FITAR RANA 31-35

Koda wasime ta waiga baya taganta tana bibiyarta batace mata komi ba dan bata riketa da komi a zuciyarta ba,so long as bazatayi wani abunda zaisaka yayanta yaji haushi ba ita bata da wani matsala da zuwar najaha.
Kusan atare suka jera zasu haura sama dakinshi,caraf sai gashi nan saukowa sumewar tsaye najaha tayi ganin shi ya sako wata all black suite na Armani
Wacce ta mugun dauƙe hasken fatar jikinshi sakake tay da baki tana fadin wayyo Allah tacikin zcyarta. fadin irin kyan da yay ma bata lokaci ne ita kanta wasimé saida taji wani abu na daban a acikin zuciyarta mai sanyi yana mata yawo tundaga tsakar kanta har izuwa tafin kafafunta
Data kallesa a hakan.
Sosai yay kyau bana wasa ba tafiyarsa yake a nitse Shikam baisan ma sunayi ba,he was seriously thinking of weda ya ci abincin or not cos baison ya debi abunda zai zo ya dameshi gashi cikinsa nada saurin tsurewa.
Fuskansa adan haɗe ya sauƙo kasa ya same suna daga tsaye, wasime dauke da tray a hannunta duk sunyi tsuru tsuru kamr yan matan bin gida kowacce tana binshi da salon kallo.
da kallo daddaya yabisu sann ya saka kai ya wuce tagabansu abunshi,wani sum sum suka juyo a tare suka hau binsa abaya.
Adaidai tsakiyar falon yaja ya tsaya wasime ta aje tray din akan center table snn ta dago ta kalle sa gefen kunnen ta tadan sosa kadan snn tace “uhumm yaya ga panken har…
Cikin sauri najaha ta cabe maganan a bakinta.
“Tace eh eh har nagama yaya, ai ni na koya mata yadda akeyi,shine sai nayi mata panken itace tace zata kawo maka ko zakaci?baice uffan ba Yanata kallonsu babu yabo babi fallasa ,sai yaga wasime tay karamin murmushi batace komi awajen ba..
Ajiyar zuciya ya mayar ta ciki,fuskansa a dan takune kamar ma bazai taɓa taɓa abun ba. kirjinsu duka biyun sai bugawa yakeyi yana racing kamar wanda suke gaban alkali
Can dai ya nemi waje ya zauna ya kalle fuskan wasime adan sace
,muryan sa ciki ciki yace”ok bring it lemme see..
Acikin sauri wasime ta dauki plate din panken zata kawo masa gabansa, babu wani kunya najaha ta saka hannun ta wafce daga hannunta cikin langwabe wuya da salon makirci
Tace kai wasime ni fa tayaki kawai zanyi ai saiki dauko tea din tunda ke kika hada mishi dakanki,wasime bata ce komi ba tabar mata panken ita ta dauki tea din kusan atare suka kai gabansa Kowacce tana kkrin miƙa mishi nata first..
Wani irin kallo mai kama da harara yabisu da shi a lokci guda yace ‘Drop it down.Najaha ce ta soma ajiyewa Æ™asa tana famar
Kankaro karairaya bata farga ba har ya miƙa hannu ya amshe shayin daga hannun wasime.
Wani Cak ta yanke karairayar ta wani kalleshi a sace haushin hakan tuni ya cikka mata kirji mtsss taja tsaki taciki ganin duk Hanklin wasime gaba daya nakan sa, ganin har yakai tea din bakinsa yana kkrin sippng wanolivdadi ne ya gume wasime musmmn ganin datay yau har sai biyu ya kurba.a hankli ya zare cup din daga bakin sa sann ya aje shi akan table.,daidai zai miƙa hannu kenan ya dago plate din pancake din yagani najaha tay wani wuff cikin sauri ta dauka ta mika masa irinna wasime tana washe masa baki..
Kallonta yakeyi he was like wahts wrong with this girl anya kanta daya kuwa?Tsaki yaja acikin ranshi cos He tot she is just being silly dan kawai ya koreta agidan ranar
Dagashi har wasime basu dago nufin najaha akansa ba,sama sama ya tattaba fanken yaci dan kadan, duk da haka saida fuskan shi yadan nuna alaman ya yaɓa da kkrinsu dan baiyi tsammanin jin taste din haka ba,murmushin najaha sai yafi na wasime wanzuwa yadda kasan anbata kyautar mota haka ta dinga washe baki.
Harga Allah so take lallai ya fahimci cew itace kawai tay masa komi.
Taga baifi sau biyu ya gutsira fanke ba ya aje sauran ya miƙe tsaye yana mai goge bakinshi da food wipes.
Jakar laptop dinsa ya dauka snn ya mikawa wasime ya wuce gaba binsa ta shigay a baya
Har suka kai waje suna takawa har wajen dayake parking motarsa
A falo suka bar najaha tana tsaye cikin son taji mezaice ma wasime a awaje,ziriya take duk ta kasa samun nitsuwa a tunanin hala ta yabonta kawai zaiyi,da mugun gudu ta isa wajen windown falon a cikin sanda ta yaye labulen kadan tanata satar kallon su.
Har gaban motarsa suka tsaya yana kallonta cikin basarwa ya dan daure fuskan sa”Yace yaushe ne zata tafi ne?..tace nima bansani ba,amma cemin tay wai har saika dawo tukun itama zata tafi..”Kankance idanunshi yay akanta cikin sigar masifa..”Yace akan me maman ta bazata nemeta ba ne?cikin gyada mishi kai ta amsa da cewa”yaa ita tacemin wai maman ta ne tace tazauna min har sai lokcin da zaka dawo saita tafi,shiru yay bai kara cewa komi ba fusknsa ba asake ba Da alaman Baiso jin hakan ba amma dai yay shiru…
Sai can daya shiga motarsa ya zauna snn ya dago kai ya dubeta cikin sanyin murya yace kina bukatar wani abu ne?kanta na kallon kasa tun kan ta amsashi ya zura hannayensa cikin aljihun sa ya zaro dari biyar ya damƙa mata a hannu
Yace toh kiy hkri ki rike wannan kinga dai banida wani kudi yanzu..and pls dan Allah dont play around ki kula da gidan nan da kyau saina dawo.
.Kanta a kasa ta dan rusuna mishi cike da nuna girmamawa tace “ok nagode yaya,bai kara ce mata uffan ba yaja motarsa ya bar wajen tsayuwa tay awajen tanajin kewar sa sosai acikin aranta,duk tabi tayi wani jimmm tana kallon bakin gate da kalar tausayi,bata motsa ba harsaida ya bace ma ganinta kat sann ta sauÆ™e ajiyar zuciya ta dawo cikin gida.
Sallama tayi Najaha dake laɓe ajikin window ta farga da mugun gudu har kamar zataci da bakinta ta barwajen cikin sauri tahau tattare tattaren karya.
tun daga can Wasime ta tsaya tana kallonta tace “yo ke kuma ina zakikai abincin bayan ya tafi ai ajemana kawai zakiyi muci, inbamu koshi ba sai muje kitchen mu kara dafa wani.
Babu musu suka aikata hakan,a falon suka baje suka ci panke da shayin su mai kauri suna yar hira,wasime tana mugun son najaha ta kokkoya mata abubuwa dayawa na girki saidai aynzu tunda taheer ya tafi taga gabaki daya yanayin najaha ya sauya lokci guda ta dena wani motsi.
Banda kwanciya da zaga waje babu abunda takeyi,
Haka Wasime ta dingajin haushin abun aranta.
Bata ƙara taya wasime daga ko da tsinke ba.
haka yau suka karace zamansu a gidan har yamma ya gabato najaha bata daga ko casss a gidan ba.
Saidaf magrib tay wuf ta tashi tahau cewa wasime muje kitchen mudafa wa yayanki abinci..ba musu wasime tace toh muje Dama duk tabi ta isheta da malala akan capert,dan hakan wurwuri suka shige cikin kitchen wasime ta bude store dinsu ta debo musu kayan abinci
Nan da nan taga najaha ta zage damtse ta shirya wata arniyar jollof rice mai uban kamshin kifin ga spices da suka saka aciki ya dabaibaye gidan da qamshi mai shegen dadi…sosai wasime ta tsaya ta koya yadda taga najaha tanayin komi
Abincin yay dadi dan Ita kanta wasime bakaramin kawo yawu tadinga yi ba,fuskar ta dauke da annashuwan yau taheer zaizo gidan ya tarar da abinci mai dadi ta gode ma najaha sukayi akan gobema intazo haka zasuyi wani irin girkin.
da yamma wajajen Shida da minti sha takwas taheer ya shigo cikin gidan,taheer yana leko falon daidai l’okacin najaha tagama shiryawa tsaf akan zata nuna kanta akan itace tay abincin nan mai shegen dadi da qamshi kodan ya yabeta ya kara bata lasisin cigaba da zuwa gidan.
Najaha sai zumudi takeyi
Duk ta kasa zama waje daya Taher kuwa daya shigo Baiko tsayayin wata wata ba yasako wasime agaba,yace maza tacewa najaha ta wuce gida dare yayi shizai kulle kofa..