DIYAM 23
❤️ DIYAM ❤️
By
Maman Maama
Episode Twenty Three : Shared Strength
Assalamu alaikum wa rahmatullah
Ina neman afuwar wadanda littafin Diyam ya saka kuka a kwana biyun nan, ina rubutu ne dan in faranta
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); muku badan in bakanta muku ba. Amma ina so ku sani ita rayuwa is full of ups and downs dole sai ansha wuya sannan za’a sha dadi. Ina so duk sanda kuke karatu ku saka a ranku cewa kirkirarren labari ne, non of this happened in real life duk da cewa zai iya faruwan. But labarin Diyam kirkirarren labari ne.
Daki ne aka bamu a gidan Alhaji Babba, dakin a babban palon gidan yake. Ciki daya ne da banɗaki mai dauke da gado da wardrobe a ciki, asalin dakin an yi shine saboda baki in sunzo daga Kollere anan suke dauka amma sauran matan gidan kowa in tayi baki to part dinta suke tafiya. Muna zuwa matan gidan duk suka firfito harda Hajiya Babba da kanta, aka zauna a palo ana ta kara yiwa juna gaisuwa da kuma jajanta abinda ya faru sannan aka saka yan aiki suka kara gyara mana dakin aka kai mana kayan mu can sai kuma kowa ya watse ya bar mu mu kadai.
Nina fara tashi na shiga dakin da aka bamu ina kare masa kallo, babu laifi yana da girma kuma da toilet a ciki amma kuma it doesn’t change the fact that aro aka bamu, aron kuma da nia ganina bama bukata. Na tuna yawan dakunan da suke gidan mu, Inna daki biyu da palo, Ummah daki biyu da palo sannan ga dakin Baffa ciki da palo ga kuma dakin waje, amma wai duk mun ajiye su mun dawo daki daya mun zauna da sunan taimako, taimakon me? In taimaka mana za’ayi ni a ganina ai food stuff ya kamata ake kai mana can gidan mu kamar monthly haka ko duk sanda aka samu dama, ko ake bamu kudi muna siyan abin bukatun mu da kan mu amma ba gurin zama muke bukata ba. Kuma ko kudin ne ma ni aganina zamu iya kula da kan mu ba sai mun dogara da kowa na. Yes, Baffa ya mutu amma bai bar mu fakirai ba, ya bar garejin sa da yake running for over twenty years, zamu iya cigaba da running kayan mu da kan mu, Sadauki can do that tunda yasan komai dashi ake komai kuma duk costomers din Baffa sun san shi.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Ni a ganina da mun yi zaman mu a gidan mu mun dora Sadauki akan komai kuma nasam as hard working and dedicated as he is zai iya yin komai. Ya cigaba da zamansa a gidan for security tunda za’a ce ba zamu zauna mu kadai babu namiji ba, in ma kuma Inna bata son zamansa a cikin gidan tana ganin ba muharramin mu bane ba zai iya zama a dakin waje ai, kuma yadda yake da kwarjini din nan babu wanda zai kawo mana raini a unguwa. Sadauki yana da gado a gidan da garejin, so it will be a mutual relationship wanda ni nake ganin mu zamu fi benefitting akan sadauki.
Ina ta tunanina har Inna ta shigo tana ta jera mana kayan mu a wardrobe din dakin, Asma’u tana tayata tana kuma mitar cewa wardrobe din tayi mana kadan sai dai mu bar wasu kayan a cikin akwati. Bayan sun gama na tashi na sake goggoge dakin na wanke toilet na jera mana toiletries dinmu da kuma kayan shafe shafen mu, sannan nayo wanka da alwala nazo nayi sallah tare da jera adduoin neman nasara akan Inna in samu ta saurare ni ta kuma yadda da shawara ta.
Da dare sai ga kwanukan abinci nan daga duk matan gidan kowa ta zubo ta aiko mana dashi, Inna ta karba tayi godiya amma daga ni har ita ba wani cin kirki mukayi ba Asma’u ce ta danci da yawa. A lokacin da muke cin abinci ne naga chance dina na magana da ita dan haka na zayyane mata duk tunani na da plans dina na kara da cewa “inna in mukayi hakan kamar mun dogara da kan mu kenan, ba ruwan mu da abinda za’a bamu da abinda ba za’a bamu ba. Duk wanda ya ke ganin zai taimaka mana saboda zumunci sai yaje har gidan mu ya taimaka mana in ma ba’ayi mana ba bamu da damuwa tunda muna da abin hannun mu. Inna dan Allah ki duba maganar nan”.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Tunda na fara ta ajiye spoon dinta tana kallona har na gama sannan ta fara girgiza kai tana kallona tace “yayi daidai Diyam, ya kamata a jinjina wa wannan tsarin naki. Amma bara in tambayeki, sanda kike yin wannan tsarin mune a ranki ni da Asma’u ko kuma bakin yaron can? Iye? Wato bakin cikin ki shine mun taho nan gidan an raba ki da shi shine kike so mu koma saboda ku cigaba daga inda kuka tsaya ko? Kuma ke yanzu a tunanin ki duk duniya in rasa wanda zan dauki ragamar rayuwata ni da yayana in bawa sai wannan yaron? Bani da yan uwane? Ko shi mahaifinku bashi da yan uwan da zasu kular masa da sana’arsa su kuma kular masa da iyalinsa? Ai ina sane na karbi shawarar Alhaji Babba ta cewa mu dawo gidan sa mu zauna saboda in raba ki da wannan yaron. Ina so ki saka a ranki cewa Alhaji Babba yayi mana mutunci yayi mana karamci daya dauko mu ya kawo gidan sa cikin iyalinsa saboda baya son mu zauna mu kadai cikin kunci da kewar mahaifinku dan haka daga ni har ku kamata yayi mu gode masa mu kuma yi iyakacin kokarin mu gurin faranta masa. Maganar gareji kuma shi Alhaji Babba da yake da mutum ne mai budadden ido kuma wanda ya san mutane na tabbatar zai san abinda ya dace ayi dashi. Magana ta karshe Diyam, daga yau sai yau, kar ki sake yi min maganar yaron nan”.
Bayan na kwanta na jawo bargo na lulluba sai na tambayi kaina ko a ina Sadauki zai kwana? Ko a wanne hali yake ciki? Sai kawai naji baccin ya dauke daga idona baki daya. Babu abinda ba zan iya bayarwa ba a lokacin dan in samu in san halin da yake ciki.
Kwanan mu biyu gidan Alhaji Babba kuma so far bamu da matsala. Muna samun kulawa da sympathy sosai daga jama’ar gidan amma ni a gurina na gaji da “Allah sarki” da “kuyi hakuri kunji” da kullum akeyi mana wanda babu abinda yake rage min a zuciya ta sai ma kara karyar min da ita da yake yi. Sannan kuma ga tunanin Sadauki daya addabi zuciya ya kullum sai karuwa yaje yi har cikin baccina wanda da kyarnake samu nake yi amma mafarkin Sadauki ne, ko inyi mafarkin rayuwar mu a baya ko kuma inyi mafarkinsa wai shi kadai a titi, har ganinsa nake yi a kwance abskin hanya ruwan sama yana dukansa duk kuwa da cewa nasan yaya ladi ba zata rabu dashi a titi ba, akwai makotan mu da akayi zaman mutunci dasu nasan ba zasu barshi a titi ba, akwai kuma marikin Ummah nasan shima ba zai bar Sadauki a titi ba, wannan sai yasa nayi tunanin to in duk wadannan ba zasu barshi a titiba why Inna? Ita me yasa ta barshi a titin ba tare da ko kayan sawa ba, wacce irin zuciyace da ita? Me yayi mata mai zafi haka?
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Bayan mun kwana hudu Mama tazo dan ganin yadda mukayi settling down, ta kuma taho mana da yan abubuwan da take ganin zamu bukata. Bayan sun kebe da inna ne take cewa “ni kuwa Adda ina so muyi magana dake a kan yaron nan dan wajen zainabu. Wallahi ranar nan ba karamin tausayi ya bani ba ke kuwa dan Allah ki sauko da zuciyarki akan sa, ji nakeda zainabu kukayi kishin ku kuma zainabu yanzu kasa ta rufe fuskarta haka zalika shima wanda akayi kishin a kansa, shi kuma yaron ina ruwansa?”.
Inna ta kuta tace “ni yanzu wani abu kika ga nayi masa, ko kallon banza banyi masa ba ballantana tsawa ko hantara. Abinda nace shine babu ruwa na dashi yayi gabas inyi yamma tunda wanda ya haɗa din ya raba yanzu. Ba shikenan ba.” Mama tace “amma at least magana mai dadi ma ai sadaka ce musamman ga maraya, yaron nan bashi da wani gata fa yanzu sai Allah” Inna tace “wai ni Hafsa kin manta da irin wahalar da nasha ne a dalilin uwar yaron nan, kin manta da irin kiyayyar da aka nuna min saboda ba’a aure ta ba? Saboda ita ake so bani ba? Kin manta? Kin manta har sakina akayi a kanta aka kuma dauki yata aka bata. Babu irin kokarin da banyi ba dan in jawo hankalin mijina zuwa gareni amma har ya bar duniya idanunsa ita suke kallo, zuciyarsa baki daya tana gunta duk kuwa da cewa nice uwargidan sa, nice uwar yayansa, ni ce yar uwarsa kuma ni ce wadda ya aura a budurwa ita kuma bazawara. To yanzu sai kiga laifina dan nace bana bukatar duk abinda ya shafe ta? Dan nace bana son ganin abinda zai tuno min da ita?”
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Mama tayi ajjiyar zuciya tace “shikenan. Allah ya kara sanyaya miki zuciyarki amma zan sake tuna miki da cewa yaron nan yana da gado a dukiyar da hamma Usuman ya bari, dai dai abinda zaki samu shima haka zai samu shida yaya ladi. Dan Allah Adda a fitar musu da abinsu a basu kinsan shi gado wuta ce, annabi ya fada cewa da mutum yaci gadon maraya gwara ya cika cikinsa da wuta.” Inna tace “wannan kuma masu rabon gadon ai sunsan wannan karatun, kuma nasan zasu basu abinsu duk samda aka zo rabawa” Mama tace “yaushe za’a zo rabawar? Ai yanzu ne yake bukatar su, tunda kin ki daukarsa ai kamata yayi a raba gidan a bashi kason uwarsa sai ya fitar da kofa ya zauna a ciki” Inna tace “wai ni Hafsa ki gayamin kina baya na ne ko kina bayan yaron nan ne?” Mama tace “ina bayanki Adda, wannan kuma shi yasa nake gaya miki gaskiya”.
A haka mukayi sati biyu a gidan, kallo daya zaka yi min kasan gabaki daya hankali na baya tare dani duk na kara ramewa dama ni ba jiki ba, kullum ina cikin tunanin halin maraicin da muka shiga ciki da kuma tunanin halin da Sadauki yake ciki. Ko wajen gate bani da damar fita saboda kullum ina tare da Inna ko aike na waje ba’ayi saboda akwai yan aiki da masu gadi. Rannan naji Hajiya Yalwati da tazo dakin mu tana cewa “wannan yarinyar kuwa anya ba sai anyi mata rubutu ba? Ita kadai sai inga kamar tana zabura” Inna tace “haka take yi wallahi, ina lura da ita ko baccin kirki bata yi” nan Hajiya Yalwati ta saka ni a gaba da nasiha akan yarda da kaddara mai kyau da marar kyau sannan tace inzo muje dakinta ta bani littafin wasu adduoi da zasu taimaka min. Naje na karba kenan na taho ina hanyar dawowa sai ga Murja da sauri tazo gurina tace “Diyam wai kizo wani yana kiranki a waje” nayi sauri na toshe mata baki muka matsa can gefe na tambayeta waye “to ni ina zan sani, mai gadi ne dai yazo ya a kiranki sai ya ganni ya fada min, wai wannan wanda yake zuwa gurinki sanda kika zo hutu” naji wani adrenaline rush yazo min, nayi kamar zan tafi dakin Inna sai kuma na dawo da baya na zare hijab din jikin Murja na saka nace “Please kar ki gaya wa kowa yanzu zan dawo” sai na wuce da sauri ita kuma ta bini da ido.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Da sauri na nufi inda muke zama in yazo, ji nake kamar inyi tsuntsuwa ko zanfi sauri. Tun daga nesa na hangoshi kuma na gane shi sannan naji dadin ganin sa sosai. He looks good, and that was all that matters to me a lokacin. Ina karasawa na lura da kayan jikinsa sababbi ne kuma masu kyau, he smells good too. Sai dai fuskarsa ce tayi betraying emotions dinsa dan idonsa ya fada ciki sosai kuma zagayen idonsa yayi baki alamun baya samun isashshen bacci. “Sadauki” na kira sunan sa da karyayyiyar murya, bai amsa ba sai murmushi da yayi min mai kokarin boye damuwarsa. Muka karasa zagayawa bayan dakin maigadi, Sadauki ya zauna akan ginin suckaway, wannan ya bani damar ganin gefen kansa inda akayi masa dinki. Na zauna nima a kusa dashi ina fuskantar sa kawai sai hawaye suka fara zarya a kumatu na, bai hanani kuka na ba sai ma ya miko min handkerchief dinsa na cigaba da kuka na, sai dana gama na share hawaye na sannan yace “dama mai neman kuka ne aka jefe shi da kashin awaki, ke din dama kuka baya miki wahala” nace “Allah yaji kan Baffa da Ummah” yace “ameen. Naje na kai musu ziyara kaburburan su. Suna kwance a sides din juna kuma ina fata da zaton suna aljanna a tare” sai naji dadi sosai a raina, dadin yadda naga ya dauki abin nima sai naji na samu courage din facing rayuwa a koya tazo min. Nace “kai kuma fa? Wanne hali kake ciki? A ina kake a zaune?” Yayi murmushi yace “ina gurin Alhaji Bukar (mutumin da yaya ladi take gurinsa) and they are treating me well, too well even. Ya gaya min cewa zai kaini gurin mahaifina, ya san shi ashe” na bude ido da baki “wow. Congratulations Sadauki, yaushe zaku je?” Ya girgiza kansa yace “I don’t know. Ban san shi ba Diyam, bansan waye shi ba and for all I know zata iya yiwuwa ma bai san nayi existing ba, zai iya yayi denying dina yace ni ba dansa bane ba” Nace “amma ta yaya zaka sani in baka je ba? Nasan Sadauki na babu abinda yake tsoro just go kayi clearing doubt dinka and move on” ya gyada kai yana kallona yace “so I have your blessings kenan ko?” Nace “of cause you do”.
Sai kuma na tambayeshi abinda yake raina tunda na ganshi “Sadauki me yasa kazo? Bayan abinda Inna ta tayi maka bayan yanzu babu Baffa kuma gashi ka samu wani mai rikon gashi kuma zaka je gurin babanka, me yasa kazo gurina? Ba ka gudun a wulakanta ka?” Ya dan bata rai yana kallona yace “me yasa ba zanzo ba to? For starters I love you, always have and always will. Na biyu duk abinda ya faru dani babu abu daya da yake laifinki dan haka baxanyi fushi dake akan abinda ba ke kika yi min ba. Na uku Baffa, a gurina darajar Baffa ta wuce in yi fushi da iyalinsa dan babu ransa, sannan……..” Sai yayi shiru yana kallona, nace “sannan me?” Ya sauke idonsa kasa Yace “sannan lokacin da mukayi accident din, he looked at me straight in the eyes ya ce in wani abin ya same shi in kula daku ke da Asma’u”.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Na sunkuyar da kaina inajin sabbin hawaye suna zubo min. Yace “amma bansan ta yadda zan iya kula daku ba Diyam, innar ku bata so na na sani, bansan ta yadda zan iya juyo da hankalinta ta soni ba tunda bansan abinda nayi mata wanda ya saka bata son nawa ba balle in daina. Diyam ina tsoron kar lokacin auren ki yayi in nema a hana ni akan dalilin da ni kaina ban sani ba, I don’t think my heart can take that”. Mun jima muna hirar yadda future dinmu zata kasance, sai daga baya yace “bara in tafi Diyam kar in jawo miki fada. I just want you to know cewa am okay, dan haka kema ya kamata ki rage wannan koke koken haka ki tsayar da hankalinki guri daya. And everything is going to be alright” nayi murmushi nace “ai na samu strength daga gurinka Sadauki, kayi sharing strength dinka dani” ya mike tsaye yana kallona yace “Aliyu shine sunan, Sadauki shine inkiyar, so ofcause am going to be alright”. Muka yi sallama yana yi min alkawarin in sun saka ranar zuwa gurin babansa zai zo ya gaya min saboda inyi masa addu’a.
Shine a gaba ni ina binsa a baya, muna fitowa yayi hanyar gate ni kuma nayi hanyar cikin gida ina waigensa, a lokacin ne kuma aka budewa Alhaji Babba gate ya shigo gidan sukayi clear da Sadauki kafin Sadauki ya fita. Na kara sauri kafin yayi packing Ina jin bugun zuciyata yana karuwa amma ina kama handle din kofa naji muryar Alhaji Babba a baya na yace “Diyam, zo nan”
Not edited. In anga typos ayi hakuri Please.