FITAR RANANOVELS

FITAR RANA 17

Ciwo ne wanda yake saka airways din mutum ya zamto very narrow,ya kumbura, snn yy producing extra mucus Wanda hakan yake haddasa wahalar fitar numfashi,daga numfashi yay wuyar fita sai kuma tari,da shortness of breath da wheezing duk su tashi a lokaci guda kuma sukan wahalar da mai ita.

Hanya mafi sauƙi da yafiye triggering din cutar baifi exposing kai ga hayaki da hazo da dik wani particles da sukan iya tuamali kai tsaye da lungs din marar lpyar ba
Hakama viral respiratory track infection kamarsu comon cold,da aikin ƙarfi, jijjiga da jigata ko sanyi mai shiga jiki ,sanadin tashin sa wanda bai cika faruwa acikin mutane ba shine Ayayinda mutum yakasance cikin strong emotion or hectic stress wanda Ayanzu haka yana daya daga cikin abunda ya tayar ma wasime nata ciwon bisa tsorata ta da zee baby tayi.har yanzu tsoron bai fice ajikinta ba.

She look so scared nd stressed out,jikinta yay lagwas batada wani cikakken nitsuwa bare kuzari,shikansa yaji babu dadi a zcyarshi matuka gameda suffocating din kanta da ruwa da zee tayi acikin bututun kashi,cos its quiet a dump move shine abunda yake dada hargitsa mai zuciya

hakan datayi hanya ce mafi sauki da zata iya kasheta har lahira batare da tasani ba saiya rasa wani irin muguwar zuciyace a kirjin zainab.

Kada kansa yay snn ya fice ya bar wasimen a kwance awajen,yana bude kofar dakinsa ya tarar da bilti a tsaye duk jikinta yay sanyi da alaman ta damu da yarinyar sosai,kallo daya yy mata snn ya dauƙe kansa ya wuce kasa baiko yi yunkrin kulata ba.

A hnkli ta shiga kiran sunan sa yana shiru yana jinta”hanklinta a tashe take cewa..taheer, taher yaya jikin wasimen ne dan Allah wai meya sameta haka?Binshi tayi suka sauko kasa iya kkri tayi domin suyi magana dashi koda ma tasan abunda yake faruwa da wasimen amma haka ya tamke fuskansa cikin taurin kai yakima ya kulata abunda ke gabansa kawai yakeyi.

Key din motar sa ya daga snn ya fita, magungunan da zai iya bata yaje ya siyo a chemist din dake kusa da anguwarsu, yana dawowa still yasame bilti a tsaye tana jiranshi
,shareta yy still bai kulata ba,yana bude kofarsa ya shiga yaja ya kulle cikin gaggawa yasaka lock taciki ya danna danma kartace zata shigo cikin dakin bare ta damesa dan a inda ransa yake bacen nan ynzu yasan zai iya mata rashin kunya
Kuma baxata ji dadin hakan aranta ba.

Samu yay wasime tana juyi tana birgima cikin wahalar fidda numfashi
Gaba daya ta fice a hayyacinta sai hamm hamm takeyi ta baki ta hanci kirjinta yay nauyi ya daureta gam gam.

Batare da bata lokaci ba ya zauna agefenta snn ya soma bata kulawa cikin gaggawa,yasha wahala sosai kafin numfashinta ya dan samu daidatuwa,sosai ciwon nata ya fusata ya motsa kusan fiye dana koyaushe,shafa gadon bayanta da tafikan hannayenshi ya rinƙayi yana comforting dinta with a warm massage
Bayan ya zarge zip din rigarta.Numfashinta ne yake wani irin fita da ƙarfi jikinta babu abinda yakey face kyarma duk tay wani lakwas abar atausaya.

Murkususu ta dingayi cikin azaban ciwon kai gashi,Sotake ta ƙwace kanta daga jikinshi amman rashin ƙarfin dake tattare da ita yasa bazata iya aikata hakanba.

manne ta yay da jikinshi snn ya lafar da kanta akan kirjinshi yana kkrin bata emotional support dan yasan da akwai mummuman tsoronsa a tattare da ita,wani sharrr
tayi akan kirjinshin jikinta duk yabi ya mutu tana sauke nannauyar numfashi.

Kusan mintuna biyar suka ɗauka manne da juna banda ajiyar zucya babu abinda takeyi tabi tayi lamo ajikinshi jikinta babu kwari yanayinta tamkar an mata shegen duka

Jiyake wani zazzafan huci na fita daga bakinta da hancinta yana ratsa mai jikinshi, Lumshe manyan idanunshi yayi yanajin yadda komi nata yake dada rikicewa.

Shimfidata akan filo yay a hankli tay sauri ta takure kanta waje guda tana kyarma,Alluran paracetamol ya hada snn ya debo ruwan sanyi a cup ya bata abaki tasha.
Ahnkli ta koma ta kwantar da kanta akan pillow tana dan maida huci mai zafi,cikin nitsuwa taji ya mikar da ita snn ya tattaro ta
Kirjinshi, babu abunda zcyrta take sai bada sautin bugu mai karfi,ji yay kamar bai taɓa yin allura ba saiyau gaba daya abun yana neman yay masa daban.

Cikin basar da feeling din dayakeso ya dameshi ya hanashi sakat ya fixge kanshi ya rangwafota kadan ta mannu da kirjnshi, baijira ba ya nemi soft spot ya dallara mata alluran dan ƙara ta saki snn ta fashe da kuka sosai, jikinta na rawa tanajin yadda yake zare bakin allurar ahnkli wani kankameshi tayi saida ya lumshe idanunsa tare da yin lamo ajikinta a bazata.

Bilti dake manne da kofa tanajiyo su kukan da wasime takeyi yasaka nan da nan hanklinta ya kara tashi.Tarasa yadda zatayi ta samu kwarin gwiwar shigowa ciki duk idanunta sunyi nauyi saboda damuwa ga bacci mai nauyi daya gama da ita.

cikin nitsuwa da yanayin tausayawa halinda takeciki ya zareta ajikinshi ahankli snn ya kwantar da ita, Zamanshi yy agefen gadon bayan yy discarding syringe din, after like 5mint yaji wajen ya dauƙa da wani irin shiru,dan leka fuskarta yy yaga wai hartayi bacci..

tsayawa yay akanta yanamai kallon zufar dayake tsatsafowa a saman goshinta,babu abunda fuskar nata yake sai kyalli,duk gumi ya wanketa da alaman saukar zazzabin ne ya zo.Tabe bakinsa yay snn ya mike tsaye ya isa ga wajen swich,speed din A.cn shi ya ƙara gudun sa kadan snn ya taho ya lullube ta da bargonshi mai laushi ya kashe musu wuta.,daga nan shikuma ya koma kan doguwar kujerarsa yay kwanciyar sa bai wani dade ba shima baccin ya kwashe sa.

Washe gari da asubahin fari 5 tana bugawa ya farka,idonshi bai fara sauka akan komi ba face wasime,gani yy haryanzu tana kanannede da bargo comfortably cikin nisan bacci wanda daga gani kasan da alaman jikintan yanada bukatar hakan ne.

Dauke kansa yay akanta ya shiga toilet ya dan watsa ruwa snn yayo alwala sharp sharp ya zura black jallabiyarsa ya nufi masallaci.

Yana bada baya wasimé ta soma motsi acikin baccinta,tana famar juye juye,sanyin asubahi dana A.c sun hadu a lkci guda suna takurata,atake atake taji wani abu na tsikararta, mararta ne ya cika tam da fitsari gashi ya matseta yahanata sakat tanata mammatse jikinta acikin hargagin bacci as usual jin komi takeyi kamar acikin mafarkinta dan haka kafin tace zatayi wani kwakwkkrn motsi tagane cewa fitsari takeji in reality har ta sake mararta ta tsula fitsari gaba daya ta jiƙa wajen kwanciyanta sharkab da fitsarin dama shi fitsarin mace yawa garesa…
wani tsuuuu kakeji fitsarin na sauƙa akan gadon Mararta yana sakewa kuwa wani niimmataccen bacci mai shegen dadi ya sake kwasarta yay awon gaba da ita.

Har izuwa ƙarfe shida da rabi taher yana cikin masallacin anguwansu yana waya da abbansa malam Qasimu akan yar wata cakwakiya dayake neman tsoma kanshi aciki.

Hanklin sa ya balain tashi bisa Wani gagarumin sharri da ake neman a kulla ma mahaifinsa,sabida shikadai ne dan kasuwar dayaki amincewa yahada kai da yan siyasa masu shigowa da mugayen makamai da kwayoyi daga kasashen waje.

A cewarsa wani shahararren dan siyasa ne a kaduna dayake neman mukami yayi odersu,yana so yan kasuwa irinsu su tayasa smuggling din makaman zuwa cikin kasa,wanda zai rarrabawa yaransa yan ta’adda suyi amfani dashi wajen kawar da duk wani mai shirim kawo musu wargi sabida gangamin shirin zabe ya gabato.

Previous page 1 2 3 4Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button