Uncategorized

HEEDAYAH 13

 

Parking Junaid yyi kofar gidan Baffa ya kashe motar sa ya bude ya sauka, sanye yake da kananun kaya, walking calmly ya isa gate suka gaisa da Mai 

gadi sannan ya shiga gidan, baya bukatar tambayar entrance don tuni ya hango, yana isa bakin kofar yayi knocking, bbu bata lkci aka bude kofar, 

kanwar Sudais ce ta bude kofar, yana kallonta da murmushi fuskarsa yace “Good evening” tana kallonsa irin kallon rashin sanin tace “Welcome…” 

Muryar Abba suka ji yace “Is that Junaid” Junaid yayi kasa da kai yace “Ina yini Abba” Abba yace “Lfya lau, Zainab ki kai sa bangaren Kaka” Zainab 

na kallon Junaid tace “Toh” bin bayanta yyi suka nufi parlon kaka, Abba kuma ya fita rike da makullin motarsa, da sallama Junaid ya shiga parlon 

kaka, Mami dake tsaye rike da jakarta alamar xata wuce ta juya tana kallonsa, Kaka ta kalli Junaid sannan ta kalli Mami tace “wannan ne d’an naki?” 

Mami tayi murmushi tace “Eh Mama” kaka tace “Ahh ba shakka… Kyakkyawan bafillatani da shi wllh, ya ma fi ki kyau ai, da ganin ubansa ya yo….” 

Mami dai na murmushi tace “To sai na shigo da daddare kaka, bari in je” kaka tace “A’a ki yi xaman ki kar ki wani wahal da kanki ba gashi ina kula 

da ita ba tsakanina da Allah….” Mami tace “Toh shkkn mama” Daga haka ta fita parlon, Kaka na kallon Junaid dake tsaye har sannan tace “To kai ko 

ka xauna mana d’an nan” ya xauna smiling broadly, with respect yace “Ina yini” Kaka na washe baki tace “Lafiya lau, ya sunan naka?” Yace “Junaid 

Muhd…” Tace “Junaidu sai kaji kuma wai yarinya ta gurde koh? To ni kai na ban san yanda akayi wnn bala’i ya faru ba, amma dai na gode Allah tunda 

ba karyewa tayi ba….” Junaid yace “Allah ya kara kiyaye gaba” Kaka tace “Ameen kai dai…. Don ma uwarka na da fahimta na lura ita ta lallaba 

Amadu bai dau abun da xafi ba, kasan sa da xuciya, Kuma kasan shi ya tsinto makauniyar a titin kano tana galantoyi….” Junaid dai bai ce komai ba, 

kaka tace “To ka leka ta tana bacci can uwar daka ka duba ta, amma ta fiye son jiki yarinyar, d’an bugewa fa kafar yyi amma duk makota bbu wanda 

bai shigo gidan nan ba, ke Zainab kai sa ya ganta, kuma bance ki tsaya kusa da kumbo na ba, kinfi kowa min sace sace a gidan nan” kasa motsi Zainab 

tayi, shi dai junaid kansa na kasa, kaka ta ja tsaki ta mike tace “Haka nan suke min ban isa in sa su aiki ba, ae dai kaga taki kai ka, to ba 

ruwana ba biyesu nake ba, tunda ‘ya yana na min biyayya ae shkkn” har dakinta ta kai Junaid tace “To ka ganta….” Junaid na tafiya a hankali ya 

isa gefen gadon kaka yana kallon Heedayah dake bacci, kaka ta juya ta fita, durkusawa yyi yana kallon kafarta ya kai hannu kneel dinta, kwace kafar 

tayi tana turo baki alamar ta ji xafi, ta juya masa baya ta ci gaba da baccin ta, mikewa yyi walking gently ya koma dai dai fuskarta ya durkusa, 

bayan seconds kusan goma yace “Ina ke maki ciwo?” Bude fararen idon tayi a hankali kamar irin xata gansa din nan tayi shiru staring into space bata 

dai ce komai ba, lkci daya kuma ta mike xaune tace “Ina Abba” Bai ce mata komai ba, ya dau ledan da ya gani gefenta dauke da drugs yana dubawa, 

bude kofar dakin aka yi junaid ya juya, Sudais ne tsaye bakin kofar yana kallonsu, Junaid ya mike shi ma yana kallonsa, Sudais ya karasa ya basa 

hannu nan suka gaisa, sannan ya isa kusa da Heedayah yace “Me ya kai ki wajen wanke wanke har kika fadi?” Heedayah na kallon inda ta ji muryar tace 

“Ita ce ta kai ni wajen tace sai inyi wanke wanke” Sudais yace “To ina ke maki ciwo yanxu?” Kafarta na hagu ta nuna masa tace “But…” Yace “But 

what?” A hankali tace “Don’t touch it” kallonsu kawai Junaid yake yi, Sudais ya duka yana kallon kafar sosai yace “Ohkk…” Hannu ta kai tana 

laluba wajen don taga ta inda yake, ta ta6a kirjinsa, shi dai kallonta kawai yake, Bude 32 set of white teeth dinta tayi tace “Wannan sweet din 

naka ya kare ko?” Ya buda ido yace “Kina so ne?” Ta gyada masa kai tace “Um” yace “Ohk to bari in kawo maki” tace “Har da short bread??” Juyawa 

Junaid yyi ya fita daga dakin ya rufe kofar, Sudais ya kalli kofar sannan ya kalleta yace “Who is he?” Ta d’an yi shiru sannan tace “Shine ya bar 

ni a middle of road wai in wuce cikin gida da kai na bayan yasan bana gani, I don’t like him” da mamaki Sudais yace “A ina kenan?” Tace “A gidansu 

mana, kuma ina shan strawberry ya dauke min plate din, wai baya son in sha…” Tana fadin haka ta turo baki, Murmushi Sudais yyi ya mike yace “Toh 

bari in kawo maki sweet din in dawo” ta kara bude hakoranta tace “Toh” ya isa kofar ya bude ya fita, xaune ya tadda Junaid a parlor tare da kaka, 

kaka na nuna sa tace “To ka gansa, sai dai idan ban ajiye abu ba wllh, shi kuma wancan axxalumin ko magana baya wani yi, sae dai yyi ta kallon ka 

yana fama da mugun abu a xuciya, shureen naji suna kiransa ko wa, shi ma dai Aliyun ne, amma gaskiya xan gaya maka xuciyarsa bbu kyau yau na sake 

gaskata hakan daxu, to dai duk sunan Mai gidana ne da yayi hatsari ya rasu” ko kallonta Sudais bai yi ba ya nufi kofa xai fita, kaka tace “Kuma 

wannan da kake gani yan matansa sun kusa dozin har na gaji da xuwan da suke gaisheni, yau fara ta xo, gobe baka, jibi mummuna, kai gasu nan dai, ni 

dai na gaya ma daya a ciki yaudaran ta kawai yake, to ita ce ta goma xuwa gaisheni, to naga tana da hankali tana ta min aiki da goge goge” Sudais 

ya mata wani kallo ya fita ya kulle kofar. Junaid ya d’an yi murmushi yace “To ni xan koma…” Kaka tace “Da wuri haka har ina murna na samu abokin 

hira?” Yace “Xan dawo da daddare” tace “Ahh to shikenan, in ajiye maka abinci kenan?” Wani murmushin da ya bayyana dimples dinsa yyi yace “Toh sai 

na xo in sha Allah” tace “Toh Allah ya kawo ka, amma kaddai ka ki xuwa ka bar min abincina yyi kwantai” yace “A’a xan xo” mikewa yyi tace “Toh ka 

leka ko ta tashi yarinyar” yace “Toh” daga haka ya shiga dakin, xaune ya same Heedayah, ya karasa kusa da ita ya kai hannu ya dunguri forehead 

dinta yace “Kina ji ina maki magana kika min shiru daxu koh” turo baki tayi bata ce komai ba, yace “Sai na yanke wannan bakin” Tana jin haka ta 

6ata fuska lkci daya ta fara Shesshekar kuka, xaro ido yyi ya xauna gefenta ya jawota jikinsa yace “Ke wasa nake maki fa” Cikin rawar murya tace 

“Toh shine xaka ce xaka cire min baki?” Yace “A’a baxan cire ba, sorry” tace “Toh ina Farida?” Yana kallon Eye balls dinta yace “Ta je Abuja” da 

sauri ta dago kai tace “Nan ne garinmu mu ma ai”  Yana kallonta yace “Where in Abuja?” ta bude hannu alamar bata sani ba, sai kuma tace “Yaushe 

xata dawo?” Yace “Soon” saketa yyi ya mike yace “I’m going” tace “To ni baxan sake xuwa wajen Mami ba kuma, ni ina tsoron wannan matar” Junaid ya 

buda ido yace “Me yasa” ta marairaice tace “Tana ma kowa masifa, kuma tana aikana bana ganin hanya” Murmushi yyi sosai yace “Mami xata xo ta tafi 

da ke” Shiru tayi bata ce komai ba, yace “Anjima xan xo da daddare” ta gyada masa kai alamar to, sannan ya juya ya fita dakin. Da daddare Junaid ya 

xo gidan Baffa kamar yanda yyi ma kaka alkawari, Kaka na can uwar daka, Heedayah kuma na xaune parlon da plate din tuwo a gabanta, Da sauri kaka ta 

fito jin an bude kofa, ganin Junaid ta washe baki tace “Ka zo ashe Junaidu” gaisheta yyi ta amsa tana washe baki tace “Bari in gama gyaran gadon in 

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button