NOVELSUncategorized

DOCTOR NA’IM 6

Page 6
Family koki family ne Wanda suka shahara ta bangaren ilimin addini. Kusan daukacin iyalan wannan gida mahaddata alkur ani ne.

A tsarinsu Sam b batun boko, ammn ynx d yk abin yazo d zamanie dole alhaji ibraheem yabar yayan shi maza suyi karatun. Alhaji Ibrahim shine babba a gidansu, sai kuwa kaninshi Abubakar Wanda su kadai iyayansu suka haifa. Ba shahararrun masu kudi bane ammn suna d rufin asiri dai dai gwargwado. Alhaji Ibrahim yayi auran shi n fari kafun dg baya kuma ya karo wani auran. Hadizatou itace uwar gida sai rafi ah kuma itace amaryah. Rayuwar gidan rayuwace wadda aka shinfidata bisa tsari irin n addinin islama, kasancewar me gidan ma abocin ilimin addini ne. Hadizatou ita ta haifa mishi yaya takwas ammn biyu sai rasu sai shida a cikin yayan nata akwai. Ibrahim shine babba Wanda yaci sunan mahaifinshi ( abbansu saleem kenan) sai Ahmad  ( mahaifinsu na’im kenan). Mukhtar shine n uku Wanda y xamo shine mahaifinsu abbas
        Auwal kuma shine n hudunsu. Yayanta mata biyu, maryam d surayya.
    Wannan kenan, bangaren rafi ah kuwa yayanta hudu, uku maxa mace daya. Akwai usman, aliyu d kuma nazifi sai macenta daya rahama
      Duk yayan gidan Kansu a hade yk. Bazaka taba banbance yan can dakin ko yan nan ba, komansu tare suke gwanin burgewa.
        Kasancewar zamany y ci gaba su b iya ilimin addini kadai suka tsaya b sun hada dana boko. Ibrahim yayi karatun shine a bangaran kasuwanci yayinda Ahmad kuma yy nashi a bangaran likitanci. Sauran kuma duk professors ne d yan kasuwa. Ibrahim yy auran shine anan garin katsina kuma dai dai gwargwado yana d rufin asirinshi bawai kudi ainun dinnan ba. Ibrahim yaso hada Ahmad  auran xumumchi d yar kaninshi sai dai kash ko lokacin yaxo d maganar ni’imatullah.
      Ni ima yar asalin garin kano ce. Sun hadu ne sanadiyyar wata rana data rasa mota gashi anyi ruwa, ta dawo dg makaranta aikin jinya sanye d farin uniform irin na likitoci
        Dg taimako soyayyah mai karfi t shiga tsakaninsu. Ahmad Sam bai dogara d aikin likitancin dy ke ba yafi maida hankalinshi akan bangaranshi n kasuwanci. Dg karshe ma y hakura d aikin gaba daya y jirkita ban garan dayafi kwarewa. Kusan b mazauni bane yau yana wancan kasa gobe yana waccan yayi kudi sosai t yadda har ta n kewaye dashi suna hutawa.
Toh d farko mahaifinshi y nuna sam bai yadda d auran shi d ni ima b, ammn dg karshe d mahaifiyarshi ta zauna tayi mishi gamsashshen bayani sai y amince
       Bayan auransu a garin kano y ajiye ta, yakan xo duba mahaifanshi d yan uwanshi lokaci bayan lokaci
   Ni ima taci gaba d karatun ta n likitanci d taimakon Allah d taimakon Ahmad. Cikin ikon Allah t karasa karatun ta ta xama cikakkiyar likita
Ni ima mace ce mai hakuri g taimako hk xalika tana d matukar tausayi. Marainiya babanta y rasu tun suna yan yaara don hk suka taso karkashin kulawar amminsu, su uku ne a gurin iyayensu itace babba sai kanwarta sumayya da kuma kaninsu sadik.
Ahmad mutum ne dayake dason yara gashi ynx kusan shekararsu nawa d aure tare d ni imarshi ammn har ynx haihuwar ta shiru. Hkn b karamin dg mata hnkl yayi b, ganin hkn yasa shi y boye tashi damuwar don kwantar mata d hnkl. Ni ima tasha shawartar Ahmad d ya karo aure tunda ita har ynx bata haihuba, ammn sai ya nuna mata shi Sam baya so. Ana hk matar Ibrahim t haihu, murna a gurin ni ima ba a cewa komai koda taje ganin baby sai d tayita kuka tace don Allah ta batashi. Fa’iza kuwa tayi mata alkawarin indai t yy shi xata bar matashi kyauta. Ranar suna yaro yaci sunan saleem
Watanni kadan d haihuwar saleem kakansu ibraheem y kwanta ciwon ajali. Hakika rasuwar alhj Ibrahim t gigita hnklin daukacin iyalin dk cikin family koki. Tun dg nan kuma Ibrahim y xamo shine kamar uba g iyalin duk wani taro d komai a gidan shi akeyi duk da ba wani kudi ne dashiba.
   Muktar ma ya samu matarshi Fatima sunyi aure. Ana hk kuma ni imatullah ta fara rashin lfy, wanda ita kanta batasan abinda yk damuntaba. Ahmad y futa d ita dubai don a duba lfyr ta, anan ne likitoci suka samu damar gano cikin dk jikinta wanda yy wata shida b tare da ita kanta tasan dashi b, murna a gurin Ahmad ba a cewa komai
Watanni kadan kuwa t haifi santalelen danta me kama da ita sak hatta farar fatar kuwa. Ahmad yy alkawarin muddin ta haifi mace to sunan ta zaisa sai gashi kuma ta haifi mace duk d hk sai daya sanyawa yaron sunan na’im. Kamar yadda fa iza tayi alkawari kuwa hk tana yaye saleem ta barwa ni ima shi
    Ni ima b yan uwantaba hatta patients dinta suna jin dadin xama d ita Ahmad yaso iyayen nashi su dawo gurin shi d zama sai dai Sam sunce baxasu dawo gidan surukai ba abin kunya m kenan
     Shekarar ni ima bakwai d haihuwar na’im ta samu wani cikin murna ba a cewa komai. Xuwa lokacin na’im d saleem sun soma nisa a karatun d sukeyi n Arabic a tsarin iyayen biyu basa son karatun boko mai xurfi
Cikinta n shiga wata n bakwai suka rankaya dukansu suka tafi england a cewarsu sai ta haihu xasu dawo. Sai dai wani abu y kawo musu tsaiko Wanda ko bayan data haihu baxata samu damar dawowa gida Nigeria b sai nan d kusan shekara daya. Ahmad y dawo dasu naim Nigeria gudun kada karatun su y tsaya, a gurin ammi aka barsu yayinda ita kuma ta zauna a england d kyakywar diyarta wadda taci sunanta wato ni imatullah ammn suna kiranta d sunan neehal
Cikin shekaru uku rayuwa tayi musu dadi d rashin dd. An samu mummunan sabani tsakanin hadizatou d abokiyar xamanta Wanda hkn y kawo rarrabuwar kawuna 
      Kowa y kama nashi guri a tsakanin yayan gidan. Ahmad y siyawa Ummn su gida anan kusa d Ibrahim  tana zaune y kara kaita makka a karo n kusan Biyar kenan
A cikin shekararda naim suke gab d kammala Junior a makarantarsu t qur anic memorization a wannan lokaci ni ima ta kwanta ciwo.
      Wanda tasha fadawa Ahmad a duk lokacin dayazo asibitin cewa mutuwa zatayi y gafarta mata.
     Ahmad yakan shiga tashin hnkl a duk lokacin dayaji furucin matarshi gareshi sai dai shima yana nuna mata muddin ta mutu to shima y mutu b abinda ya rage masa a fadin duniya don hk bb abinda xai zauna yy
A ranar wata juma ah ranar d daukacin family koki vaxasu taba mantawa d ita b ranar data xamo silar rugujewar duk wani farin ciki nasu domin kuwa a ranar ne ni ima ta amsa kiran mahalicci. Akan idon Ahmad ni ima ta daina numfashi. A take anan shima y yanke jiki y fadi sai gawarshi aka daga
      Allahu akhbar rayuwa naim hauka ne kawai baiyiba. Kusan yadda t shagwabashi komai ita takeyi mishi hatta abinci wani lokacin ita take xama d kanta tayi ta basu a baki har sai sun koshi, naim d saleem dukansu sun shiga rudanin rayuwa. Tun dg rasuwar iyayenshi naim y tabbatar y rasa farin cikin shi kenan har abada
Allahu akhbar rayuwa
D hk n kawo karshen wannan page din mu hadu a next page inda xamuji ci gaba d yardar Allah
Taku har kullum Mariyat lawal Muhammad ( mommy)
????????jin jina ta musammn g aminiyar kwarai haleema yazeed labo

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button