FITAR RANANOVELSUncategorized

FITAR RANA 31-35

Haka wasime taje ta sameta ta fada mata
badon taso ba haka ta sabi hijabinta jikinta a mugun sanyaye ta wuce gida tanajin bakin cikin abincinta datayi.

Har ta isa gidansu tana famar cizon yatsa,duk bakincikin zagewarta datayi wajen yin masa abinci shiyake dawainiya da ita ko sallama batay ba ma uwarta data iske a tsakar gida ba,zucyarta qumshe da bakinciki ta wuce dakinsu ta zauna abakin gado ta wani hade tagumi.

Tunani take dan Batasan ma ko zaici ko bazaici ba,yau tasone ace yaci abincin agabanta kodon taga reaction din fuskarsa.

Anan gida kuwa wasime ce a kitchen tana famar tattare wajen da si’ukayi girkin,bayan ta kammala komi ta tsaftace daga nan ta wuce dakinta tay sallolinta gameda doro sabuwar wanka sabida dadewar da sukayi acikin kitchen.

Riga da sket ta saka batare da ta shafa komi a fuskanta ba ta sauko kasa ta same sa lokcin har ya dawo daga masallaci Yana zaune a falon da remote din tv a hannun shi yana daddanawa kara gaishe sa tay cikin ladabi snn taje ta kawo masa abincin ta aje agaban sa…
Da gefen idonshi ya kalli abincin yanaji aransa kamar bazaici ba
Da kyar ma ya amince mata cewa zai dan cin,duk tsronsa kar suje subashi wani jagwalgalen da zaizo ya hanasa yin bacci,da rawar jiki wasime ta zuba masa jollof rice din a plates,snn itama ta debi nata zataci. saida ya bari ta gama deɓa sann ya karbe plate din a hannun ta ya hada musu waje guda danashi alaman yanason suci a plate daya tare dashi.

Batace komi ba ta zauna kusa dashi sun dan dau lokaci sunacin abincin su a cikin nitsuwa,baaiyi tsammnin zaiji taste din abincin so normal kamar haka ba,ci sosai yay dan baisan sanda ya zage yana deban dadin abincin daya raina din sosai ba.

Lura da ita ya dingayi a sace ganin tunda suka faracin abincin sam bata yarda sun hade ido tare dashi ba. Kyabe bakinsa yay game da sauki karamar smirk,jin tayi ua jawota jikinshi kamar tay kuka ta dada binne kanta kasa game da lafewa ajikinshi tay shiru”dauke kansa yay snn ya dage kansa sama yana tauna abincin bakinsa har saida ya kammala kafin ya sassauto da muryan sa yace hmmm ahaka ne zakici abinci harki koshi kinaci kamar bazaki ci ba?..cikin sanyin murya batare da ta dago ba tace inaci fa yaya, Æ™arban
Spoon din hannunta yay tana kallonsa har ya debo abinci mai dan yawa ya kawo daidai setin bakinta yana kallon ta da wni irin siga mai sanyi”..kirjinta na bugawa ta runtse idanun ta game da budewa da idanunshi taci karo yace “ci mana!..a hankli ta bude bakinta ya cusa mata abincin aciki cikin nitsuwa,taunawa takeyi a hankl kamar bata san abunda takeci ba jitake
Kamar wani sabuwar abincine ya juye mata acikin bakinta,da wasa da wasa haka ya dinga
Bata tana amsa harsaida ta gaji tace masa ta koshi.

Murmushi yay ya dauƙe idonshi daga kanta abincin dake gaban shi ya cigaba da ci sai kuma ya ajiye spoon dinsa ya jiyo da wani irin smirk a fuskanshi ya sake matsota ta jikinshi yace
“You didnt tell me who cooked this?..dagowa tayi ta kallesa ahankli tace masa najaha ce.
Baice uffan ba ya cigaba da kallon bakinta…
Can kuma sai taga ya cirota ajikinshi batare da yay wani coments ba ya miÆ™e tsaye ya haura sama zuwa dakinshi yana mai barinta a wajen a zaune…..

Na kudi ne,300₦ via 0152983148..GTB
08060712446.
7/25/22, 19:19 – Kawata: FR33

Desperate 13;fairy wife

Na kudine 300₦ via 0152983148 Gtb wasap 08060712446

Inda yabi ta dinga bi da kallo,can cikin sauƙe ajiyan zuciya ta dauke idanunta daga wajen zcyarta cike da waswasi da neman son sanin me yake nufi daya tashi haka kawai ya kyaleta awajen batare da yace mata komi ba..

Dan tsuke bakinta tay snn ta mike tsaye tahau tattara wajen da sukaci abincin takai empty dishes din kitchen ta ajiyesu akan sink, ta dawo falon tay zaman ta tare da daukar remote tanata daddanawa harta kamo tashar da ake zuba american films ta samu dai dai ana kan wani funny film waishi “the boss baby”..shi ta nitsu ta soma kalla,film din ya dan tsufa kam amma bakaramin nishadantuwa takeyi dashi ba,dariya ta dingayi ita kadai kamar wata sabuwar kamu.

Ahnkli aka tura kofa taheer yana fito daga dakinsa sanye da wani grey three qtr shot da white armless shirt da waya a kunnensa yana kkrin jan kofarsa yana kuma amsa wayar a nitse..ya fito ne sabida ya dauƙo ruwa mai sanyi a fridge.

tunkan ya kammala wayar yasomajin karar sautin dariyar wasime tana kyakytawaa duk sautin ta ya karade gida,Daga can saman corridor ya dan leƙo ƙasa kasa da mamaki dan ya gaskta hakan,a can yaganta tana zaune sai famar kyakyata dariya take har kaman zata zubda hawaye tsaban dariya.

Tsayawa yay yanata kallon dariyarta,zai iya cewa ma tunda yake bai taɓa ganinta a cikin farin ciki da Annashuwa irin wannan ba,gabaki daya hanklinsa saiya koma kanta yana ta kallon annuri da nishadin dayake wanzuwa Akan kyakkwan fuskarta, haka kawai yaji ransa yay sanyi atake ya sauƙe wata ajiyar zuciyar daya sauƙe masa wata sabuwar nitsuwa.

Dan firgita yay jin anata calling attention dinsa atacikin wayarsa, adan harzarce yanamai dafe goshinsa yace oh im so sorry i got carried away me kace ma?Wanda suke wayar dashi yace “ok,i said next week insha Allah zan turo maka sauran kudinka idan sun shigo saika min magana…yace ok babu komi thanks..daga nan sai suka datse wayar..

ajiyar zuciya ya sauƙe da tunanin duk yadda zaiyi ya kashe kudadensa dake cikin acct da salaryn shi na wannan watar.

Yasan dai rabi akan Hidimar komawar wasime schl zai tafi sabidaa new session ne kusan komi da zai siya mata zai iya zamtowa sabo,and he needs to get some food stuffs a gidan
Tunda yaga kamar she is having so much intrest akan girka abincinta agida, har yau dai baiji duriyar iyayen sa ba barema su turo da normal upkeep da suka saba turowa a gidan.

Saukowa yay zuwa cikin falon atake iskan wajen ya gauraye da qamshin turarensa mai dadin qamshi,qamshin ne ya soma sanarda wasime zuwan sa,amma bata ko iya juya kanta ba ,a cikin nitsuwa tay saurin gintse sauran dariyarta tay shiru tana satar kallonsa harya ya karoso ciki.

Ko kallanta ba baiyi ba ,waje kawai ya samu ya zauna a one sitter baice mata komi ba ya fara latsa wayar sa,juyawa kadan tayi tadan sace kallonsa sai taga gabaki daya hanklinsa yanakan wayarsan me…duk saita rasa meyakeyi acikib wayar daya bada hanklinsa gabaki daya baiya ko kiftawa,Kamar da wasa tafarajin kamar bata da nitsuwa acikin zuciyarta sabida abunda yakeyi din.

wani lumui tay tana ta satar kallonshi ita Kawai tana son taga ya dena latsa wayar,inba haka ba kuma tana son sanin abunda ya dauke hanklin sa dayawa har haka aciki.

Da kyar dai ta kaucar da wannan yanayin a zuciyarta ta basar ta cigaba da kallonta jim kadan anayin wani part mai abin dariya bata iya controlling kanta ba ta wani tuntsire da wata mahaukaciyar dariya mai dan iskan karfi wanda yasa shi dauke kanda akan wayar game da dagowa atake,kirjinshi saida ya buga dayaji sautin dariyar, fuskan sa a dore ya dago kansa ya na kallonta,suna hade ido Wasime tay tsit game da kama bakinta bata kara yin wani motsi awajen ba.

Hade rai yy Cikin hararar ta,muryansa ciki ciki yace “ke zo nan!.

Sadaf sadaf ta tashi ta iso gareshi tare da rusunawa a gefen shi ta takune fuskanta tana dan turo bakinta gaba

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button