
” I love you ta kuma fad’a hawaye na zubo mata, ta bud’i baki zata kuma magana jini yayi tsartuwa daga bakinta da hancinta, numfashinta ya d’auke da sauri Jennifer ta saka mata oxygen ta bawa nursing umarnin shiga da ita emergency room.
A nan Naseer ya durk’ushe yana gurza kuka iya k’arfinsa, jikin kowa agun yayi mugun yin sanyi, Ikram ma sai kuka take yi, ba’afi 20 minutes da shiga da Zarah emergency room ba, Jennifer ta fito cikin matsanancin tashin hankali, da sauri Naseer ya mik’e had’i da nufarta, bakinta na rawa tace ” she is pregnant for 3 months, cak Naseer ya tsaida kukansa yace ” ciki?
“Yes of course, she is pregnant, cikin mamaki Naseer yace ” for 3 months? kafin ta bashi amsa wata nurse ta fito a firgice ta kira ta, da sauri tabi bayan ta, wajen 15 minutes ta fito cikin sanyin jiki muryarta na rawa tace ” she is dead.
” what? Cewar Ikram, wani Doctor ne ya fito daga emergency room d’in cikin sanyin murya yace ” sai dai muyi hak’uri, wanda yafi mu sonta, ya kuma bamu aronta ya kira ta izuwa gare shi, Allah ya karb’i rayuwar kayansa, ALLAH YAYIWA ZARAH MUHAMMAD RASUWA………..
Bana editing novels d’ina so nasan akwai typing errors da yawa
MOMYN ZARAH
Visit to Like my Page-https://www.facebook.com/Hauwa-A-Usman-Jiddarh-Novels-310316182944006/?referrer=whatsapp
GADAR ZARE!!!
(IT’S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)
~NA~
HAUWA A USMAN
JIDDARH
????KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍????
Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh
Gmail: Jiddarh012@gmail.com
Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh
GARGAD’I
MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA
~DEDICATED TO~
AISHA A BAGUDO
BEST FRIEND FOREVER & EVERZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA
~(UMMU AMAN)~
55
A haukace Naseer ya mik’e yace ” waye ya mutum? please karku ce min Zarah, dafa shi Doctor d’in yayi had’i da cewa ” am sorry, zuciyarta ce ta buga, cikin tashin hankali Momy ta kalli Doctor, batare datace komai ba, tun daga nan Naseer bai kuma cewa komai ba, ya koma ya zauna kamar wani sakarai, ganin an fito da Zarah daga emergency room fuskarta da jikinta rufe da farin k’yalle yasa Ikram d’ora hannu aka had’i da karma uban ihu ta sulale k’asa sumammiya, da sauri nursing sukayi kanta suka shiga bata taimakon gaggawa, Dady na hawaye ya ciro wayarsa daga aljihu ya kira Alhaji Abdullahi murya Dady na rawa yace ” Assalamu Alaikum, jin yanayin muryarsa yasa Alhaji Abdullahi dake kishingid’e saurin tashi zaune, ba tare daya amsa sallmar ba yace.
” El-Mustapha lafiya kuwa naji ka haka?
Da kyar Dady ya daure yace ” Allah ya yiywa Zarah rasuwa, cikin mummunan tashin hankali ya mik’e tsaye yana cewa ” innalillahi wa’inna ilaihirraji’un, cikin rawar murya yace ” kuna ina yanzu?
” Muna asibiti amma yanzu zamu karb’i gawarta mu koma gida, “ka sanar da iyayen nata?
” No ban sanarwa da kowa illa kai dana sanar yanzu, ” to shikenan mu had’u a gidan, a rud’e Alhaji Abdullahi ya mik’e yana sanarwa da Kakar Zarah, tana jin rasuwar Zarah ta fasa kuka, yana fituwa harabar gidan ya fara kwalawa driver kira kamar zai tashi sama, ana tafiya yana yiwa driver magana akan ya k’ara taka motar dan shi gani yake kamar ba tuk’in yake ba, a d’imauce Alhaji Abdullahi ya kira Abban Zarah yace su had’u yanzu a gidan El-Mustapha.
Duk wasu k’adoji da ake bi wajen karb’ar gawa Dady ne yayi aka basu gawar Zarah suka nufi gida da ita, har lokacin Naseer yayi jigum kamar wani tab’ab’b’e koda za’a shiga mota sai Momy ta rik’o hannunsa ta shigar dashi.
Haka kawai Abban Zarah yaci gabansa na muguwar fad’uwa, kwata-kwata hankacinsa yak’i kwanciya, tsoro da fargaba sun dirar masa a cikin k’ank’anin lokaci, dan haka ya kasa tuk’in yasa driver ya tuk’a shi.
A mota Dady ya kira Mannir yace masa duk abinda yake yi ya bashi nan da 10 minutes su had’u a gida dashi da Zainab su zo yanzu, a tare Dady da Alhaji Abdullahi, Abban Zarah suka isa gidan, ana yin parking Naseer ya fito sukuku ya shige bedroom d’insa ya rufe, yayi zaman dirshan a k’asa, ya kasa yin komai dan kwakwalwarsa ta daina aiki, shi bai ma san waye shi ba, da gudu Ikram ta fito ta fad’a jikin Alhaji Abdullahi tana gunjin kuka, fito da gawar Zarah akayi daga cikin mota aka shigar da ita main parlor gidan, shi dai Abban Zarah tsaye yayi cikin mutuwar dan har yanzu bai san takamai-mai abinda ke faruwa ba.
Cike da matsanancin farin ciki Mannir ya shigo gidan yana d’okin ganin Na’eem, Zainab ko sai cika take matsewa, tun daga harabar gidan take jiyo ihuuuu Ikram tana kuka, da sauri Mannir da Zainab suka k’arasa shiga gidan cikin matsanancin firgici, da sauri Ikram ta saki jikin Alhaji Abdullahi tayi wajen Zainab tana kuka tace ” shikenan Momy Zarah ta tafi ta barmu, Momy ZARAH TA MUTU!!!.
Wai tashin hankali wanda ba’a saka masa rana, saboda tsabar rud’ewar da Zainab tayi rufe Ikram tayi da duka hannu bibbiyu kamar zata kashe ta tana cewa” uban ki ne ya kashe ta, dakyar aka kwaci Ikram daga hannun duk ta rud’e ta fita hayyacinta.
Shiko Mannir k’amewa yayi a tsaye ya kasa kwakkwaran motsi, a hankali Alhaji Abdullahi ya kama hannun Zainab ya kai ta har gaban gawar Zarah dake kwance yace ” gata nan ki bud’eta ki gani da idonki dan ki tabbatarwa da kanki, hannun Zainab na kerrrrrrma idanta na duk ya firfito waje tasa hannunta dake rawa ta yaye farin k’yallen da aka rufe fuskar Zarah dashi, da sauri ta runtse idanuwanta had’i da had’iyar yawu k’uttttttt.
A hankali ta sauke idanta akan gawar Zarah, a haukace Zainab tayi baya da sauri had’i dayin zaman dab’aro a k’asa ta d’ora hannu aka ta kurrrrrrma uban ihuuu, a d’imauce take girgiza kanta hawaye na zuba tana cewa ” wallahi k’arya ne Zarah bata mutu ba, duk wanda yace min Zarah ta ta mutu sai na kashe shi.
A kid’ime ta mik’e ta nufi wajen Dady tace ” Dady please ka dawo min Zarah ta, ina tsananin buk’atar ta, idan ta mutu ta barni nima mutuwa zanyi, wallahi ina matuk’ar san Zarah sosai, har cikin rai na da zuciya ta kullum sai nayi kukan bak’in cikinta a kusa dani, dan girman Allah ku tashe ta, ganin Dady bayyi magana bane tasa ta nufar Alhaji Abdullahi tana k’ugin mutuwa tace ” please Abba ka taimaki rayuwa ta ka dawomin da Zarah ta da……….
Wani gigitaccen mari Alhaji Abdullahi ya kifawa Zainab, cikin k’onar zuciya yana zubar hawaye ya kalle ta yace “, kina san nata ne kika yi watsi da ita da lamuranta, dan Allah ya d’ura mata k’addara, wacce ke kanki yaki fi k’arfin Allah ya jarrabeki da irinta ba, wanda nasan idan ke Allah ya jarraba da irin k’addarar daya jarrabi Zarah da ita Fatima mahaifiyar Zarah bazata tab’a yin watsi dake da rayuwarki ki ba.
” Wallahi nasan mahaifiyar zata bazata tab’a yi miki abinda kikayiwa tilon ‘yarta ba, nasan koda duk duniya zata juya miki baya ta k’i ki Fatima bazata tab’a juya miki baya tak’i ba, koda za’a zare mata rai, zata iya rabuwa da kowa akanki, tasha hawala akanki, tayi wahala dake iya rayuwarta tayi miki duk abinda uwa take yiwa ‘yarta, ko sau d’aya bata tab’a kallan ki a matsayi k’anwarta ba, tana d’aukarki ne a matsayin ‘yar cikinta, amma ke tilon ‘yarta guda d’aya tak data mutu ta bari bari in kasa yi mata irin rik’on data yi miki, kin wulak’antar da ita da rayuwarta, alhalin nasan da Ikram Allah yayiwa wannan jarabawar dabaki mata abinda kikayiwa Zarah ba.