Hadiza GabonKannywoodLabaraiMatashi

Amsar Da Hadiza Gabon Ta Bawa Wani Matashi Daya Zage Ta Yadau Hankulan Mutane A Shafin Twitter

Wani Bawan Allah Ya Yi Wa Jarumar Kannywood Hadiza Gabon Zagin Rashin Mutunci Inda Ya Kira Ta Da Karuwa Duk Don Ta Ƙi Amsar Shi A Saƙon Da Ya Tura Mata A Twitter.

A ranar 14 ga watan Janairu ne wani ma’abocin amffani da kafar sada zumunta ta Twitter mai suna Ahmad Babayo ya yi wa jaruma Hadiza Gabon zagin cin mutunci ta sashin sakon ta, ya kuma ce mata ta tura wa abokan sana’ar ta su ga irin cin mutuncin da yayi mata.

Ahmad Babayo ya zundumawa Gabon zagi inda ya kira ta da lalatatta, wacce ake zina da ita, mara mutunci kuma kowa ya san karuwa ce.

Sai dai Hadiza Gabon ta bada mamaki saboda irin addu’ar da ta yi masa na samun salama da soyayya a rayuwarsa duk da cin mutunci da yayi mata.

Kamar yadda aka gani, Ahmad Babayo ya bukaci Hadiza ta karbe shi a cikin abokan ta na Twitter, ko ta bi shi a shafinsa amma hakan ba ta yuwu ba.

Bawan Allah ya yi wa Hadiza Gabon zagin cin mutunci, ta yi masa martani da kyakyawar addu’a. Hoto daga @adizatouGabon.

Kamar yadda yace, ita ta fara bin sa a shafinsa na Facebook wanda ake kyautata zaton shafin bogin ta ne ya bibiye shi. A zatonsa ita ce kuma zai samu sakin fuska a Twitter kamar yadda ya ke samu a Facebook, sai ya ga kamar wulakanci ta yi masa a Twitter.

Idan kuka duba hoton Babayo, ba karamin yaro ba ne amma zagin da ya yi wa Hadiza irin wanda ko yaro ne ya yi wa dan’uwansa, dole ne a tuhumi tarbiyyarsa.

Sai dai kuma, yadda jarumar ta kwantar da hankalin ta tare da yi masa addu’a, ya dauka hankalin jama’a masu tarin yawa kuma hakan ya ja aka dinga yin tir da al’amarinsa.

               

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button