GADAR ZARENOVELS

GADAR ZARE COMPLETE

GADAR ZARE COMPLETE HAUSA NOVEL

A kanta yaci gaba da kwanciya yana hutawa, sai da yayi wajen 10 minutes akan ruwan cikinta batare daya d’aga ta ba, suna ta faman mayar da lumfashi had’i da sauke ajiyar zuciya, a hankali Naseer ya mirgina gefen ta ya kwanta, yasa hannu ya jawo ta jikinsa ya matse ta da k’irjinsa yaja musu blanket iya cibiyar su, yana shafa kanta, ajiyar zuciya Zarah ta sauke a hankali cikin sassanyar murya tace ” Uncle ina san muyi wata magana dakai please, numfashi ya sauke sannan yace ” ok ina jinki, sai da ta d’anyi jummmmm sannan tace ” Uncle naji ranar nan kace duk wanda yazo duniya ta wannan hanyar yazo ko? “eh, ” to Uncle dole sai ta wannan hanyar kad’ai yake ake samun ciki da Baby, batare da ya kawo komai a ransa ba yace ” yes.

Cikin rawar murya tace ” kenan kana nufin har Na’eem ma ta wannan hanyar yazo, dole sai da akayi sex sannan aka same shi? gaban sa ne yayi muguwar fad’uwa, dan shi bai tab’a tunanin inda maganar tata ta dosa kenan ba, dan da ya san wannan tambayar zata yi mishi daya ce a’a, kallanta yayi cike da matsanancin mamaki, yaga duk ta koma kalar tausayi, k’ara jeho masa tambayar tayi, da k’arfi Naseer ya lumshe idansa, ya rasa mai zaice mata, ganin yayi shiru, yak’i cewa komai, yasa Zarah fahimtar amsar “eh ne, a hankali Zarah tasa hannu tana shafa kwantaccen gashin k’irjinsa, cikin rawar murya irinta masu kuka tace ” Uncle na rasa mai yasa har yau nak’i yarda kai ne mahaifin Na’eem, zuciya ta da ruhi na sunk’i aminta, sunk’i gaskatawa gami yarda cewar kai ne ainahin mahaifinsa.

” na rasa mai yasa har yau nake kokonto akan hakan, kwata-kwata zuciya ta tak’i yarda, nayi-nayi na yarda na amince ko sau d’aya ne na danganta ka dashi amma zuciya ta tak’i yarda na rasa mai yasa, saboda na tabbatar Uncle bazaka tab’a yi min haka ba, bazaka iya cutar da ni ba, bazaka iya wulak’anta min duniya ta ba, bazaka iya gigita rayuwa ta ba, bazata tab’a kawar min da farin ciki na ba, ka sanya ni cikin bak’in ciki da k’unar zuciya ba, Uncle na yarda dakai sosai, na yarda dakai fiye da yadda na yarda na kai, I trust you 100%, ta k’arasa maganar cikin kuka, kanta kawai ya shafa ya kasa cewa komai, cikin kukan ta kuma cewa ” please Uncle kayi min magana, ka fahimtar dani GASKIYAR AL’AMARI.

Ajiyar zuciya ya kuma saukewa ya shafa kanta cikin sanyin murya yace ” ni kuma na rasa mai yasa tun ranar danaga Na’eem nasan cewa d’ana ne, jini na ne, Zarah k’addara ta riga fata, sai dai kawai muyi addu’a, dan Allah Zarah karki kuma tada maganar nan, dan kwata-kwata bana k’aunar Na’eem ya girma yasa cewa shi shige ne, zata kuma magana yayi saurin had’e bakin su, tun daga wannan ranar Naseer ke satar hanya yazo bedroom d’in Zarah ya kashe arna, wani lokacin ma anan yake kwana sai an kira sallar asuba yake komawa bedroom d’in sa.

BAYAN WATA UKU

Har lokacin Zarah tana cikin matsananciyar damuwa a zuciyarta, gaba d’aya hankalinta yana kan Momynta Zainab, kullum da matsanancin tunaninta da kewarta take a ranta, kusan kullum sai tayi kukan bak’in ciki da takaici, tana dai dannewa ne ta barwa ranta saboda idan Momy da Naseer suka fahimta bazasu tab’a jin dad’i ba dan suna iya ganin duk abinda suke yi, da iya k’ok’arin da suke akanta ta raina, yayinda Na’eem yayi wayo sosai ya girma dan yanzu yana da kusan 6 months har ya fara rarrafe sai shegiyar b’anar tsiya, kwata-kwata baya jin magana, gashi da wayo dan da yaga yayi b’arna a waje zai rarrafa ya gudu wajen Ikram ko Momy, yayinda mugun san Na’eem yake k’ara shiga zuciyar kowa a gidan musamman Abban sa Naseer, yana mugun san Na’eem sosai,haka ma Momy, Dady, Ikram, Zarah ce ma bata wani damu dashi sosai ba, shiyasa shima kwata-kwata baya zuwa wajenta sai dai wajen Momy da Ikram ko Dady, idan ko Naseer yana gida baya tab’a yarda da kowa sai Abbansa, dan agaban uban kowa Naseer zagewa yake yi ya nunawa d’ansa so da kulawa.

A b’angaren su Aunty Zainab kuwa rayuwa suke cikin matsanancin bak’in ciki da damuwa, dan gidan yayi musu shiru, ba motsin kowa sab’anin da dasuke cikin kwaramniyyar Zarah da Ikram, musamman Zainab dan idan Mannir ya tafi aiki sai gidan yayi mata girma, ta rasa inda zata saka kanta da rayuwarta taji kamar tayi hauka, tasha zama tayi kuka kamar ranta zai fita.

Haka ma b’angaren Mannir tun ranar daya d’ora idansa akan d’an Zarah da Naseer Allah ya jarrabe shi da mugun so da matsananciyar k’aunar Na’eem, dan shi yanzu kwata-kwata bashi da wata damuwa ko matsala data wuce ta Na’eem, shi kansa ya rasa wanne irin so yake yiwa yaron, gaba d’aya baya cikin nutsuwa da hankalinsa, duk ya shiga damuwa ya rame, ga shi Dady ya hana shi zuwa gidan, balle ya rink’a ganinsa yana jin dad’i, duk ya lalace, kullum cikin tunanin Na’eem yake, ya d’orawa kansa tension, gaba d’aya san da yakewa Zarah sai ya koma kan Na’eem.

BAK’AR RANA

Ranar alhamis da tsakar daren juma’a da misalin k’arfe 3:20am Zarah ta farka da wani matsanancin ciwon k’irji, ta rink’a ji kamar zata mutu, Allah ya rufa asiri Naseer yau ma ya yiyo satar hanya yazo, dafe k’irjin tayi tana kakari, sai kuma ta fara shek’a aman jini ganin jinin ne yayi bala’in tsora ta, a kid’ime ta fara tashin Naseer, a hankali ya bud’e idansa, ganin halin da Zarah ke ciki ne yayi masifar d’aga masa hankali, cikin tashin hankali ya duro daga kan gadon, lokacin harta galabaita ta fara fita daga hayyacin ta, cikin matsanancin firgici ya d’auke yayi harabar gidan yana kwalawa Ikram kira.

A firgice duk ‘yan gidan suka fito Momy, Dady, Ikram, shi Naseer yama manta daga shi sai boxer, a kid’eme suka k’araso wajen ganin Zarah a sume ga jini yana fita ta baki da hancinta yayi masifar firgita su, da sauri suka k’arasa wajen, Dady ya karb’i Zarah yacewa Naseer ” maza jeka saka kayan ka, da gudu Naseer yayi d’akin, jallabiya da 3 quarter kawai ya zira ya fito.

Dady ne ke jan motar dan yasan Naseer bazai iya jan Motar ba, Naseer na baya rungume da Zarah, Ikram ma na baya tana ta faman kuka, Momy na gaba, tun kafin Dady ya k’arasa yin parking Naseer ya bud’e k’ofar motar ya fito ya sungumi Zarah yayi cikin asibitin da ita da gudu cikin matsanancin tashin hankali yake kwalawa Doctor kira.

Da hanzari suka nursing suka karb’i Zarah suka d’orata a gadon mara lafiya da sauri Doctor Jennifer (baturiyar nan) ta fito zata shiga emergency da Zarah, caraf Zarah ta rik’o hannun Naseer tana hawaye tace ” Uncle jiki na yana bani bazan tashi ba mutuwa zanyi, dan haka zan fad’a maka abinda ban tab’a fad’a maka ba, I LOVE YOU NASEER, I REALLY LOVE YOU SO MUCH, I LOVE YOU MORE MOST, I LOVE YOU WITH ALL MY HEART, gaba d’aya zuciya ta da ni kai na naka ne Naseer, ina sanka fiye da yadda nake san kai na da rayuwata, ba mutuwar da zanyi shine bak’in ciki na ba, babban bak’in ciki na shine zan tafi na barka kai kad’ai, cikin maraici, please ka kularmin da Momy na, ka yafewa Dady na abinda yayi maka, na baka amanar Ikram da Na’eem, please ku dawo kamar da kai dasu Momy, ka yafe musu, kace ni ma na yafe musu suma su yafe min, kai ma ka ya yafe min, in banda kuka babu abinda Naseer keyi, ya rik’e hannayenta gam cikin nashi, ya kasa koda furta kalma d’aya, kai kawai yake girgiza mata.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button