FITAR RANANOVELS

FITAR RANA 19

“Bakinta taji an make da karfi saida yay jini..,cikin daka mata tsawa yace”kikace mene? Waye ɗahirun ki?Nace waye dahiru?

Matsowa bilti tay zuciyanta duk ya raunana da tausayin wasime

Taheer dan Allah kabita a hankli.

Dangwala wasimen yay a kasa batare da ya kalleta ba ya daure fuskansa tamau yace “babu ruwanki”.ni ki kyaleni.

Hannun wasimen yaja a sukurkuce ya tura keyanta zuwa inda yake wanki Ya tsayar da ita acan ta gabansa yana kallonta cikin harara

Neman waje yay ya zauna agaban bahon inda zai fara wanki snn ya umarceta data saka gwiwowinta a kasa snn ta daga hannunta sama

Jikinta na rawa ta aikata hakan…sai ruwan hawaye datake saukarwa
Hararta yay snn yace
“Close ur eyes..”
Batagane meyace ba.
Ahnkli cikin sanyin jiki Bilti tace yace ki rufe idonki”. Da sauri ta rufe idon..
Wani shiru wajen ya dauƙa ayayin da ya shiga wanke bedsheets din kansa a kasa baiko sparing one minutes danya dubi yanayinta ba.

Hakama bilti datake tsaye,zuciyanta duk ya mutu da tausayin wasime,she just cant find the caurage to leave her acikin wannan hali

Haka wasime taci kneeling hannayenta suka dau tsami,gaba ki daya idanunta rawa sukeyi gashi tasani bata isa ta budesu ba.

Ahaka har ya gama wankinsa ya dauraye yaje ya shanya a clothline snn ya dawo yamaida komi mazauninsa a yadda ya samu….

Plastic chair ya jawo ya zauna ata gabanta ya harde kafafun sa daya akan daya snn ya zaro wayarsa yacigaba da latsawa,bilti harta gaji da tsayuwa ta wuce jiki a sanyaye ta koma cikin gida tana hawayen tausayin wasime.

Yarinya ga yunwa,ga rashin lpya amma ace taheer baiyi duba da hakan ba?ji tayi kamar ta dauki wayarta ya kira mahaifiyarshi ta sanar da ita abunda ke faruwa,saidai kuma itakanta tasan yadda suke sangartashi ba lallai bane hakan yay wani amfani,domun kuwa iyayensa basa amincewa su amshi laifinsa haka kawai sumtimes harsai sungani da idanunsu ko ya aikata agabansu snn su amince
Barinma mahaifiyarshi datake tsoron bacin ransa,sam bata son taga danta ya bata rai fadama daurewa kawai takeyi tamasa amma badon wai tana so ba.

Daga waje kuwa wasime
Tagama galabaita da yunwa ,jikinta ya dau wani irin zafi sabida kuka da tashin hanklin datake ciki…tsabar taji babu dadi ajikinta bata san sanda tafara bashi hkri ba..da kyar ma ya hakura ya kalleta…snn ya umarceta data mike tsaye .”a dangale ta tsaya kafafunta da hannayenta duka suna mata wani irin nauyi da tsami.

Yace zaki sake fitsarin kwance,cikin kuka sosai tace A’a Wallah tallahi na dena

Tsaye ya mike kamar wanda zai sharara mata mari “menace miki akan rantsuwa”..sauri tayi ta kama bakinta muryanta na rawa tace “kayahakuri shima bazan kara ba.

Kunnenta ya kama ya ja ya kuma kafe ta ido ita kanta tasan bata isa tayi gigin yin wani kuka ba,a tsomare tayi tsamm da jikinta tana jan ajiyan zuciya yace “ke bakiji kunya ba katuwa dake kinai ma mutane fitsarin kwance?,wani irin sunkuyar dakanta tayi can kasa tanajin wani iri iri sosai acikin zucyarta gaba daya kunya da damuwa sun dagulamata kwakwalwa she is feeling soo awful abt her self…jikinta yay sanyi bana wasa ba.

Yace “toh daga yau sai yau,in na kara ji ko na gani kina fitsari saina miki shegen duka….
Snn na hanaki fitowa waje ko zuwa wani waje,daga yau sai yau babu ke babu saheeb kinji menace ko bakiji ba?zuciyanta a matukar karye tace naji,”yace menace?..dagowa tay a hankli cikin muryan kuka tace “kace karna sake fitsari, kar na fita waje snn babu ni babu yaa saheeb “yace good…
Toh ki aje wannan a kwakwalnki kinaji na ko?
cikin hanzari ta gyada mishi kanta snn tace eh naji..sake kunnentan yy ya tsaya yana kallonta snn yace “akwai sa’anki a gidan nan ne?..a hankli tace a’a babu.

Yace Toh karna ƙara jin kin kira wani babba da sunanshi gatsau babu girmamawa sabida duk gidan nan babu sa’ar wasanki.wato sabida ke baki da kunya, bakisan babba ba shine zaki bude katon bakinki kinacemin dahiru ko?toh zan kuwa koya miki hankli,nasaki jin suna na abakinki saina yanka miki wuya..wawiya kawai,Shiru tayi batace komi ba hannunta yaja yanamai jan tsaki suka shiga ciki tare,direct ya wuce da ita dakinsu
Nabaki minti biyu ki shiga kiyi wanka yanzun nan kifito,..kamar walkiya ta yi hanyar bathrum cikin sauri tayi wanka agurguje tanayi tana kuka ahankli.
Yau Bakaramin tashi hanklinta yayi ba bata taba shiga hali irin na tsoro da firgita kamar nayau ba.

Haka tayi wankan ta fito ta same sa a tsaye duk jikinta na rawa haka ta shafe jikinta da mai duk kunyarsa ya cika mata kirji amma ko ajikinshi yana tsaye yana kuma lura da ita,..yunwa sosai takeji,tarasa abunda yake mata dadi…ganin jin kunyar bazai ficceta yasaa ta dan saki ranta ta shirya tsaf agabansa snn suka sauko kasa tare.

bilti ne kadai a falon ta rafka wani uban tagumi.
Boyayyar ajiyan zciya ya sauke yanamai ayyana wasu abubuwan acikin ransa…”amma bayajin zai iya saukowa yanzu.

Ya fara lura da cewa da akwai tsagwaron rashin tarbiya ajikin wasime kuma bayajin bilti zata iya saita mata kanta ta dawo normal,dan haka dolenshi ne ya jajirce akanta harse ta koyi hankli…bai damu da yadda zasu dauki abun ba amma zuciyarsa ta riga ta harxuka da fushi
Da tsananin kishi musamman akan ababen da saheeb yaay masa gori akai yana kiransa wawa.

Hannunta yaja suna tafiya har suka iso tsakiyar falo bata iya dago kanta sama ba.
Jan zciyarta kawai takeyi ahankli ta dawo abar tausayi kamar ba wasime ba.
MIkewa tsaye bilti tayi data gansu saidai bata iya ce mishi komi ba
its already getting to 10ckl yarinya bata saka komi acikinta bakaramin tausayinta bilti takeji ba.

Tana cikin sake sake aranta sai taji anjefo wasimen ajikinta jeki ci abinci…yana fadan hakan ya juya abunsa ya haura sama ya nifi cikin dakinsa.

Kuka mai zafi wasime ta sake ayayinda ta kankame jikin bilti kamar yar da aka rabata da uwarta shekaru aru aru

Cikin tausayawa da sanyin jiki bilti ta dauketa ta dorata akan cinyarta ta dada rungumeta tana bata hakuri da kyar tayi shiru,sannan ta zubo mata jollof din taliyar data dafo mata tahau bata abaki,tunfarawarta harta gama fi hawaye takeyi..bata wani yimasa cin kirki bama tace ta koshi…janta bilti tayi suka nifi daki anan ma ta dinga rarrashinta har saida bacci mai nauyi ya saceta

Bangaren taheer kuwa yana isaga dakinshi yahau kintse kimtse
Ya zanxa sabon bedsheet yay wanka ya shirya kansa cikin wata black suits,baiko bita kan abincin bama ya wuce yay hanyar military medical schl dinsu domin attending make up classes dinsa dayay missing kwana biyu a sakamakon tafyar da sukayi..

Daga nan wani Shiru gidan ya dauka da kyar bilto ta sake ranta ta dena damuwa ta fada yin ayyukanta nayau da kullum,duk wani abunda tasan zai kwantar ma wasime hankli shitake nema domin tayi mata dan bakaramin tausayi wasime ta bata yau ba.
Aikuwa tana farkawa abarci acikin kalilan lokaci bilti tajanye ra’ayinta harta sake ranta ta tsunduma wasanta da yar baby.

Karfe 1.30 lokacin ana kkrin fita daga sallahn azhar amma Har yanzu saheeb na kwance bai dawo cikin hayyacinshi ba…”abunda ya afku tsakanin sa da taheer ne kawai yake masa yawo akansa… Inya tuna zancen auren nasu sai yaji kamar ana kona mishi zciyarshi ne da wuta..he was deeply cut abun yay masa zafi sosai
Duk dama yana son abokin sa amma ayanzu haka baijin son dayake masa zai iya rabashi da yarinyar daya gama dora duk wani burinsa na rayuwa akanta.

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button