HALIN GIRMA COMPLETE HAUSA NOVEL

HALIN GIRMA 13

 Halin Girma    13

*Zafafa biyar na kudi ne, idan kina so ki karanta ki tuntubi 08184017082 or 09134848107* 

I’m on Instagram as @zafafabiyar5. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1ft46u5twk6r3&utm_content=nj79azb

***Sai da suka ga tafiyar su sannan suka dawo ciki, kowa da abinda yake cin sa a zuciya. Tabbas sun amsa sunan babban gida, haka sun nuna Halin Girma da dattako na irin manyan mutane da suka san mutunci da yakana.

   Fadar irin tarin kayan da suka zo dashi ba abu bane me sauki, hakan ya dan tarsa tsoro a zuciyar Abba, yake jin tamkar siyar da Iman din zai yi, wannan uban dukiya a matsayin tambaya, ina ga idan aka zo auren? Basu da talaucin da arziki zai tsorata su, sai dai dole ne suyi mamaki ganin uban dukiyar da aka lafto da sunan na Iman din ne, tun daga kan sutura zuwa kayan kawa na mata, da kyautata gwala-gwalai tamkar ba’a san darajar su ba. 

   Haduwa suka yi suka tattauna yadda zasu adana komai saboda yadda rayuwar yanzu ta zama ta rashin tssro, shawarar farko shine su bar maganar tsakanin su domin mata akwai sakin baki musamamn idan abun da ya sha musu tunani ne, yanzu zasu yi ta kwazozotan sa har wasu dake waje su samu damar aiwatar da mummunan kuduri akan su.

  Tabbas shawarar tayi dan da gaske komai na iya faruwa idan maganar ta fantsama shiyasa kawai a take aka fita da motar da duk abinda yake ciki daga gidan zuwa in da zai fi zama safe kafin bikin yazo kusa sosai sai ayi abinda ya dace dasu, ko bata kayanta ta tafi dasu tunda dama su chan babu wani tsoron rashin tsaro ta ko ina zagaye suke da Jami’an tsaro. Karshen magana kuma ma shi Muhammad din kansa, su ne tsaron ma baki daya. Da wannan shawarar suka tashi bayan Abba ya sanar musu da zuwan iyayen Bashir a gobe kamar yadda Mama ta shaida masa.

   

Sake gwada kiran Maman Iman din yayi bayan ya koma gida, cikin sa’a kuwa kiran ya shiga, bata wani jima tana ringing ba ta dauka a nutse cikin sallamar ta da muryar da yake jin ta kullum a bakin Iman din, maganar da sak ta mahaifiyar ta, hatta nutsuwar ta irin ta uwarta ce shiyasa yake jin ba zai iya mantawa da ita ba ko da shekaru sun ja, duk da yanzu babu batun soyayya a tsakanin su tun da be riga yasan matsayar da take a yanzun ba ko da aure ko babu, a dai kwanakin baya ya samu labarin tayi aure har da albarka Yaya a tsakanin su.

“Ina wuni Abban Iman?” Ta gaishe shi jin yayi shiru bayan amsa sallamar ta

“Lafiya Lou Maimunatu, ya gida ya kowa da kowa?”

“Kowa lafiya Alhamdulillah, Iman fa?”

“Tana nan lafiya.”

Shiru sukayi baki daya, kowa da kalar tunanin sa a ransa, shine ya katse shirun ta hanyar cewa

” Inaso zan kawo miki ita kamar yadda nayi miki alkawari idan auren ta ya tashi, ta samu miji har an tsaida rana wata daya, in sha Allah a tsawon wata dayan nan zata zauna a wajenki, a matsayin ki na mahaifiyar ta sai kiyi duk abinda ya dace, kiyi hakuri da Kaddara, kiyi hakuri!”

Wani irin yar taji har cikin kanta, Iman dinta har ta girman da zata yi aure, rayuwa na gudu sosai, tana tuna lokacin da ta dawo masa da ita, da irin tashin hankalin da ta shiga a rashin ta wanda bata taba tunanin zata dawo daidai ta cigaba da rayuwa ba, a lokacin tunani take rayuwarta ta kare gaba daya, amma kuma sai gashi ta cigaba da rayuwa duk da babu ranar da zata fito ta fadi bata tuna yar tata ba, amma ya zatayi? Mutane na fifita al’ada akan addini. Ta sani sarai uwa ce taka da ikon rik’e yarta har zuwa aurenta, tare da sharadin kula da duk wata bukatar ta daga mahaifin ta, sai dai idan anji tsoron tarbiyyar da zata samu a wajen uwar, toh amma a lokacin wa take dashi da zai tsaya mata? Bayan iyayenta da take ganin su a matsayin gatan ta sun kekashe kasa sun ki amincewar da rikon nata a wajenta? A lokacin da akwai karancin shekaru a tare da ita, amma da ace yanzu ne, babu me raba ta da yarta kuwa, duk yadda zatayi zatayi ta tabbatar da ta rik’e ta a wajen ta. Ta bata kulawa da dukkan gatan da take bukata.

“Allah ya sanya alkhairi, ya nuna mana lokacin.”

Kawai tace dan bata kuma san me zata ce masa ba, taji dadi da ma ya cika alkawarin sa, zatayi kokari a dan zaman nan ta koya wa yarta kaunar ta da sabawa da ita da yan uwanta, sannan ta nusar da ita rayuwa da yadda zata kula da auren ta. Sallama sukayi da alkawarin ana gobe zai kawo ta, zai kira ya sanar mata. Godiya tayi masa dan har gobe tana ganin kima da mutuncin sa, mutum ne shi na gari, me kirki da son iyalin sa.

  Bayan gama wayar da sukayi ne zuciyar sa ta gwada masa kiran Zeenat ya sake gwada tankwarata, idan Allah ya taimake shi ta hakura sai yafi kowa murna, dan yanzu bashi da babban tashin hankali kamar auren zeenatun da yake da yakinin zai iya zamar mata wani Babban tashin hankali a gaba.

  Kiran nata yayi, tana dagawa yace ta matsa daga wajen kowa zai yi magana da ita, da ido ta kalli Mama dake zaune ana maida maganar auren Zeenat din da Hajiya ta fice zuwa tsakar gidan.

“Abba na fito.”

“Yawwa zeenatu, magana nake so muyi a matsayi na, na mahaifin ki, kin san dai ba zan taba zabar miki abinda zai cutar dake ba, ba kuma zan ga cigaba a gareki na dakushe ki ba, ina neman alfarma, kiyi hakuri da Bashir  ki kawo wani ba shi ba,nayi miki alkawarin tsaya miki kinji?”

Gabanta ne ya fadi, a tunanin ta an gama wannan babin, sai gashi Abban ya dawo da shi yana kuma kokarin daure ta da jijiyoyin jikinta.

” Kina jina zeenatu?” Ya sake fad’a cikin yanayi me wahalar fassarawa

Shashekar kuka yaji, ta fashe da kuka cikin muryar kukan tace

” Dan Allah Abba kayi hakuri?”

“Ai ba laifi kikayi min ba Zeenatu, alfarma kawai nake nema a matsayi na, na mahaifin ki.”

“Abba dan Allah kayi hakuri, wallahi ba zan iya hakura da Bashir ba.”

Kamar saukar aradu haka Abba yaji, ya dafe kansa ya shiga karanto innalillah wa inna ilaihi rajiun, babu babbar jarrabawa irin yayanka suyi rashin sa’ar miji, duk abinda yaje ya dawo dole kana ciki, kamar ka saida akuyar ka ne tazo tana ci maka danga, baya fatan hakan ta faru ga ita, shiyasa tun farko ya hakurkurtar da zuciyar sa be ga laifin ta ba sai na Mama, amma yanzu ya tabbata abinda Zeenat din take so shi Maman take goyan ba, dama mafiya yawan lokuta uwa na tafiya ne da ra’ayin yarta.

“Shikenan zeenatu, duk abinda yaje ya dawo karki kuka da kowa, ki kuka da kanki.”

“Abba dan…” Kafin ta kai karshe ya katse kiran, Jan kafarta tayi ta koma ciki tana jin a ranta tayi abinda ya dace, a kalla ta yi kokarin kare soyayyar ta ko ba komai idan akayi auren Abban zai hakura ya sakko.

“Lafiya?” Mama tace tana kallon ta.

“Ya kukayi da Baban naki? Maganar dai ce ko?”

Da kai ta amsa mata da eh, tsaki Maman taja

“Shine kike kuka ko me? Ni wai Zeenat asiri Bashir yayi miki ne? Da bakya ganin kowa da komai sai shi?” 

Kanwar Maman Atika ta fad’a cikin bacin rai

” Ni banga wani abun naci a Bashir din nan ba, tunda mahaifin yarinyar nan baya so toh a hakura mana? Iyaye maza sun fi mu tunani da hangen nesa.”

“Toh Atika ya za’a yi? Shi ma fa duk zuga ce wallahi, ai da be san da hakan ba sai bayan yaga mijin da yar lelen tasa ta samu, shikenan kuma sai kananan maganganu bansan daga ina ba, amma ina kyautata zaton daga wajen Gaji ne, dan ita kadai ce take sauya musu tunani da raayi dukkan su, ita kuma na tabbata munafurcin Iman ne dan ko yaushe tana wajen ta.”

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button