
“Mahaifinta cikekken mutum ne wanda ya isa a kira shi d’an halak, kuma asalin bafulatani na kwarai, tun da ake abin nan yayi muku kara ke da mijinki bai tab’a yin ko tari ba, bayan nasan yana jin abin har cikin ransa da k’ok’on zuciyar sa, yana dai d’auke kai ne kawai, har dukan mutuwa kukayiwa ‘yarsa , da karaya biyu, amma ko kallan banza bayyi muku ba, bayan kema a matsayin ‘ya kike a wajensa, yana da ikon hukunta kamar yadda kuka hukunta Zarah, tak’amarku dai kun rik’e Zarah kuke ganin kuna da k’arfin iko akan ta, to kamar yadda kuka rik’e masa ‘yarsa haka shima ya rik’e ki, duk gata da so da kike tak’amar kinyiwa Zarah haka shima yayi miki, kuma bashine ya baki rik’on Zarah da kansa ba, ke da kanki kika nema wanda a lokacin ma kara yayi miki kawai ya baki dan bai so rabuwa da ‘yar sa a lokacin ba, amma haka ya daure ya baki ita.
Saboda kara irin ta shi, dan ko a mutanen da ba kowa ne zayyi irin karar da yayi ba, kuma tunda ya baki ita bai tab’a nuna miki komai ko a fuskarsa ba, amma ku kun taru kun azabtar mishi da ‘ya, daga k’arshe ma kunyi sanadin barinta duniya, kina tsammanin Fatima zatayi farin ciki da muguwar sakayyar da kika mata ya k’arasa maganar yana hawaye, cikin muryar kuka yace ” na zuba muku ido ne dan naga ko zaku gane abinda kukeyi ba dai-dai ne kuskure ne, ku gane kuranku amma ina kun riga da kunyi nisa, ni wallahi kunyar Muhammad nake ji, da sauri Abban dake kuka tun lokacin da Ikram tace Zarah ta mutu, sosai yake kukan bak’in ciki da takaicin karar da yayiwa wad’anda kwata-kwata basu san kara da kawai ba yace.
” A’a Alhaji har abada babu wannan a tsakanin mu, kuskure ne mu duka munyi sai dai a kiyaye gaba, Zainab dake tsaye ta zube akan gawarar Zarah had’i da d’ora hannu aka ta zunduma iban ihuuuu ta na birgima tana cewa ” wayyyyyyyo ni Zainab na shiga uku naga ta kaina ina zan sa rai da rayuwata, naga taskon rayuwa gami k’angin duniya, sosai Zainab take bori had’i da zunduma uban ihuuuu.
Cikin rawar murya Dady yace ” duk mai faruwa dai ta riga da ta faru aikin gama ya gama, yanzu muyi gaggawa kamar yadda Allah yace mu kaita makwancinta, Alhaji Abdullahi yace ” a shirya ta kafin sallar juma’a sai ayi jana’izarta a masallacin juma’a bayan an idar da sallar juma’a, cikin k’anganin lokaci akayi mata wanka aka shirya ta tsaf cikin likkafani a bisa koyarwar sunnah, Alhaji Abdullahi yace ” a kira mijinta, d’an jummmm Dady yayi dan yasan akwai tashin a kiran Naseer shi inda san ranshi ne a barshi kawai a yadda yayi hocking d’inan, k’ara maimaita maganar Alhaji Abdullahi yayi a karo na biyu, cikin mutuwar jiki ya nufi bedroom d’in Naseer, acan k’uryar gado ya had’a kai da gwiwa kawai ya rasa meke faruwa.
Hannunsa Dady ya rik’o batare dayace masa komai ba, aiko ba musu Naseer ya biyo Dady kamar sakarai ko dolo, haka suka isa parlor kamar rak’umi da akala, Alhaji Abdullahi ya nuna masa gawar Zarah dake rungume a jikin Zainab yace ” kayiwa matarka addu’a.
A hankali Naseer yabi inda Alhaji Abdullahi ya nuna masa da kallo, maganganun da Zainab keyi rungume da Zarah ne suka dawo dashi cikin hayyacinsa, Zainab cikin kuka ke cewa ” ina sanki Zarah, dan Allah ki dawo karki tafi ki barmu please, wallahi ina miki mugun so, meye zakiyi nesa damu, meyasa ta har abada ba dawowa Zarah meyasa zaki MUTU!!!.
Sai a lokacin Naseer ya tuna abinda Doctor yace masa ” ALLAH YAYIWA ZARAH MUHAMMAD RASUWA, a hankali ya juya inda inda yake jiyo gunjin kuka Ikram ya juya kalli Abban Zarah yaga shima kukun yake, a hankali ya rink’a bin jama’ar wajen yana kallonsu, yaga kowa kuka yake ya juya ya kalli gawar Zarah dake kwance cikin linkafani tab!!!! tashin hankali wanda ba’a sa mara rana, wani irin mahaukacin gigitaccen fitinannan uban ihuuuuu Naseer ya baki iya iya k’arfinsa ya kurma had’i da dafe fuskarsa da tafin hannusa ya durk’ushe wajen yana kurma gigitaccen Ihuuuuuuuuuuuuu kamar ransa zai fita.
Hannu yasa yana cizgar gashin kansa yana yakushin fuskarsa, yana ci gaba da sakin fitinannan ihuuuu, a haukace yaje wajen gawar Zarah ya d’aga ta ya rungume gam a k’irjinsa yana kuka yake cewa ” mai yasa zakiyi min mai yasa zaki tafi ki barni, bayan kin yi min alk’awarin kasancewa dani har rai da mutuwa, mun gama tsara rayuwarmu, mun tsara yadda zamu rayu da yaran mu cikin farin ciki, mai yasa Zarah ya k’ara fashewa da mahaukacin kuka, dai-dai lokacin Na’eem ya tashi daga bacci had’i da tsandara k’ara, a kid’eme Naseer ya nufe shi ya d’aushi ya kawo shi kan gawar Zarah yana nuna masa yace ” please Na’eem kacewa Momynka ta tashi karta tafi tabar mu cikin maraici da kad’ai, gaba d’aya Naseer ya fita fit daga hayyacinsa ya koma cikekken mahauci, cikin rashin nutsuwa yake yin komai, sai a lokacin hankalin Mannir dake tsaye kamar mutum mutumi dan ya gazayin komai, tsaye kawai yake yana zubar da hawayen bak’in ciki daka kallan shi kasan yana cikin tsantsan nadamar rayuwa, hankalinsa ya kai ga Na’eem dake ta faman rusa kuka yana laluben nonon Zarah.
Cikin tsananin bak’in cikin rayuwa Mannir ya fasa kuka dan ya kasa controlling kansa, gaba d’aya wajen tausayin Naseer da Na’emm ya mamaye musu zuciya da duk ilahirin jikinsu, tuni Zainab ta yada hijab da d’an kwalli babu abinda ya rage a jikinta sai doguwar riga, duk ta zare ta d’imauce ta fita daga hayyacinta, a firgice ta mik’e ta nufi Naseer tasa hannu tana k’ok’arin kwace Na’eem daga gareshi, d’ago jajayen idanuwansa da suka gama rinewa yayi ya kalle ta, ganin Zainab ce tsaye a gabansa tana k’ok’arin kwace Na’eem yasa shi tuna duk abubuwan data yiwa Zarah.
Aiko cikin zafin rai ya mik’e ya kifa mata lafiyayyen marika guda biyu kyawawan masu k’arfin gaske wanda sai da suka sakata bajewa wanwar a k’asa,, ya damk’ i wuyanta yace ” kinsan me yayi sanadiyyar mutuwar Zarah?
A haukace yace ” mata ciwon zuciya, ya nuna saitin zuciyarsa yace mata ” zuciyarta ce ta buga, wanda kece sanadiyyar faruwar hakan, Zainab, Zarah bata da wata matsala ko damuwa balle bak’in ciki sai naki, kullum sai tayi kukan rashinki a kusa da ita da kuma kewarki, kallo d’aya zaga yiwa Zarah kasan tana cikin matsananciyar damuwa, duk iya k’ok’arin dake nake naga na sanya ta cikin farin ciki da walwala amma a banza saboda tunaninki, duk iya k’ok’ari na akan naga Zarah ta rayu cikin farin ciki amma sai da kika wargaza min burina KIKA YI AJALIN ZARAH.
A firgice ta kalle shi cikin alamun tambaya amma ta kasa furta koda kalma d’aya, kallanta yake shima yace ” yes ZAINAB KECE SANADIYYAR MUTUWAR ZARAH, saboda da bakiyi abinda kika yi ba da bata mutu ba, da kin yarda da k’addara, kin kuma d’auki k’addara kin fauwalawa Allah komai da hakan bata faruwa ba, da kin rungume ta kin saurare ta, kinyi mata gata kin zame mata uwa ta gari da batayi kukan bak’in ciki har ciwon zuciya ya kamata ba, da kin yarda da rantsuwar data miki da Qur’an da kin jata ajikinki kin nuna mata so da kulawa Zainab kin cuce mu.
Wani mahaucin kukan ya kuma saki, cikin rashin nutsuwa Naseer yasa hannu ya damk’i k’afarta ya fara janta a k’asa………….
MOMYN ZARAH
Visit to Like my Page-https://www.facebook.com/Hauwa-A-Usman-Jiddarh-Novels-310316182944006/?referrer=whatsapp