NOVELSUncategorized

DIYAM 29

❤️ DIYAM ❤️

By

Maman Maama

Episode Twenty Nine: The Lost Flower

Warning: Emotional Episode

Ta mike zata fita sai na rike zanin ta na kifa fuskata a cinyarta na fara kuka mai tsuma zuciya amma sai tasa hannunta ta cire hannuna daga
zaninta ta juya ta fita. Na rufe fuska ta da hannayena ina kuka, ji nake kamar wannan auren shine karshen rayuwata, ji nake ina ma mala’ikan mutuwa yazo ya dauki raina, anya kuwa zan iya yiwa Saghir biyayyar aure kamar yadda ya kamata? Kuma gashi aljanna ta tana defending on wannan auren alakakai din and I so much want to go to jannat idan na mutu, wannan yasa na fara addu’ar Allah yasa in mutu a wannan ranar. 

Ina cikin kuka na su murja suka shigo suka zagaye ni, Rumaisa tace “ke baki san yanzu an daina kukan aure bane ba wai? Wannan ai sai ki bada mu in abokan ango suka zo” murja tace “suka zo ina? Wai nan gidan? To ni kam bada ni ba babu wani siyan baki da zan zauna yi yazo ya hada mu ni da amaryar ya huce haushin sa akan mu” Rumaisa tace “ke dan Allah ki daina fadar haka ai sai ki saka taji tsoro”. Suna ta hirarrakin su ni dai na mike nayo alwala na gabatar da sallar isha ina kaiwa Allah kuka na.

Ina nan kan sallayar sai na jiyo muryar yaya Mukhtar daga palo, sai ga Rufaida ta shigo tace “wallahi yaya Mukhtar yace duk ku fito mu tafi in ba haka ba sai dai ku kai kanku gida dan shi tafiya zaiyi. Wannan unguwar tasu kuwa ba abin hawa zaku samu ba, angon kuwa in ya zo ko suma kuke ba zai kaiku gida ba” kusan duk a tare suka mike suna harhada kayansu. Na kalle su da kumburarrun idanuna nace “yanzu tafiya zaku yi ku barni ni kadai a gidan nan?” Rumaisa tace “da anjima angonki zai zo, kuma ai naga kuna da maigadi” Murja tace “idan yayi tafiya kiyi min waya sai inzo in taya ki zama, amma in yana nan ba zan zo ba”. Yaya Mukhtar ya sake kwala musu kira dan haka suka fice da sauri. 

Ina jinsu suka sauka daga bene, ina jinsu suka fita daga palon kasa suka rufe kofa sannan naji sun shiga mota an bude musu gate sun fita, na tashi da sauri na leka ta window na hango hasken motar su har sun dau hanya. Sai kuma na tsaya ina kare wa unguwar kallo, babu gidaje sosai sai kwangwaye wannan ya kara wa unguwar duhu. A bakin gate naga mai gadi a zaune akan benchi da radiyo a gefensa. Sai naji wani irin loneliness sannan kuma naji wani irin tsoro. 

Na haye kan gado da sauri sai kuma wani tunani yazo min sai na tashi da sauri na bude kofa na fita. Sai na ganni a cikin wani palo madaidaici wanda aka kawata da kujeru da kayan kallo da adon frames a bango da  sauran tarkace. Kofofi uku ne a palon, na fara bude su daya bayan daya ina neman kitchen amma sai naji daya a rufe take dayar kuma wani bedroom din ne kudan irin wanda na fito daga ciki sai banbancin colors. Na sauka daga bene da sauri shima palon ne amma yafi na sama girma da tsaruwa, sai wadansu kananan bedrooms guda biyu da dining room mai hade da katon kitchen. Ban tsaya kallon komai ba saboda yadda jikina yake karkarwa saboda tsoro, na shiga kitchen din na fara bude drawers ina neman abinda ya kawo ni, can naga set dinsu, wukake, na dauki wadda naga tafi kowacce girma na boye a rigata na sake fita da sauri na haye sama. Dakin da aka kaini na koma na tura kofa da niyyar locking amma sai na ga babu key a jiki. Na fara fara neme neme cikin lockers din dakin amma babu key babu alamarsa. Na shiga toilet na duba nan ma babu. Sai na dawo na zauna akan gado kamar zanyi kuka amma tears din sun tsaya, maybe sun kare. A hankali nace “Sadauki, Please come and take me away from here”.

Sai na kwanta na dunkule a guri daya, na jima a haka sannan bacci ya fara fusgata ina yi ina farkawa a tsorace cike da mafarkai, wani mafarkin wai Sadauki tazo yace in tashi mu gudu, wani kuma wai Saghir yazo ya zare belt dinsa yace ba yace kar in sake inzo gidan nan ba? 

Cikin baccin naji karar bude gate, na tashi zaune a tsorace, sai nayi sauri naje na kashe fitilar dakin sannan nazo na leka window, mota naga ta shigo tayi packing, sai kuma ya fito yana tafiya unsteadily. Ina lura da maiigadi yana gaishe shi amma bai ko kalle shi ba ya taho cikin gidan. Nayi sauri na tura kofar dakin da na ke ciki sannan na dauki wukata na tafi can lokon gado na kudunduna a cikin duvet, naji ya bude kofar palo ya shigo amma banji ya rufe ba, najiyo shi yana hawowa sama sannan naji ya bude kofar dakin da yake kusa da inda nake, sai kuma takunsa yana tahowa sannan naji ya bude dakin da nake, na dauke numfashi na ina kara addu’ar Allah ya dauki raina. 

Ya kunna fitila sai can kuma naji ya kashe amma na tabbatar ya ganni, sai kuma naji ya karaso inda nake kudundune ya saka kafarsa mai sanye da takalmi ya dake ni da ita “ke!” Na dunkule hannuna a handle din wukata na mike da sauri ina nuna shi da ita, fuskata cike da hawaye nace cikin murya mai karkarwa “if you dare touch me!” Ya tsaya yana kallona ta kasan ido, da mamaki a fuskarsa sannan cikin wata irin murya da tafi yi min kama data yan maye yace “what? What will you do?” Na sake nuna shi da wukar “in ka kara wani takun kusa dani na rantse I will….” Ya tako step din without hesitation yace “you will what?” Gabadaya jikina karkarwa yake yi hatta wukar hannuna rawa take yi tana neman faduwa, hannu daya yasa ya doke hannun nawa sai wukar ta fadi. Na dunkule a kasa “don’t touch me please” sai yasa hannu ya kamo wuyan rigata ya mikar dani tsaye, ya hada ni da bango sannan ya kawo fuskarsa dai dai tawa, wani wari naji daga bakinsa, ba warin kazanta ba amma wani wari marar dadi, nayi saurin dauke kaina yace “mena gaya miki zanyi miki in kika sake kika shigo gidan nan? Kin dauka wasa nake yi dake ko?” Nace “wayyo Allah na, wayyo Sadauki” ya saki wuyana yana kallona “Sadauki? Sunan saurayin naki kenan? To yazo ya nuna sadaukan ta kar tasa in gani” nayi shiru a raina ina fatan zaizo din, yace yana kara matsowa jikina “bana ce miki karki zo gidan nan ba?” Na girgiza kai nace “nima kawo ni akayi, Bani nazo da kaina ba. Please ka mayar musu dani kace ba ka sona” yace “with pleasure. Amma kafin in mayar dake sai na yi musu proving abinda na gaya musu su kaki yarda. Kinyi min kankanta da aure” yana fadin haka sai ya saki wuyana, sannan ya hankada ni na fada kam gado kaina ya bugu da jikin frame din gadon. Na fara ganin dusu dusu a idona amma duk da haka sai nayi kokarin mikewa sai dai nauyin da naji a kaina ya sa na kasa ko motsi. Amma sai na takarkare tun karfi na zunduma ihun kiran Sadauki a lokacin da naji zani na ya bar jikina. Sai kuma naji wani piercing pain daya taho tun daga kasana ya dire har cikin kwakwalwata. Sai muryar ihun ta dauke, numfashi na ya dauke, naga wani haske a idona. The last thing da naji kafin hankali na ya barni shine muryar Sadauki lokacin da yake ce min “everything is going to be alright”.

A short episode. But mu fara jajanta wannan lamarin tukunna.

Dear parents, This might be what will happen to your daughter in kuka rufe idon ku kuka aura mata wannan lalataccen dan masu kudin da bata so, ko wannan alhajin da yake zuwa a babbar mota, ko kuma wannan dan uwan naku da yaki aure shekara da shekaru kukayi tunanin bara ku hada su dan inganta zumunci. It might not always be the right choice, especially idan wanda za’a hada ta da shi din ansan bashi da halayya mai kyau. Yaya amana ne a hannunmu, don’t trade them for wordly things please.

Yes, addini ya yarda iyaye su taya ƴaƴansu zaben mijin aure, amma kuma bai ce a tirsasa musu ba. Akwai ingantaccen hadisin ma da ya nuna haramcin hakan.

Allah ya sa mu dace.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button