FITAR RANA 15

Bawai iya nan ne ciwon nata ba,hatta sauyawar halayyar wasime yana daya daga cikin abunda yake tada mata hankli.
Lokacin da anono ta kawo wasimé ko kara kasaka abakinta bazata tauna ba,amma yanzu gabaki daya ta sauya ta dawo wata marar da’a gashi bata son girmama na gaba da ita.
Tasan hala dan bata taba haihuwa ba batasan zafin ɗa ba amma rayuwar taheer da na wasime tamkar wani babban responsibilty ne akanta tunda amana iyayensa suka damka mata,bazata ce tayi nasarar rayuwarta ba inhar ta kyale tarbiyan dayan su ya gurbace.
aynzu kam taheer ya dan girma,tasan ba lallaine ya bata ciwon kai mai yawa ba,duk dama yakan dan taba yarintar,amma aynzu batashi take ba yazame mata dole tasaka ido akan rayuwar wasime,dole ne tasan yadda zatayi ta saita tarbiyanta dan kwata kwata wnn sabbin dabiu da halayyar nata sam basu dace da ita ba.
Tana cikin wannan tunanin wayarta ya soma ringing saheeb tagani akan screen da kamar bazata dauka ba can dai ta hakra ta dauƙa gameda kara wayar a kunne..babu yabo ba fallasa tace “salamu alaikum saheeb? As usual da fararsa ya amsa suka gaisa..kai tsaye ya tambayeta ko zai iya zuwa ya dauƙi wasime izuwa birthday partyn sistersa yau..”tace a’a saheeb kasan dai wasime bata fita acikin gidan nan saida umarnin taheer kuma kaga taher din bayanan kabari mana sai wani lokaci inyaso by then taheer ya dawo amma ynzu kam baya gari.
..,yace eh nasan da hakan shiyasa ma nake neman alfarman ta wajenki dan Allah bilti,namiki alkwarin baxata jima ba zamu dawo,taheer dont even need to knw this, ana yanka cake akayi dan hotona shikenan saina dawo da ita,it wunt take dat long…please kitemaka min . ya karashe maganan cikin magiya..dan shiru bilti tay sabida rashin sanin hukuncin da zata yanke
Wasime ne ta dosu falon
Goye da white teddy bear a gadon bayanta tana tafiya tana wasa da wani abu mai balls balls aciki.
Bilti bilti doramin abuna ya tsinke…
Saheeb yana tsinkayo muryanta yace
‘Is that beauty?bilti bata amsa ba,yace bilti dan Allah hadani da ita..
Mika mata wayar tayi kiyi magana saheeb ne,”da uban zumudi ta amsa taa kara a kunnenta tace “Alo?yeeeeyyy yaa saheeb…dariya yay beauty beauty..beauty na kitayani rokon bilti mana tabari in zo in dauƙeki kije kiga mummy na.
Wani daka tsalle tayi cikin murna tace haba?
Kace Allah zan ganta?
Dariya yay sosai snn yace eh mana amma ai sai bilti ta amince…dan shiru tay tana mai satar kallon biltin da gefen idanunta,gani tay kamar bilti ta hade fuska.
Gaba daya zuciyar bilti bai wani kwanta da abun ba amma dai zata kyalesu din suje kawai da sharadin saheeb zai cika alkwarin sa na dawowa da ita akan kari.
Tunda ta basu go ahead dukansu suke cikin halin murna at arnd 3 na yamma saiga saheeb ya shigo,yau half jumfa yasaka ajikinshi ta masa cas cas dake bugun kamfani ce ya sako hularsa mai shegen tsada. Riga da zani na leshi wasime ta saka sky blue in colour shima duk acikin sabbin dinkunan da akayi mata ne,saheeb yana isowa tay gudu taje ta hau jikinshi tanai mai oyoyo.Duk dama yau bataga wani sakewar fuska awajen bilti ba
Da zasu fita bilti ta kirawo saheeb gefe
“Dan Allah karku dade dayuwar taheer ya dawo yau kuma kasan dai bazaiji dadi ba inyazo ya tarar da cewa bata nan.
Cike da assuring dinta yace insha Allahu zan cika alkwari.
40min drive yakaisu makaken gidan su saheeb ko ina a shirye yake tsaf da kawatattun decorations wanda akayi su musamman don shagalin partyn,kusan rudewa wasime tayi ganin wnn gidan ma yafi wancan wanda sukaje shekaran jiya girma Surutu kam yau yashata harsaida yaji babu dadi.
Everything went well,saidai plan din saheeb na bayyana wasime ma mahaifyarsa bai samu yay aiki akan tsarinsa ba..
muhimman baki ne suka tsareta a babban falon gidansu cikin wata muhimmiyar zantawa ta kasuwanci.,tunda aka yanka cake da ita suka dan daddauki hoto shikenan bata ƙara samun daman lekowa wajen ba,su wasimé kam tuni ta saje cikin yan uwanta yara,saidai kaf cikinsu itace tay daban sabida yanayin suturarsu yasha bambam da nata.
Kusan kowani yaro awajen dan masu shine kuma ancan caɗa ma kowannen su kwalliya da hadaddun ready made gowns nd expensive suits, amma ita kam riga da zani nema ajikinta wanda a kiyasce kudin leshin bazaifi dubu takwas ba.
While da party is going on kowa yanata enjoying kanshi da abinci kala kala ana rawa ana games amma gaba daya hklin saheeb baya jikinshi,baida wani abunyi a zcyarshi face sake sake,And zee was there to annoy him more, dan tunda taga zuwansa wajen tareda wasime take famar tsine masa albarka duk inda ya zauna haka zata bishi ta nanike mishi Snn bata da wani magana mai armashi sai Aibata alakarsa da wasime.
Aranta ta tsane Duk wani abunda ya shafe taheer.
Ayanzu sosai take nuna adawarta da shi.
Da abun ya ishe sa ne yay zciya ya tashi yabar mata wajen yabarta a zaune ita kadai akan table a tsakiyar idanun mutane, Hakan dayay sosai ya bata haushi,aftr like 2 mint tana kkrin latsa wayarta zata turawa kawarta eesha text messg caraf sai idanunta suka sauka akan wasime.
Tun daga can ta zuba mata ido tanamai hararata, wucewar ta ta gani ta hanyar guest washroom tana doka uban sauri,mammtase kafafunta datakeyi ya nuna alaman fitsari ne ya matseta.
Wani Dariyar mugunta zee tay snn ta tashi tsaye a gaggauce cikin satar idon mutane tabi bayanta washroom din
ahnkli take lekawa cikin sanda a Lokacin data shigo lkcin har wasime ta kammala yin tsarki tana kkrin maida panties dinta bata hankara ba taji an wani fincikota tayi baya,wani irin bugawa da karfi kirjinta yay acikin yanayin firgita da tsoro har ta karkace baki zata saki ihu Da ƙarfi zee ta buge bakinta sanda jini ya tsittu..,bata jira ba ta fixgo ta ta cakume mata wuya ta shaketa sosai tanamai hadeta da jikin bango”
tuni hancin cikin wasime ya cure, cikin nata ya duro ruwa tanajin kamar zata saki fitsari ajikinta
,”ihu tayi niyyar sakawa…zee din ta zare mata ido tare da daka mata tsawa “kiyimin shiru da bakinki,kikq yadda kikayi ihu anan saina kasheki,mayya kawai shahsha yau saina kasheki,in kashe banza.
Kukan bazata wasimevta barke dashi wani mari zee ta dora mata snn ta turata ta fada akasan toilet din cikin ruwan datti,karkar jikin wasime yake rawa jin kanta kamar wata mutacciya
Kuka takeyi mai tsananin nuna firgita saidai marar sauti sabida toshe bakinta da zee din tayi..”wato ke bakiji ko?Uban wa yace miki kizo nan…uban wayace miki kinabin saurayina?zare mata ido take kamar zata hadiyeta cikin masifa
Da baya baya wasime takejan kanta hawaye sungama wanke mata fuskanta tana famar girgiza kanta alaman ta balain jijjiga da tsoro.
Toh Daga yau saiyau
Naƙara ganin ki a inda saheeb yake saina yanka ki…saina hallakaki kin bar duniya.. kina ji ko bakiji?Wasime Bata iya daurewa ba ta saki kuka mai firgitarwa.Au baxaki yi min shiru ba munafuka?Janta tayi akasa tanamai wurgi da ita..ajijjiya take ya soma rufewa wasime ido,cikin kokawa da numfashinta ta soma cewa cikin kuka”..anty anty anty dan Allah dan Annabi kiyi hkri bazan ƙara ba waayyo Allah na kasheni zakiyi anty? kallo daya kay ma wasime zaka tabbatar da cewa bata cikin hayyacinta dan bakaramin raxana tayi ba
Haka zee ta bushe idonta ta cakumo ta kamar yar tsana ta mikar da ita tsaye tana kallonta babu ko digon tausayawa a idanunta taja tsaki mtsww”bangama dake ba”..wani janta tay izuwa bakin water flush system suna kaiwa wajen ta danna kanta acikin bututun kashi ta murda flush ruwa ya rinka zuba akan fuskar wasime yana suffocating dinta,numfashinta ta dinga jaaaa da ƙarfi tanajin kamar ranta zai fice ajikinta,yarinya sai bari take tana tsananta kuka mai ban tausayi amma zee bataji kamar zata dena muguntar ta ba.