FATU A BIRNI COMPLETE HAUSA NOVEL

Na Mrs Aslam Haidar✍
0⃣1⃣
CIKIN TASHA:
Mutanen dake fitowa daga cikin bus din ne na hango wata matashiyar budurwa, wacce inka lura da yadda take waige waige tana zare idanu zaka tabbatar yaune farkon shigowanta garin Gombe, “Gombawa diban fari, ba’a kwana daku ba an tashi daku”???? Itama FATU haka ya ksance da ita don ynxu misalin karfe 7:20 na safe. Matsawa gefe tayi ta tsaya inda bbu mutane sosai ta cigaba da dube dubenta. Can nesa ta hango wata mai sayar da kosai da dankali a cikin tashan. Nufanta tayi da sauri cikinta na bada wani sauti qululululu don rabon da taci abinci tun jiya da rana sai fura kadan da kakanta ya bata da dare. Sauri take yi har ta isa, sallama tayiwa mata mai sayar da kosai, matar ta amsa, fatu tace a bata kosai da dankali na dari, matar ta sa mata a leda ta miqa mata, kudi ta ciro 500 daga cikin jakarta ta miqawa matar, aka bata canji, gurin wasu yara masu sayarda pure water taje gefe kadan da mai sayar da kosan. Ta sayi guda biu. Anan ta fara tunanin a ina zata zauna taci, don har masu shaguna sun fara budewa. Bakin wani shago taje inda bbu mutane ta zauna, juya baya tayi yanda baxa a ganta ba ta fara cin kosan tana korawa da pure water. Sauri sauri har ta gama. Alhamdulillah ta furta, sannan ta wanke hannunta ta goge bakinta da zumbulelen hijabinta. Minti biyu da haka ta miqe hade da karkade jikinta ta dauki jakanta ta rataya ta cikin hijabi. Wajen tashar ta fito tana tunani barkatai a cikin zuciyarta. Kuuuuuuuuuuu sai timm. Innalillahi abunta matar dake cikin motar ta fada cikin kidimewa. Kafin ta fito har an fara taruwa akan fatu, tana fitowa tayi kan yarinyar da saurinta tana su taimaka mata su saka ta cikin motar ta. Wasu mata yan sharan titi ne suka taimaka mata suka sata a mota yayin da matar ta shiga driver seat ta cilla kan titi sai hospital.
[2:25PM, 5/4/2016] Mum Fateey: ????????????????????????????????????????????
????????????FATU A BIRNI???????? ????????????????????????????????????????????
Na Mrs Aslam Haidar✍
0⃣2⃣
Hospital:
Tana isa asibiti ta shiga sai gata ta fito da nurses biu hade da gadon tura mara lafiya. Suka ciccibi fatu suka daura akan gadon sukayi ciki da ita cikin sauri. Emergency aka shigar da ita, bayan 15 minutes wata doctor ta fito da sauri matar ta tare ta, tace “ya patient din? Doc tace “da sauqi don bata buge sosai ba, tsoritan da tayi ne yasa ta suma, sai kurjewa da tayi a kafa. Ynxu za’a kaita dakin hutawa zata farka nan da 4-5 hours. Don tana bukatar hutu. Tana gama fadan hka tayi gaba abinta yyinta wata nurse da gangaro fatu a kan gadon marasa lfyn ta kaita dakin hutu matar ba biye da ita. Ta kai minti biu tsaye a kanta sannan ta juya ta koma mota, yaronta dan kimanin 7 yrs yace ‘mum ina wanda kika bugen? Sai a sannan ta tuna ashe tare suke, school zata kaishi da yake yau monday tana sauri kar y makara, shine hatsarin ya faru. Shafa kanshi tayi tace ‘farouq tana ciki an bata gado, muje in kaika school.
Acan school tayiwa teachers bayanin abunda ya faru don yara sun dde da shiga class. Komawa gida tayi wanda a lokacin 9 da yan mintuna. Ta samu dija mai aiki tana goge a palour, ‘sannu da dawowa hajia’ hajia ta amsa tace ‘kiyi abinci da mutum 1 za’a kai asibiti, na buge wata yarinya a hanya. Bata farfado ba balle in san gidansu, na duba jakanta banga tana da phone ba ko ID card. Cikin jimami dija tace “to hajia Allah ya kiyaye na gaba, taji ciwo sosai ne? Hajia ta mata bayanin da Doc ta mata sannan ta haura sama tana tunanin yarinyar game da tambayoyi cike a kanta wanda bbu wanda zai bata amsan sai yarinyar. Don daga ganin shigar da tayi zaka gane yar kauye ce, amma cikin jakarta kudi dari biyar biyar sabbi wanda yawansu zai kai 25k, kuma jakan nata irin na yara masu zuwa makaranta ne, sai kaya kala uku. Ni kaina mmn Fa’iz sai da zare????. Duk answers na gurin fatu wacce har ynxu tana gadon asibiti bata san duniyar da take cikiba.
Taku Maman Fa’iz????
[11:44AM, 5/5/2016] Mum Fateey: ????????????????????????????????????????????
????????????FATU A BIRNI???????? ????????????????????????????????????????????
Na Mrs Aslam Haidar✍
0⃣3⃣
Fatu bata farka sai 12:23. A hankali take bude idonta har ta fara gani rass. Juyo da kanta tayi gefe inda taji muryan mace na mata sannu, kyakkyawar mata ce mai dan jiki kadan wanda da alama ta danbmanyanta, “Ya jiki ta qara cewa da fatu, a hankali ta furta da sauqi. Sannan ta fara qoqarin tashi, matar tayi hanxarin taimaka mata ta zauna. Tace “ki dan huta sai kici abinci. Bari in hada miki tea. Tea ta hada mata mai kauri tasha kadan tayi hamdala. Sannan matar tace meye sunanki, kuma a ina iyayenki suke? “Suna na fateema ana cemin fatu, dangina suna kauye mai suna Garin Modibbo dake karkashin qaramar hukumar Akko. Matar tace “sunana hajia kulsum, nice na buge ki da mota ina sauri zan kai dana makaranta. Kiyi hakuri. Hope yanxu bakya jin ciwo? Daga kai fatu tayi, hajia kulsum tace “gurin wa kika zo nan garin? Ina son in kaiki in bada hakuri. Saurin girgiza kai tayi kanta na qasa tace “a’a hajia hakama ya isa, ba sai kinje ba, nagode. Hajia kulsum ta tashi ta deba mata abinci da kyar fatu taci rabin plate tace ta koshi tasha ruwa. Hajia na lura da yanayinta, yarinyar tana cikin damuwa. “Hajia ina son zuwa bandaki” hajia kulsum ta taimaka mata taje bandaki, kama ruwa tayi sannan tayi alwala ta fito. Zama ta qara yi a kan gadon, shiru sukayi na dan lokaci sannan aka fara kiraye kirayen sallah. Sukayi sallah, sannan Doc ta shigo ta duba fatu, ta mata questions game da yadda take ji. Doc ta juya gurin hajia kulsum tace “zaku iya tafiya gida, shes gud now” ta fita. Hajia ta fita taje ta biya kudi ta dawo tace mu tafi. Sun fito harabar hospital dinne fatu tace “hajia ko kun tsinci jakata” hajia tace “eehh, yana gidana manta wa nayi ban dauko miki ba. Amma muje sai ki karba. Mota suka shiga suka tafi. Unguwar GRA suka shiga, ita dai fatu in banda kalle kalle bbu abunda takeyi, wani layi suka shiga wanda yafi ko ina haduwa don gidaje 20 suna kallon juna sai titi a shimfide a tsakiyarsu. Gaskiya fadin tsaruwar houses din ma bata lokaci ne. Nidai mmn fa’iz nace kamar a turai. Fatu kuma tace Aljannar duniya. A cikin jerin gidajen wata mota hadaddiya ta fito ta hau kan titi, hakan yyi daidai da juyowar fatu wacce take kalle kalle tun shigar ta unguwar mutumin da ta gani a cikin motar shiya sata daskarewa, bakinta a bude tana nuna shi da yatsa, har yazo ya wuce baima san tanayi ba don waya ma yakeyi yana murmushi. Horn hajia tayi a bakin gate din gidanta wanda yake kallon gidan da mutumin ya fito. Aka wangale gate ta kusa hancin motar har ta samu parking space tayi. Sai a sannan ta lura da fatu wacce idanunta na tsiyayar hawaye tana nuna glass da yatsa, fatu” ta kira sunanta amma bata amsa ba, dafa kafadarta tayi ta juyo a firgice sannan ta fashe da matsanancin kuka wanda yasa hajia cikin wasi wasi. Anya yarinyar nan ba aljanu gareta ba? Ace yarinya da ita ta fito daga garinsu ba kowa tare da ita, kuma ba’a mata komai ba tana kuka tana nuna glass. Whats wrong with her? Kodai auren dole za’a mata ta gudu? Ko ko ko?