Uncategorized

HEEDAYAH 7

 

7……

Sudais na tsaye compound din gidan nasu Abba ya fito rike da hannun Heedayah, Sudais ya nufe sa ya gaishesa da ladabi, Abba yace “Lafiya Aliyu, ya 

weekend?” Sudais yace “Alhmdllh sir….” Yana kallon Heedayah ya kai hannu kanta yace “How are you?” Shiru tayi bata ce komai ba, Abba yace “Talk 

to him Heedayah” tana rike da hannun Abba a hankali tace “I am fine” Sudais ya mata murmushi yace “Good girl….” ya kalli Abba yace “Allah ya 

bayyana iyayenta” Abba yace “Ameen My son” jin taku a bayansu Sudais ya juya, Shuraim ne ke tahowa yana tafiyar kamar bai son yi, wani kallo Abba 

yyi masa ya kalli Shuraim yace “Xan wuce gida ynxu, anjima ka taho can gidan ka sameni” Sudais yace “In sha Allah….” Daga haka Abba ya bar wajen 

xuwa gun motarsa tare da Heedayah, Sudais na kallon Shuraim da ya bi Abbansa da ido yace “Kai ma baka bada goyon bayan taimakon yarinyar da Abba ke 

son yi ba kenan, coz naga kallon da ya maka” Shuraim ya bude hannu yace “But…. She’s blind, ta ina xa a fara kula da ita, is it even 

possible….” Sake baki Sudais yyi yana kallonsa a bit shock, can ya juya da sauri ya kalli parking space yaga Abba is helping her Into the car, ya 

kara kallon Shuraim yace “Blind? How is that?? Who told you that, ban gane ba” Shuraim ya shafa kansa yace “Yes makauniya ce…” Yana fadin haka ya 

juya ya koma ciki ya bar Sudais a wajen baki bude, Sudais ya kara satan kallon motar Abba har ya fita compound din…. A hankali Abba ke driving 

yana yi yana waigen Heedayah dake shan yoghurt da ya siya mata, muryar ta ya ji tace “Abba gida xa mu je ynxu wajen Ammina?” Ya gyada mata kai 

kamar tana ganinsa yace “In sha Allah” wani babban eatery ya shiga yyi parking yana kallon agogon wrist dinsa da ke nuna karfe sha biyu saura, 

wayarsa ya dauka yyi dialing number ya kai kunne, bayan few seconds yace “Hope you aren’t going to keep me waiting Barrister” bin motar da ya shigo 

eatery din a dai dai lkcn yyi da kallo sannan ya katse wayar, Heedayah tace “Abba mun kai gida?” Ya shafa kanta yace “A’a, I want to see a frnd 

now, xa ki jirani har in dawo koh?” Ta gyada masa kai a hankali, kamo hannunta yyi yana murmushi ganin she looks sad and insecure, kamar dai tafiya 

xai yi ya barta din nan, mika mata wayarsa yyi yace “Ki rike min wayata har in dawo ynxu, kin ji?” Ta kara gyada masa kai, ya bude motar ya sauka 

sannan ya rufe ya nufi entrance din eatery din, Table din dake dauke da wata mata that is in her early fifty ya nufa, kana ganinta kaga well 

educated bafillatana cikin shiga ta kamala, ya ja kujera ya xauna yace “Good morning Barrister” Ta ajiye wayar hannunta da take operating tana 

kallonsa ta cikin siririn glass din idonta tace “Morning, ya family, ya weekend?” ya gyada kai yace “Alhmdllh mun gode Allah” tace “Hope ba aiki 

xaka hadani da shi ba kace xaka yi tafiya, coz nima tafiyan xanyi gobe in sha Allah” yayi ‘yar dariya yace “Not at all, how are the children?” Tace 

“They are all alhmdllh, ya su Rabi’ah?” yace “Lfya lau” tace “Toh Maa sha Allah” shiru ne ya biyo baya, bayan few seconds ya kalleta yace “Ba aiki 

xan baki ba, na dai xo maki da magana mai muhimmanci ne Hajiya Rahinah…” kallonsa tayi ita ma tace “Ohk Am all ears in sha Allah barrister, Allah 

kuma yasa dai lafiya” yace “Sai alkhairi, Hajiya Rahinah na gayyatoki nan ne…. To ask for ur hand in marriage” Da wani irin mamaki take kallonsa 

wanda hakan bai bata damar iya ce masa komai ba, yyi kasa da murya yace “Yes nasan xa ki yi mamaki but ba abun mamaki bane, I want to marry you…” 

Ta yi wani yake tace “Haba Barrister, do you even know what u are saying, ni ynxu auren me xan kuma yi? Me nake nema a rayuwa….” Ya katse ta yace 

“Aure shine rufin asirinki let me tell you idan baki sani ba, idan kika yi aure kimarki da darajar ki xai fi haka a gun jama’ah, I have known you 

for more than 15 years now tun mijin ki na da rai….” Bude handbag dinta tayi ta ciro tissue don nan da nan har hawaye ya kawo idonta, ya girgixa 

kai yace “I don’t mean to hurt you ko in fama maki ciwon xuciyar ki Rahinah, kar ki manta tun ba yanxu ba na sha baki shawaran kiyi aure sai ki ce 

min sai kinyi shawara, to yanxu na yanke shawarar auren ki for 3 reasons, which I will let you know ko ba yanxu ba” tace “I am sorry Ahmad bana 

tunanin xan yi aure har karshen rayuwata, rabuwan tashin hankali nayi da mijina ba wai normal rabuwa, bana da ra’ayin aure har abada” ya katse ta 

ya d’an buga table din gabansu yace “Stop this nonsense Rahinah…” A d’an fusace tace “In koma gida ince ma yarana xan yi aure? Me ye nake nema a 

duniya a yanxu? Me yarana suka rage ni da shi da xai sa inji ina sha’awar yin aure? Plss come off this barrister” Ya lumshe ido ya bude yace “Noo 

Rahinah, ba don kin rasa komai xaki yi aure ba sai don auren shine suturar ya mace….” Tana goge hawayen idonta tace “Idan ma sbda tafiye tafiyen 

da nake yi ne ko sbda Aikina ni naji xan ajiye in xauna gidana dama Junaid ya fi son haka, tun ba yau ba yake son in daina aikina coz ban rasa 

komai daga garesu ba, ni kuma xaman kadaici ne dama bana so” Kallonta kawai yake, ya sauke boyayyen ajiyar xuciya yace “I’m sorry I am making you 

cry this much, I’m sorry Rahinah” tayi murmushin karfin hali tace “It’s okay….” A hankali yace “Xa mu ci gaba da magana amma ba ynxu ba, it’s 

almost time for zuhur, but….” Jin yyi shiru ta kallesa tace “But?” Ya sakar mata murmushi yace “Ban hakura ba, anyway that aside xan baki yarinya 

ki tafi da ita, for now marainiya ce bata da kowa….” Da mamaki take kallonsa tace “Ban gane ba, a ina ka samo ta…” Briefly ya 6ata labarin 

Heedayah, wanda hakan yasa jikinta yyi sanyi tace “Allah sarki, Allah ya bayyana iyayenta, I will go with her in sha Allah” yace “Yes I know u will 

Rahinah, sai dai I didn’t made mention of her blindness to you, she’s blind” xaro ido tayi tace “Blind??” A hankali ya gyada mata kai, tace 

“Innalillahi wa Inna ilaihi raji’un” yace “Tana mota ita kadai, mu tafi ki ganta” a tare suka fita eatery din, sai da suka kusa motarsa a hankali 

tace “Matar ka tace baxata riketa ba kenan?” Ya juya ya kalleta ya d’an yi murmushi yace “Ehh” Ta girgixa kai tace “Toh Allah ya kyauta” yace 

“Ameen, amma a gidana Heedayah xata xauna, she will stay with u just for few days let me settle down things” Bude mota yyi Heedayah ta juya 

direction din da sauri fuskarta duk hawaye tace “Abba” ya kamo hannunta yace “Kuka kike yi daughter” cikin rawar murya tace “Naga baka dawo ba” ya 

share mata ido yace “I’m back dear, xaki bi Maminki gida yanxu kin ji?” Tace “Abba ina xaka je?” Yace “Xan je in siyo maki sabbin kaya ko baki so” 

tayi shiru bata ce komai ba, Hajiya Rahinah dake ta kallon Heedayah da tausayi tace “Ba dadewa xai yi ba baby, mu je gida kafin ya kawo maki kayan” 

daga haka ta sauketa a motar, ya kalleta yana murmushi yace “Thanks Barrister, sai na xo anjima” ta gyada masa kai ta nufi motarta da Heedayah, sai 

da ya ga fitansu sannan ya ja motarsa ya bar Haraban eatery din shi ma. Hajiya Rahinah na parking a parking space ta bude motar ta fito, wata 

yarinya da baxata haura sha hudu ba ta iso gun motar tace “Mami sannu da dawowa” Tana mika mata handbag dinta tace “Thanks dear, har kin gama 

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button