suka Fara magana.
Make kafada tayi,tare da fadin,” Ni Wallahi ba inda zani,kaje kaitamin tambayar ya ake wanka ba,to Wai dama mama in za’ai jaraba Wai sai mutum yayi wanka? Ta juya akalar tambayar ga Hajiya.
Wani mugun takaici ne yatasowa Hajiya Hafsa,domin kuwa tun maganar Mai gidan take cikin bakin ciki,wannan wace irin rayuwa ce,shin rashin samun da namiji cikin gida shike sa mutum yaita aure aure! In Bata Manta ba wannan itace Mata ta bakwai da Alhajin ya auro,Kuma ko wacce Saida ta haihu cikin guda shidan,iyakarsu su haihu da Kuma sun haifi mace to fa zaice ki Kara gaba,Dan shi ya gaji da Zama uban ‘ya’ya mata.Kallonta ta mayar garesu da suke tsaye tace,”ai saika Bata amsar shiriritar tambayar ta,ta juya cike da takaici,ta bar wurin.
Dariya Nihila tayi,sannan ta kalli Alhaji dake tsaye tace,kaga itama Bata San ana wani wanka in za’ai jaraba ba…ji tayi kawai yaja hannunta yayi saman da ita,suna shiga dakinshi ya saketa tare da zuba Mata ido na tsawon lokaci,itako ko’a jikinta illah ma kallon dakin data bige da yi, juyowa tayi,tare da fadin,” Amma dai baba Kai Dan napping ne? Inba hakan ba taya ka Tara wannan kudin haka,ji fa dakinka,Ashe har yafi na mama haduwa,Ni Kuma ji nawa abin tausayi,Kodan…..”ke dayalla rufawa mutane baki! ya fada cikin tsawa,ga mamakin sa,sai yaga ko alamar motsi batayi ba,illah murguda Masa baki da tayi tana gunguni,Bai San Mai take cewa ba,Amma hakan da tayi Saiya sa yaji wani Abu ya tsarga Masa a jikinsa gaba Daya,Sam Bai San lokacin Daya karasa kusa da ita ba,bakin nata yake kallo Wanda har yanzu take ta faman motsashi Kuma besan me take cewa ba.
“Zagina kike yi ko?
Ya furta with husky voice,
Kara turo bakin tayi tare da fadin” Ni kada kaimin sharri,duk rashin kunyata bana zagin babba,Kuma wlh kayi sa’a Dan Kaine da saina yi maka Allah ya isa”.
Ta karasa maganar tana murguda baki.
” NI din zakiyiwa Allah ya isa baby”?
” NI kada ka Kara kirana baby,Kuma yaseen danma Kaine Aunty hama tace Wai inyi maka biyayya kada in maka musu,shiyasa ma daka ce min dayalla na kyaleka,sannan Kuma Wai ka kirani baby,dubeka fa babba dakai kake cemin Wai baby!
Caraf taji ya cafe bakinta,inda ta shiga mutsu mutsun kwacewa,sosai yake kissing dinta,Wanda Saida yaji tsayuwa na neman gagarar su sannan ya saketa da zummar daukarta zuwa cikin dakin, kasancewar a falo suke,Yana shirin daukarta ta zille sai gani yayi ta fita da gudu,kafin yayi yunkurin rukota harta fita,dakinta ta shiga da gudu ta fada saman gado,ta jima kwance,sai Kuma ta mike ta Isa gaban madubin dakin,bakinta ta hau kallo tana shafa shi tana dariya ita kadai,ta jima a haka kafin ta shiga toilet,ta jima tana kallon toilet din da haduwarsa,sannan ta kunna showar,ta Dade tana wasa da ruwan sannan tayi wankanta jika’jika ta fito.
Shikuwa Alhaji sani ya fito yabiyota Amma sai yaji karar ruwa a toilet,Nan ya tabbatar da tana wanka,sai Kuma yaji Dadi a ranshi,Dan Yana son tsafta,Dan haka ya fice.
Itako Koda ta fito, wardrobe ta bude,aikuwa Kaya ta gani shirye,sai dai tayi mamaki,ganin duk English wears ne,Sam Bata damu ba,ta zabi wasu daga ciki tasa,Riga da wando ne tasa,tanata murna Dan tana son ta koma bakin aikinta,wato sililu,tana ko Gama sawa ta nufo wajen,kafar benen take shirin hawa,caraf idonta ya sauka kan ahlin gidan,duk sun hallara da niyyar yin breakfast,itama karasawa tayi taja kujera ta zauna,kallon kallo aka Fara yi tsakanin su Ameera,Dan Basu San wacece ita dinba,Sam Mami Bata kula kowa ba ta shiga sarving dinsu har ita Nihila,suna Shirin Fara ci,suka ji alamun sakkowarshi,sanye cikin wani lallausan yadi ruwan Madara sai zuba kamshi yakeyi,domin yayi kyau sosai,babu Mai cewa zai iya haihuwar wadan Nan yaran.yana karasowa yaja kujerar dake kusa da Hajiya Hafsa ya zauna,yayin da yaran nashi suketa kokarin gaishe sa,suna son su tambayi amarya suna Kuma Jin tsoro,amsawa yayi cikin rashin fara’a kamar ko yaushe,suma hakan be damesu ba,Dan sun Saba da halin mahaifinsu.abincin suke ci cikin nutsuwa,yayin da kowa yayi shuru,sai ji sukayi Nihila tace,
“Jar uba”
Kowa dagowa yayi ya kalleta,sai ji sukayi tace, mama dama baba Dan Indiya ne?
Cike da mamakin tambayar Hajiya Hafsa tace me Kika gani?
“To ba shine ba ya rikomin Nan kawai Saiya Fara yimin….wata muguwar kwarewa yayi,yayin da kowa ya maida kallonsa gareshi Yana mishi sannu.
“Sorry Daddy “cewar Ramla,aikuwa itama caraf Nihila ta cafe da fadin,
“Sorry daddy,this is no my life ko your this ‘yammatan,you hear Abincin is Dadi sosai that is why you do bigi Loma ba dole you kwarewa ba, sorry fa kun San nifa muguwar kwararriya ce a harkar turanci,ta fada tana kallon su Ameera da suka tsaya suna Jin boko iya boko.
Shikuwa tsabar bakin cikin turancin da tayi yasashi mantawz da wata kwarewa da yayi ya….
Dare yayi Kuma ‘yar mama ta cikin ciki ta gaji
Alkalamin khady ✍