
Ahankali muryarsa Na rawa ya furta sunan Ramlat ….can km yasoma girgiza kanshi yana cigaba da kallon mahaifiyarsa hawaye km Na tsiyaya Daga idanushi murmushi takaici mama ta sake yi tana jin tayi daci da radadin ciwon abinda akayiwa diyar mutane duk da bata ganta ba Amman abun yata ruhinta da gangar jikinta .
Muryarta a sarke tace ” ita dayake ‘yar uwarka ce ba, shine duk ka frigice kadawo wani mutun abin tausayi , ba lalle sai d’an uwanka na jini kadai zaka iya taimakawa ba arayuwa .
, kamata yayi ka fi taimakon wanda yake da yak’ini akanka fiye da jininka.
, ni dai inda zan baka shawara ka kai gidan jaridu, TV, radio a buga labarin a ko’ina.
Ta yadda za ka samu sauke nauyin da Allah ya d’ora maka. Allah sarki yarinya karama hk abar tausayi ko a wani hali yanzu iyayenta suke ciki ?
Ko yaya zasu ji idan suka samu labarin mutuwarta mama takarasa mgnr zuciyarta cike da alhinin mutuwar yarinyar dabata San kowace ce ba..
Shiru Abdul yayi yana sauraron mahaifiyar tasa, sosai ta k’arayi masa nasiha ta k’ara masa k’arfin gwiwa, a YouTube Abdul ya fara d’ora video daga bisa yakai wa wani abokinsa dake aiki a gidan TV a gaban Abdul aka nuna video had’e dayin bayanin da yarinyar ta sanar dashi, duk da ba Abdul dinne yayi bayanin ba, daga direct gidan jarida ya wuce ya biya aka buga masa labarin.
Bayan kwana biyu labari ya kaiwa sanata Sambo, aiko hnklinsa ba k’aramin tashi yayi,ba.
cikin k’ank’anin lokaci labarin ya yad’a ko’ina duk gidan TV ko radio daka kunna maganar da akeyi kenan, sosai hankalin Sanata ya tashi, saboda hakan yana nufin rugugujewar siyasar shi.
Nan da nan sanata ya kira taron gaggawa, na manyan ‘yan siyar sa, ciki kuwa harda Haidar d’an sanata wanda yayiwa Aisha fyad’e bayan kowa ya zauna an natsa Sanata ya kalli Haidar yace ” kai ka fad’a min gaskiya kayiwa yarinyar nan fyad’e? kai tsaye Haidar yace ” eh Dad, cikin fushi sanata yace ” dan ubanka baka da hankali ne bakaga zab’e ya kusa ba, gashi nan sbd da sakarcinka kana neman ka watsar min siyasata danayi shekara da shekaru ina ginawa, ya kai dubansa ga sauran mutane yace ” meye shawararku yanzu akai ?
Babban yaronsa yace ” gaskiya ranka ya dad’e kar muyi wani motsi yanzu saboda idon jama’a yana kanmu, yaron zamu nemo musa ya k’aryata kansa, yace kud’i aka biyashi dan ya b’ata maka suna kaga daga nan zamu k’ara samun d’aukaka, kowa ya yarda da wannan shawara.
Kasancewar su manya ne a k’asa ba’a wani sha wahala ba, aka samu address d’in, Abdul har gida Sanata Sambo ya aiko aka tafi dashi cikin aminci da kwanciyar hankali, babu wata alama ta wulak’anta duk da dakyar Abdul yaje dan da farko k’in zuwa yayi sai da Mama ta matsa masa, bayan Abdul ya bayyana a gaban Sanata Sambo ne, Sanata ya gabatar masa da buk’atar sa, murmushi Abdul yayi yace ” gaskiya bazan iya ba.
Alahakikanin gaskiya acin zarafin yarinyar an cuceta an cuci rayuwarta da iyayenta.
Idan Na amsa bukartaku Na cika muku burinku na rufa muku asiri naje nakaryata abinda yake gsky ne akan siyarsarku ni km meyye hukuncina agurin Allah?
babu yarda Sanata Sambo baiyi da Abdul ba.. amma fir Abdul yak’i amincewa bukartasa sosai Abdul da Sanata Sambo sukayi cacar baki da musayar magana amma ba cikin fad’a, ba Abdul ya zage ba tsoro ballanantana wata fargaba ya dinga gayawa Sanata magana sosai daga k’arshe yace ” idan kashe ni zakuyi kuna iyawa amma gaskiya banza iya cin amanar mamaci ba.
, mai yasa d’anka bai yiwa bakin jijiyarsa key ba, ai yasan dakai da km siyarsarku amma yaje ya aikata san ransa.dan kawai yana takamar Ku wasu acikin kasa .
, dan haka wallahi wallahi banza tab’a karya alk’awari dana daukarwa yarinya ba.
Sai naga an durkufar danka gaban koto an yanke masa hukunci daidai da kaifinsa ta yadda ruhin yarinyar nan zai samu salama , yana kaiwa nan ya mik’e tsaye jikinsa a sanyaye yayi waje.yana takaicin masu hali irin Na senata sambo masu fifita harkar siyasarsu akan rayuwarsu wasu ..
Da wani irin kallo Sanata yabi bayan Abdul yana murmushi ‘cikin kasan ranshin , yace yaro baisan wuta ba saiya taka,i Dan kasan wata bakasan wata ba zan b’ullo maka ta yadda bazakayi tsammani ba, zan baka mamaki yaro, idan ko har kasa burina .
Na siyatata yak’i cikawa saina saka kuka .idan
har ka tsani kuka, sai na saka yin kukan jini da idanunka Sai Na gigita rayuwarka Na wujijiga duniyarka da farinciknka ta yadda har ka mutu bazaka daina kukan bak’in cikina …..
MOMYN ZARAH
[21/01, 04:12] +234 701 517 2910: GADAR ZARE!!!
(IT’S ABOUT DESTINY, HYPOCRITES, BETRAYALS)
~NA~
HAUWA A USMAN
JIDDARH
????KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍????
Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh
Gmail: jiddarh012@gmail.com
Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh
GARGAD’I
MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES , SU KARANTA BA
~DEDICATED TO~
AISHA A BAGUDO
8
Gida Abdul ya wuce Kai tsaye cike da alhinin abinda yashiga tsakanina da senator , yana shiga ya iske Mama a tsakar gida tana shara, tana jin shigowarsa ta mik’e tsaye tana kallonsa tace ” yaakayi ?
Ya kukayi da su ne?,tayi masa tmbyr ajere.
Acikin tsanake Abdul ya zayya ne mata komai , shiru Mama tayi na d’an wani lokaci, sannan tace ” ni dai Abdul ina jin tsoro kar wani abu ya sameka fa, mutanen nan ba imani gare su ba, akan cikar burinsu babu abinda bazai iya ba.
“Bakomai Mama in sha Allah babu abinda zai faru sai alkhairi, Allah ya sani dan shi nayi nasan kuma bazai tab’a bari a wulak’anta ba.
Km ma mama kece kika bani kwarin ya km naga duk jikinki Yayi sanyi ?
, jikin Mama a sanyaye tace “to shikennan Allah yabada sa’a Abdullahi, Ubangiji ya tsare min ka, Daga sharrin su Yasa kayi nasara akansu ” Amin Ameen Mama,t are da shigewa d’aki.
D’aki ya iske Umar yana sallah, zama yayi yana jiran ya idar, shima ganin Abdul d’in yasa bai ja doguwar sura ba, yana idarwa ya juyo .
Ahankali ya kalli Abdul din yace ” bro lafiya dai naganka hk ?
Guntun murmushi Abdul yayi sannan ya shiga bashi labarin duk abinda ya faru tun daga kan had’uwar shi da Aisha har zuwa yau din nan da Sanata Sambo ya nemi son ganinsa.
, shiru Umar yayi sosai yana tunani tare da nazarin mgnr , sai kuma yace ” gaskiya nima dai ta bakin Mama wallahi tsoro nake ji, bana san su cutar dakai.
, dan idan wani abu ya faru da kai, wallahi bazan tab’a ragawa iri irin su ba, dan sai na fi baya zama terror, sai na addabi ahalinsu gabadaya.
Murmushi sosai Abdul yayi yace ” da yardar Allah ma babu abinda zai faru balle na tuna maka jiya, ” Allah yasa haka inji cewar Umar.
Tun daga ranar da Sanata Sambo ya had’u da Abdul yaji ya k’ara tsanarsa fiya da koyaushe burinsa kawai yaga ya kawar da Abdul a doron kasa amma ya rasa ta inda zai b’ullowa al’amarin saboda kar jama’a su farga.
, saboda ga dukkan alamu Abdul ya tarwatsa masa siyasarsa, shiyasa a yanzu bashi da wani buri daya wuce yaga ya tarwatsa rayuwar Abdul, burinsa kawai yagan shi ya tagayyara, dan haka ya shiga binciken hanyar dazai b’ullowa al’amarin, cikin sa’a kuwa sanata ya samu labarin Umar, yasa akayi masa bincike akan sa sosai, ya samu cikekken bayani akan dangartakar su, da kuma halin Umar na baya, murmushi Sanata Sambo yayi sanda ya samu wannan damar, sannan yace ” da d’an gari kan ci gari.