Ni da Dr. Sadeeq

NI DA DR. SADEEQ Book 1, page 15-16

🅿️15&16

……suna isowa asibitin Aysha tace”.nawane kud’in ka mlm?”200 ne ranki yadad’e”yafad’a yana kallon ta”d’aure fuska tayi ta fito……hakan kuma yayi daidai da motar dr sadeeq ta iso wajen”yana k’ok’arin shiga cikin get d’in asibitin Aysha data hangosa ta tsaidashi”

tsaki yaja dayaga itace”yakuma k’i tsayawa”gabanta yafad’i”
Amma bata dena tsaida shiba”adaidai bakin k’ofar shiga get d’in yatsaya”hakan kuma yayi daidai da me adaidaita na cewa ranki yadad’e kisallameni natafi mana”

abakin k’ofar motar ta tsaya gabanta nata fad’uwa ta dake ta kallesa”taga yawani had’e rai”kayi hak’uri me adaidaita ne zaka sallama”banganeba?

Turo baki tayi tace”.to sbd karnayi latti nazo a adaidaita mana”

Tsaki yaja yace”.bbu ruwana dashi”bazan bashi ko sisi ba”karki manta jiya kika fara aiki anan”bawani jimawa kikayi ba balle abashi acikin albashin ki”gulmar data saka kika hau masa kaya”sai kisan yadda zaki biyashi”

D’aure fuska tayi tace”.muddin baka biyashi ba nagama aiki anan yasin”

wani banzan kallo yamata yaja motar sa ya wuce”tana k’ok’arin juyawa me gadi dake sauraron su yace”.nawane kud’in?”200 ne baba”zarowa yyi yamik’a mata”ta amsa tana godiya tace aro nayi zan mayar maka insha Allah”

bata jira amsar saba”ta wuce gun me adaidaita”dama bakida
kud’i kika hau?”cewar me adaidaita yana kallon ta”harara ta gallah masa ta mik’a masa kud’in ta wuce”

Tana shigowa ciki tasami office nashi abud’e”bbu ko sallama ta kutsa kanta”

sosai dr sadeeq yayi mamakin rashin kunyar ta”sai wani cin magani takeyi tayi tsaye”

K“zonan!nidai gsky bazan zoba”mena sanar miki jiya?wai dan Allah bakasan sunana bane?”

d’ago kansa yyi suka had’a ido”turo baki tayi ta kauda kanta”koma kiyi sallama”

dan Allah mena maka katsaneni wai?”asibitin ka nazo aiki fa “danna tsayar dakai kabiya me adaidaita shine laifi ?ko cikin albashina saika zare d’arinka biyu ko?amma saika gayan mgn me zafi”mgn me dad’i itama sadakane”akwai hadisin monzon Allah (S A W)daya ke cewa acikin taimaka ma mutum”da dabbarka,koka d’aukesa bisa ita”koka aza kayansa asamanta”shima sadakane”ko kuma mgn me dad’i kayiwa musulmi”shima sadakane”amma shine ni kagayan marar dad’i kak’i kuma biyamun”saidai me gadi yabiya sbd yaji komai”yanzun dan Allah idan sukaje suka bada shaidar bakada kirki fa?”

sosai maganganun yarinyar ke amsa kuwa acikin kunnansa”yatabbatar Aysha nada ilimi na addini ba kad’an ba”

Amma afili sai cewa yayi ke kin isa kigayamun yadda zanyine?”miye damuwarki da abinda zasu fad’a”kud’i bazan biyaba”gobema kikoma hawa”

sannan ki koma kiyi sallama kizo ki gaisheni” ko kuwa nasaka wannan belt d’in jikinki yagaya miki”yatsoratar da ita ,sbd yalura tana tsoron duka”

Dan Allah karka dakeni wlh zanyi”tana fad’in hakan ta juya ta fita”dama dr sadeeq atsaye yake”

gaba d’aya maganganun Aysha sun saka zuciyarsa yin tunani barkatai”

Assalamu Alaikum! tafad’a cikin siririyar muryarta”

wslm yafad’a can k’asa”nayi sallama kak’i ka amsa”ke wai ni sa’an wasankine?”yafad’a cikin cool voice”

Allah yabaka hak’uri”ina kwana?”banza yamata”kaji dan Allah ina kwana??

dama haka aka koyamiki gaida nagaba dake?”batace komaiba ta matso kusa da kujerar sa ta duk’a k’asa tace”.yaya sadeeq ina kwana?

sosai gabansa yafad’i jin ta ambaci sunan sa”amma afili sai cewa yayi niba yayanki bane”kitashi kije kicigaba da aikinki”

sosai ran Aysha yab’aci”tarasa wane irin mutum ne wannan mutum.

Uffan batace ba ta tashi tafara share sharenta”sai kuma yatashi yafita dg office d’in”

Tana gamawa da office d’in ta wuce toilet”tsab ta wanke shi tas”tama lura jiya beyi amfani dashiba”ahakan takoma wankewa”bayan ta idar tana warware hijab nata data d’aure kanta da ita”sbd karta takurata agun wanke bayin”taga kyankyaso……ihu ta saka ta fito aguje”hannunta rik’e da hijab nata”kanta bbu d’an kwali”uban tulin gashinta anade bak’i k’irin…..hakan kuma yayi daidai da shigowar dr sadeeq da dr Abbas dake biye dashi…..

yaya sadeeq!wlh wani kyankyason nakoma gani”tafad’a atsorace zata fita”

Mutuwar tsaye dr abbas yyi yana bin jikin Aysha da kallo”yyinda dr sadeeq ya wani had’e rai sosai”cikin tsawa yace”.dallah ina zakije ahaka kamar sabon kamun hauka?

Ba’a mun wannan gidadancin anan”zaki mayar da hijab naki ko kuwa”jikinta na kirma ta kalli kanta”saima sannan ta lura da yadda ta fito”

Da sauri ta rufe jikinta da hijab nata ta mayar”dr sadeeq yaja tsaki”yyinda dr abbas ya lumshe idanuwansa”yana hango dogon wuyan Aysha da baby face nata”da k’aramin bakinta”

shikuwa dr sadeeq beso dr abbas yaganta ba”sbd yasan mugun halinsa akan mata”(neman mata yakeyi)

Aysha bata wani saurari dr sadeeq ba tafice waje”kan kujera ta zauna tarufe fuskarta taci gaba da kukanta.

murtala nata kallonta da sauran jama’a masu wucewa”da wanda suka zo ganin likita”

Aysha na fita dr Abbas yace”.abokina wacece waccan yarinyar pls?”

kaga mlm miye amfanin tambayar taka akanta?”dan Allah kasanarmun”tab’e baki dr sadeeq yayi yace”.yarinya ce k’arama”amanarta aka bani tanamun goge goge”tama kusa barin asibitin nan”

shiru dr abbas yyi sbd shidai Aysha tamasa”yasan kuma dr sadeeq bazaiso alak’arsuba”gara yabari idan yaganta dg shi sai ita a waje sai suyi mgn”

Da wannan tunanin dr abbas yagama abinda zaiyi yabaro office d’in dr sadeeq”

yana fitowa yakalli Aysha dake zaune tanata kuka”yanaso yamata mgn amma yaga da jama’a”hakan yasa yawuce kawai.

Dr sadeeq kuwa sosai Aysha tabashi haushi”yalura akwai k’uruciya sosai atare da ita.

Jinta shiru bata shigoba”yasaka yakira murtala”kai ina yarinyar nan take?”

gatacan zaune tana kuka”tsaki yaja yace”.cemata nace tazo”dato ya amsa ya ajiye tele phone d’in”

Aysha! d’ago kanta tayi ta wani banka masa harara”yana murmushi yace”.banina nakashe zomon ba”both yace”.kije”

bazanjeba ,saiya saka anfidda kyankyason nan”

murtala beyi mgn ba yad’auki telephone yakira dr sadeeq”y’allabai gatanan tace”.bazata zoba saika saka anfidda kyank…..tsaki yaja ya ajiye talephone d’in”

Tashi tsaye yyi ya jawo wata loka “yazaro belt aciki”d’aure fuska yyi tamkar hadarin gabas yafita dashi ahannunsa”

Aysha najin anbude k’ofar da sauri ta d’ago kanta”idanuwanta suka hasko mata belt d’in dake hannunsa…..zaro ido tayi ta tashi arikice zata gudu…..

Idan kik✍️

mom fareesa🖊️

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button