NOVELSUncategorized
DOCTOR NA’IM 4

Page 4⃣
Mummy sakeena tayi mata wani irin kallo kafun tace, ke nifa kinsan bana ciki d shirme. Yanda kk tsoron naim dinnan ko ubankineshi sai hk, siyama ki fadamun gsky ko dae kinasonshi ne?
Tayi saurin girgixa kae aa mum wllh ni Sam bana sonshi shi kanshi yasan ni ba ajinshi bace. Kawai dai kinsan halinshi bashi da wasa ne. Ni kuma ina tsoron karya duk wata dokar daya shinfida a gidannan
Mummy sakeena taja tsaki ta mike ta shige bedroom dinta
A xahirin gsky siyama idan tace bata son na’im to tayi karya. Saboda ita ganin ta ko don kyaunshi ya cancanci asoshi, balle kuma idan akayi duba da wasu qualities d yk dashi Wanda ba duk maxa ba. Sannan yasan kanshi sosae. Yana d ajin da ko ita kanta da take mace kuma take takama d kyau baxata nuna mishi ba.
Abu daya Allah y rageshi dashi shine kudi, Sam bashi d kudinda xata shiga a dama d ita cikin manyan mata bayan auransu.
Ta dago kanta tana kallon sunan doctor AA, inama Allah xai bata miji mai kudi hk irin Dr AA, data aureshi komai kiyayyar dayake mata xata jure
Mum ta mika mata Leda viva tace anshi ni shashasha kawai kina nan kina t saka shirme. Kice mata sauran bayanin sai munyi waya
Ta falon gidan ta biyo cikin takuntana isa d kasaita. Neehal ce da maryam kadae a falon suna ta shirmen gabatar d program, a wayar Abbas suke dauka
Neehal tana ganinta tace aa yan mata ina xuwa?
Ta dan yamutsa fuska wllh mum ce ta aikeni gidansu muslihu. Raihan ta dago ta kalleta, oooh ynx ai n gane kan xancan shiyasa bakinki yaki rufuwa Ashe gidansu masoyinta xata. Siyama ta kai mata duka d pillow kefa yar iska ce wai masoyina da sa ranar yaya naim din xan kula wani?
Neehal ta kalli agogo to suda sarkin xance sai ki hanxarta tafiya don ki dawo d wuri kinsan halin yy na’im
Siyama tace wllh kuwa ni dama xaki rakani muje tare
????rufa mun asiri, hk kurum b tambayarshi mukai ba gara make kya fake d aiken ki akayi nikuwa fa? Gashi kwana biyu daman n lura fushi yk dani
Siyama tai murmushi wae gara, ynx dae kunga yafiyata sai n dawo. Dg hk sukayi sllm ta huce
Naim kuwa sosai yk rawar sanyi ta cikin bedsheet har hakoranshi n kaduwa
Da kyar y lallaba y futo y falonshi ya dau paracetamol akan fridge yasha y koma y kwanta
A hnkl xafin jikin nashi yasoma raguwa sai gashi har y iya futowa falonshi y xauna don y samu wani Abu yasa a cikin shi.
Y dauki wayarshi ganin missed call rututu. Tsaki yy yasoma duba num ban wani a cikin kannen nashi
Bashi d num ban kowa cikinsu don hk y futo xuwa saman balcony, yakuwa ci Sa an ganin maryam xata sauka, yace yauwa don Allah ki turo mun neehal
Ta amsa mishi d to sannan t nufi kasan. Suna kitchen ita d raihan ta sanar mata d sakon yy na’im, tayi mmk jin wai yana gida.
A kofar falon ta tsaya ta danyi knocking, dg ciki aka bata ixinin shiga. Karo n farko data taba shiga dakinshi ta murda handle din kofar tare dayin sallama. Yana zaune kasan carpet hannunshi dafe da kanshi idanunshi a rufe. Neehal ta lumshe idonta tana Shakar daddadan kamshin dk manne d dakin. Komai n dakin neat kamar b dakin namiji ba, lallai yayan nata karshe ne
Ta durkusa a gefan shi cikin sanyin murya tace yy gani.
Ya dago d rikitattun idanunshi yana kallon ta, kallon d yake sanyayar d jikinta kallon dayake sanya ta shiga taitayinta kallon d yake sa xuciyarta yin daar
Tayi saurin maida idonta kasa don gujewa wannan kallon nashi. Y sauke sassanyar ajiyar xuciya kafun yasoma mgn neehal yunwa nakeji ki samomun wani Abu a cikin abincin da kk San ina ci tun kafun ulcer ta illatani. Yanayin da yy mgnr y bata tausayi ainun, ta mike jikinta a sanyaye ta fuce don hada mishi abinda y umarceta
Few minute t dawo d tray a hannunta ta dora saman dan karamin centre table din dk gabanshi, da kanta t hada mishi komai ta ajiye mishi a gabanshi. Y dago yana kallon ta ngd sist.
Tayi mishi murmushi kawai t juya xata futa y kirawo sunan ta bata juyo ba tadai tsaya. Kina tafiya bazan ciba, sai kawai t juyo ta dawo t zauna gefan shi duk a darare take t kagu y sallameta.
Yana cin abincin ammn idonshi n kanta ita kuwa ta kasa dagowa sai wasa tk d zara zaran yatsun Wanda su kasha ado da Jan lalle.
Kafun y Ankara har ya kusa cinye abincin duk d bawani dadin abincin yk jiba kawai turawa yakeyi
Bayan y kammala ta karaso gabanshi t durkusa tana har hada kayan Sam taki yadda su hada ido
Caraf y ruko hannunta ta dago ba shiri tana kallonshi. Shima ita yk kallo eyeball to eyeball
Ku gafarceni ma karanta mu hadu a next page wani Abu ( neehal d naim uwarsu daya ubansu daya ) xamuji mafarin lbrn insha Allah
Taku har kullum
Mariyatu lawal mhmmd