DIYAM 30

❤ DIYAM ❤
By
Maman Maama
Episode Thirty : The Empty Heart
Sama sama nake jin maganganu a kusa dani, a hankali ake maganar amma sai naji tamkar wanda ake
hayaniya saboda ciwon da kaina yake yi min. Na kai hannu a hankali na dafe goshina sai naki ance “sannu Diyam. Ta farka” naji muryar kamar na santa amma sai na kasa gane mai ita. Wannan yasa nayi kokarin bude ido na amma sai naji sunyi min nauyi. Na mayar dasu na rufe. Sannan na fara tunani where am I? What happened? A hankali pictures din abubuwan da suka faru suka fara yi min yawo a kaina. Mutuwar Baffa da Ummah, bankwana na da Sadauki, auren dolen da akayi min, abinda Saghir yayi min da daddare. Nayi saurin bude idona sannan nayi kokarin tashi zaune ina girgiza kaina hoping in ganni a gidan mu in ga cewa duk wannan wani mugun mafarki ne nayi. Amma wani irin azaba da naji daga kasana wadda cikin second daya ta gauraye duk sassan jikina ita tasa na koma da baya na kwanta, bana bukatar assurance, wannan ciwon ya tabbatar min cewa ba mafarki nayi ba, ya tabbatar min cewa Saghir raped me. Na runtse idona ina so hawaye yazo min amma yaki zuwa sai wata irin kuna da zuciyata take yi min. Na tuno alkawarin da Sadauki yayi min “ki saka a ranki cewa Sadauki zai kasance tare dake a koda yaushe, kome ya faru dake ko me kike yi ki saka a ranki cewa I will always be watching over you. This is my promise to you” sai nace “where were you Sadauki?” Duk sanda yayi min alƙawari yana cikawa amma ta gaza cika wannan. Na kai hannu zan taba inda nake jin tamkar anyi min tsarki da attaruhu sai naji an rike min hannu, na bude idona naga Adda Zubaida a zaune a bakin gado tana rike da hannuna, nabi dakin da kallo, bakin dakin nan ne dai da aka kawo ni jiya aka ajiye tamkar akuyar da akayi sacrificing dan a kama zaki, dakin da zakin kuma yazo ya karasa destroying rayuwata, ya karasa karbar dan sauran abinda nake rakama dashi.
Na sauke idona kan Adda zubaida da fuskarta take nuna tsantsar tausayi na. Ta kara cewa “sannu Diyam” sai naji wata muryar kuma a gefe na itama tana yi min sannu, na juya naga wata mata da muke kira Uwani, kamar kanwa take a gurin hardo dan haka kamar kaka ce a gurin mu. Na kalli jikina naga doguwar riga ce yar kanti marar hannu. Na koma na kwanta a hankali nace “Adda ki kirawo min Inna dan Allah ki ce nace dan Allah tazo ta daukeni daga gidan nan” ta girgiza kai tace “Diyam ba zan iya ba, bazan iya gatawa innarki wannan mummunan labarin ba. Da wanne zata ji. Na dai gayawa su iyayen tantirin. Su san ga abinda dansu ya aikata” Uwani tace “to ya zasu yi? Sai addu’a” Adda tace “wallahi uwani duk abinda Saghir ya zama a duniya da sa hannun mahaifansa. Basa son laifinsa, soyayyar da suke yi masa ta rufe musu ido ko me yayi basa tsawatar masa. Duk dukiyar Alhaji fa ta salwanta a hannun Saghir kullum in ya di ba ya tafi sai sun kare zai dawo, in muka yi magana ace masa ai kasuwanci yake yi bayan mun san babu wani kasuwanci da yake yi sai iskanci. Sai yanzu kuma da lokaci ya gama kurewa sannan suke son su gyara shi. Yanzu kalli uban kudin da aka kashe aka sai masa auren nan aka sai masa gidan nan aka dauki kankanuwar yarinyar nan marainiyar Allah aka bashi amma dan iskanci shine a ranar da aka kawo ta yayi mata wannan wulakancin ya tattara kayansa ya gudu” uwani tace “au wai tafiya yayi? Ina ya tafi?” Adda tace “to wa sani ne. Da assubar fari ya kira wayata wai in taho gidansa Diyam zata mutu, ina jin gaka nasan yayi tsiyar. Haka nazo na samu Diyam tana numfashi da kyar maigadi ya gaya min tun assuba yaga ya saka akwati a mota ya fice, na sake kiran wayarsa bata shiga. Ni kuwa na kira uwar da uban nace to ga abinda Saghir ya aikata nan kuma ya gudu. Alhaji yayi ta salati, in ba sa’a muka ci ba in anjima kiji shi a asibiti hawan jini ya tashi, kuma hawan jinin mun san Saghir ne ya sama masa. Ita kuma Hajiya Babba saboda tsabar son kai ina gaya mata sai ta kama rokona wai dan Allah kar in gaya wa kowa mu bar maganar a tsakanin mu, in kai Diyam asibiti amma kar in gaya wa kowa. To ni wa zan iya gayawa wannan kayan takaicin ne?”.
Uwani tace “hmmm, ni ina bacci ai taje ta same ni wai dan Allah in taho gidan nan in taimaka wa Diyam, ina ji nasan an yi aika aika kenan. Kuma dan dai ya saka mata karfi ne, amma in da a hankali ya bita babu abinda zai same ta” Adda tace “to ina zai bita a hankali? In yayi haka ai bai cika dan iska ba” sai tayi tsaki “ni ban ma san yadda zanyi ba wallahi. Na daiyi mata ruwan dimi na dan gasa ta, ni ba zan iya kaita asibiti ba wallahi wannan ai abin kunya ne, in je ince musu me? This is a rape case zasu iya cewa sai na dauko police” ta sake yim tsaki “Allah wadaran naka ya lalace. Amma ai duk wanda ya sai rariya dama yasan zata zubar da ruwa”. Sai kuma ta dauko waya tayi kira. “Hello, sister Asiya dan Allah in kina off ki taimaka min, wata kanwata ce akayi wa aure jiya kuma yar karama ce wallahi…..to kinsan halin maza… Dan Allah in baki address din kizo ki duba min ita” sai kuma tayi mata godiya ta katse, ta sake tsaki tace “this is very uncomfortable wallahi”.
Duk maganar da suke yi ina jin su amma na rufe idona kawai dan bazan iya tankawa ba. Addu’a kawai nake jerawa a cikin zuciya ta “ya Allah duk wanda yake da hannu akan wannan wulakancin da aka yi min ya Allah ka saka min. Ya Allah tafiyar nan da Saghir yayi Allah kasa yayi hatsarin mota ya mutu kar ya dawo. Ya Allah ka hada shi da yan fashi a hanya su sabauta shi kamar yadda ya sabauta ni. Ya Allah ka saka ginin gidan da zai sauka ya fado masa cikin dare ya tarwatsa shi kamar yadda ya tarwatsa rayuwata”.
Ina nan kwance matar tazo, ina jinta suka gaisa da Adda zubaida da Uwani. Sannan ta zauna kusa dani tace “amarya” na bude ido na kalleta na rufe, tace “kar ki zama raguwa mana. Tashi tsaye mu gani” nayi saurin girgiza kaina sai ta kama kafafuwana tayi bending dinsu, nayi kara saboda jin cinyoyi na nayi kamar wadda nayi frog jump, ta bude rigata tana dubawa tace “babu tear, the place is just sore kuma akwai bruises” ta rufe rigar tace “zanyi mata allurar da zata rage mata pain sannan zan rubuta muku magani ku siyo mata. Sai take amfani da ruwan dumi sosai” Adda tayi mats godiya sai ta juyo tana kallona tace “ina angon? Yazo ya mayar dani gida” ita as a joke ta fada ni kuma kalmar angon ma bata min rai tayi. Har zata fita ta juyo ta sake kallona tace “amma yarinyar nan tayi kankanta da aure wallahi Zubaida. Wai dama har yanzu fulani kuna irin wannan auren?” Ban dai ji amsar da Adda ta bata ba suka fita.
Ranar har dare Adda Zubaida tana guri na, kuma ta saka ni na shiga ruwan zafi sosai sannan kuma ta dafa min abinci mai kyau ta matsamin na ci. Sai kuma ta saka ni nayi tafiya wadda sanda ina yi ji nayi kafafuwana kamar ba’a jikina suke ba. Uwani ce ta zauna ta kwana a gurina washegari sai ga kayanta Alhaji Babba ya saka a aiko mata dasu yace ta zauna a gurina har sai Saghir ya dawo daga tafiyar da yayi. Sai da nayi kwana uku a sama ina jinyar kaina sannan na iya saukowa kasa, ina saukowa daga bene idona ya sauka akan katon hotonsa ya sha shadda army green wadda ta kara haska farar fatarsa, ya turo hular nan gaban goshi fuskarsa dauke da murmushi, sai a lokacin nayi tunanin kamar ban taba ganin murmushin sa ba. Na taka naje har gaban hoton na tsaya ina kare masa kallo sai kuma na saka hannu na ciro hoton na sauke shi kasa sannan na juya shi ya koma kallon bango.
Jikina ya warke, amma tabon zuciyata yana nan kuma banajin zai warke har abada. Saghir kuma kullum zuciyata kara tsananta tsanarsa take yi. Ko mai irin sunansa baba son inji an ambata ballantana shi. Babu sallar da zanyi ba tare da nayi addu’ar neman sakayya tsakani na dashi da duk wanda ya aura min shi ba. Kullum kuma da fargabar dawowarsa nake kwana da ita naje tashi. Ko wani kwakwkwaran motsi uwani tayi sai na firgita ballantana in naji an taba gate. Muna da kayan abinci wadanda aka kawo da sunan kayan gara, kudi kuma duk karshen sati Alhaji yana aiko mana dashi shi dai kawai burinsa in zauna a gidan. Uwani tana tare dani, kuma duk weekend su murja ko su Rumaisa sukan zo su kwanar min biyu, wannan sosai yakan rage min kewa amma a zahiri a zuciyata kuwa empty nake jin heart dina.
Kwanaki suka wuce haka satittika, sai watanni suka biyo baya har nayi wata uku a gidan Saghir amma babu shi babu alamar sa. A ranar da na cika wata ukun ne Hajiya Babba tace mu shirya muje gida mu kwana biyu. Da wuri driver yazo ya dauke mu muka tafi. Tun daga bakin gate na lura da yadda gidan ya chanja, ma’aikata sun ragu, motoci ma haka, gidan kuma yayi datti flowers sun mutu.
A main palo muka samu Hajiya Babba, har da mikewar ta tsaye ta tarye mu da fara’a “sannunku da zuwa uwani” ta jawo ni jikinta zata rungume ni sai na zame na durkusa na gaisheta, ta amsa da fara’ar ta ni kuma na mike na nufi dakin inna ta ina jin missing dinta a raina, ina jin Hajiya Babba tana cewa “Masha Allah, lallai Diyam, wannan girma haka kamar ana hura ki?”
Ina shiga na tarar da Inna tana ta murnar zuwa na itama. Na je na rungume ta tana ta dariya ta dan tura ni baya tace “Diyam kinyi girma haka? Alhamdulillah, naji dadin ganin ki sosai. Ni ina nan ina ta fargabar halin da kike ciki gashi Saghir ance yayi tafiya kasar waje business ya rike shi” na zauna akan gado ina rungume da Asma’u ina dariya. Ta zauna gefe na tana ta yi min tambayoyi game da halin da nake ciki ni kuma ina bata amsa a takaice. Tace “naso inyi miki girki tunda aka ce zaku zo, nasan kina son tuwo amma kinsan bana girki a gidan nan” na kalle ta sai na lura da yadda ta fada tayi baki bakinta duk ya bushe. Nace “inna ku ya kuke ciki? Lafiya dai ko?” Tace “hmm, lafiya lau” nayi shiru dai ina kallonta dan na fahimci ba karshen maganar ba kenan. Sai nace “Inna an saka Asma’u a makaranta kuwa?” Tace “eh an saka ta” sai ta sake shiru, ta jima kuma sannan tace “na jima inata faman bi akan zancen makarantar yarinyar nan, da kyar na samu aka saka ta amma wai ga makarantar da sauran yaran gidannan suke yi sai aka dauke ta aka saka a makarantar gwamnati. Tana kallon yaran zasu shiga mota a tafi dasu makaranta ita kuma sai dai ta tafi a kafa, har kuka sai da tayi min wai ita makarantar su siyama take so amma haka ba bata hakuri saboda babu yadda zanyi”
Naji zuciyata tana zafi nace “to Inna ke ki saka ta ata kudin mana? Ina kudin da ake samu a garejin baffa duk wannan watannin ayi amfani dashi mana a saka Asma’u a makaranta mai kyau” tace “hmmm. Diyam kenan. Wanne gareji kuma kike magana? Tun a lokacin bikin ki nayi wa Alhaji maganar gare jin kinsan me yace min?” Na girgiza kaina tace “yace garejin shi aka siyar akayi miki kayan daki” na bude baki ina kallon ta nace “garejin? Da duk motocin da suke ciki?” Eh kawai tace, na sunkuyar da kaina sannan nace “filin Sadauki fa? An bashi kayansa?” A can kasa ta amsa tace “har dashi ya sayar”.
Na tashi na shiga toilet na hada kaina da kofa, rabona da in kira sunan Sadauki tun ranar da aka kaini gidan Saghir amma ni kadai na san me nake ji a zuciyata, I missed him so badly dan tunda nazo duniya ban taba yin wannan dadewar ba tare dana ganshi ba yanzu kuma ambatar sunansa ya tayar min da mikin dake cikin zuciyata. Na tuna ranar da yaje school gurina da murnarsa yake bani labarin Baffa ya saya masa fili, kuma da kudinsa daya tara masa ya siya masa his hard earned money amma wai Alhaji Babba ya siyar. Ban roki Allah sakayya bama saboda nasan tabbas zai yi maybe slowly but surely.
Bayan na dawo dakin ne uwani ta shigo suka gaisa da Inna ta kuma kawo min mangwaro na dana siya a hanya. Inna ta karba tana cewa “wannan mangwaron Diyam ai bai nuna ba aka baku shi” na karba na fara sha ina cewa “yafi dadi ai” sai ta tsaya tana kallona sannan ta juya ta kalli uwani tana girgiza kai sai naga uwani ta gyada mata kai, sai kuma suka juyo suna kallona a tare ina ta rasgar danyen mangwaro. A raina nace “su kuma wadannan menene naga suna magana da ka kamar kurame?”.
Not edited