
Hawaye na zuba daga fuskar Abban Zarah ya shafa kan Zainab yace ” wanda ya bamu ita ya kuma fi mu santa ya karb’i abarsa dan alk’awarin Allah baya tashi, babu abinda Zarah tafi buk’ata daga gare mu yanzu sama da addu’a shine kad’ai hanyar da zamu nuna mata tsantsan so da k’aunar da muke mata, muna nan duk zaman jiran namu lokacin komawa ga Allah muke, domin gaba d’ayan mu matafiya ne, komai dad’ewar dazakayi a duniya dole akwai ranar da zaka barta ka amsa kiran mahaliccinka.
” Dan mutuwa bata kwankwasa k’ofa, kuma Allah baya tab’a barin wani dan wani yaji dad’i, idan lokacin mutum yayi ko 1 second baza’a tab’a k’ara masa, a koyaushe, a ko’ina idan lokaci yayi tafiya zamuyi batare da wani b’ata lokaci ba, shin kana ina, me kake aikatawa a dai-dai lokaci nan, wallahi idan tazo aduk yadda kake tafiya zakayi, shiyasa ake san a koyaushe, a ko wanne lokacin mutum ya kasance yana aikata alkhari, ana san d’an Adam ya kasance mai tsoran Allah, mai aikata alkhari a kowacce rana dan yanzu mutuwar bazata ake yi, sai a kwanta dakai ba’a tashi da kai ba, ko’a tashi dakai ba’a kwanta dakai ba, dan haka mu kasance masu tsoran Allah da tunawa da ranar sakamako, mu kyautata mu’amular a tsakaninmu, mu kyautatawa junnanmu zato, mu zamo masu yafiya da afuwa, mu zamo masu zumunci, mu zamo masu duban laifukan kan mu, bana wasunmu ba, mu zamo masu yiwa kanmu hisabi.
Sosai Abban Zarah yayi musu nasiha mai ratsa zuciya, daga k’arshe Alhaji Abdullahi ma ya k’arba yayi iya yinsa akan yadda da k’addara da jarawar Ubangiji, haka ma Dady yayi iya yinsa, dan gaba d’aya jikin su yayi mugun yin sanyi, sun saduda, cikin ikon Allah sosai zuciyar Naseer tayi sanyi, ya ji sauk’in abinda yake ji, zugi, da rad’ad’in da k’irjinsa yake masa yaji ya ragu sosai, haka ma tafasa, k’ona, azalzala, zafi, k’unci, da zuciyarsa ke masa yaji duk sun gushe, a hankali Naseer ya mik’e ya d’auki Na’eem dake cinyar Mannir ya mik’awa Momy batare dayayi magana ba ya juya ya nufi bedroom d’in sa, kiran sunansa Alhaji Abdullahi yayi ” Naseer! tsayawa yayi cak batare daya jiyo ba, ” ka yawaita fad’ar
انا لله و انا اليه راجعون
اللهم اجرني في مصيبتي واخلفلي خيرا منها
استغفر الله
سبحان الله والحمد لله والله اكبر
حسبنا الله و نعم الوكيل الحمد لله
” in sha Allah, Allah zaya yaye maka damuwar ka yayi maka maganin damuwar da kake cki, ya ya gusar maka da bak’in cikin dakake ciki, murmushi Naseer yayi masa batare dayace komai ba ya shige bedroom d’in sa, ya kulle.
Addu’a Dady yayi aka shafa, Dady ya kalli Zainab yace ” yaushe zaki koma gidan ki? cikin muryar kuka tace ” sai anyi sadakar bakwai, “ok kawai Dady yace, Momy dai batace komai ba illa rungume Na’eem datayi a k’irjinta tana hawaye, tana k’ara jin tsananin tausayin yaron a ranta, ranar da daddare Naseer na kwance wajen karfe 1:00am na dare ya kashe gaba d’aya light d’in dake bedroom, ya kwanta rigingine yana kallan sama ya tsunduma duniyar tunani yayinda hawaye ke zubo masa.
A hankali yaji motsi a gefensa, cikin mutuwar jiki ya juya b’angaren dayaji motsin, Zarah ya gani zaune a gefensa sanye da doguwar riga ta atamfa ta saka hijab tana yi mishi murmushi hawaye na zuba daga idanunta zuwa kuncinta, a hankali tasa hannunta, ta shafo fuskarsa, zuwa sajensa, ta cusa hannunta cikin sumar kansa cikin muryar kuka tace ” Uncle bakayi min adalci ba, da ma wannan ce irin soyayyar da kake min, kasan bana san b’acin ranka balle har yakai ga kayi kuka, Uncle matuk’ar kana san na kwanta a kabarina cikin salama kayi min alk’awarin baka k’arayin kuka, yana hawaye ya girgiza mata kai, “a’a kayi min magana kace kayi alk’awarin baka k’ara kuka cikin rawar murya yace ” nayi miki alk’awarin ban kuma kuka, amma me yasa kika tafi kika barni, murmushi tayi takai masa kiss, lumshe ido Naseer yayi, jin shiru yasa Naseer saurin bud’e ido, ganin wajen yayi ba kowa mik’ewa yayi ya kunna light yaga kwata-kwata ba alamun Zarah, hannu ya d’ora akansa yana shirin kurma ihuuuuuuu sai ya tuna da alk’awarin daya yiwa Zarah, dan haka yayi saurin maida kukan sa ya shiga kukan zuci, ya tabbatarwa da kansa Zarah ta fara yi masa gizo, mik’ewa yayi ya shiga bathroom ya d’auro alwala, yazo ya tada sallah, tun daga ranar Naseer ya daina haukan kuka da ihuuuuuuu ya koma kukan zuci kawai.
Ya zama so silent kamar bashine Naseer d’in da, mai yawan wasa da dariya, mai yawan san barkwanci da yawan tsokana ba, duk ya zama wani iri dashi kwata-kwata baya magana, kullum yana d’akinsa rufe idan kaga ya fito to masallaci zashi, dan ko abinci baya ci, sai Momy ta matsa masa dakyar yake shan tea ko coffee.
Ranar sadakar bakwai Naseer yana kwance a bedroom d’in sa ya rink’a jiyo magana sama-sama, kasancewar baya san hayani ko yawan magana yasa Naseer mik’ewa dan ya sawa kofarsa key, yana kaiwa dai-dai k’ofar ya jiyo maganar Zainab na cewa ” Momy duk duniya babu wanda yafi cancanta daya rik’e Na’eem sama dani, dan Allah Momy ki bani shi, tab!!!! Wata irin muguwar zabura Naseer yayi a sukwane yayi waje bibbiyu yake taka step d’in saboda tsananin sauri…………………
A zafafe ya fisge Na’eem daga hannun Zainab a matuk’ar fusace ya kalleta ido cikin ido yace ” lalle Zainab ke cikekkiyar mara kunya ce, fitsararriyar zamani ce, ke yanzu idan kina da kunya da cikekkiyar nutsuwa ko bana raye kyama soma tab’a Na’eem?
“Ko an gaya maki na manta abubuwan da kika yi akan shi, tun kan yazo duniya tun yana cikin mahaifiyarsa, sai yanzu ne zaki nuna so da damuwarki akan sai yanzu zaki kula dashi, ko shima kina san na bak’i rok’onsa ne ki salwantar da rayuwar sa kamar yadda kika salwaantar da rayuwar mahaifiyarsa?
“Ko ke a zantan ki bazai samu labarin kashe masa uwa da kika yi ba?
“Ko kina san wanke laifin ki ne a wajensa dan kar ya girma ya d’au fansa?
“To bari kiji matuk’ar mahaifinsa Naseer Mustapha yana raye sai ya d’au fansa, kuma karki d’auka kinci banza ko rayuwar Zarah ta tafi a banza, dan wallahil azim bazan tab’a barin makasan Zarah su rayu cikin farin ciki da walwala ba…….
Ihuuuunn kuka Zainab ta zunduma had’i dayin kukan kura tayi kan Naseer………
MOMYN ZARAH
[14/02, 22:00] Atk: Visit to Like my Page-https://www.facebook.com/Hauwa-A-Usman-Jiddarh-Novels-310316182944006/?referrer=whatsapp
GADAR ZARE!!!
(IT’S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)
~NA~
HAUWA A USMAN
JIDDARH
????KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍????
Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh
Gmail: Jiddarh012@gmail.com
Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh
GARGAD’I
MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA
~DEDICATED TO~
AISHA A BAGUDO
BEST FRIEND FOREVER & EVERZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA
~(UMMU AMAN)~
57
Kukan kura tayi,tayi kan Naseer a fusace, murmushi Naseer yayi had’i da gyara tsaiwarshi yana jiran k’arasowarta, cikin zafin nama, Mannir yayi wuf ya tare ta dan yaga shirin da Naseer yayi yana jiran k’arasowarta, fisge-fisge ta fara yi tana son kwace kanta daga rik’on da Mannir yayi mata, amma inaaa yayi mata mugun rik’on da bazata iya kwacewa ba.
K’ara tayi mai k’arfi ta fisge kanta daga jikin Mannir ta durk’ushe k’asa had’i da fasa kuka mai k’arfi, hawaye na zubowa Naseer yace ” Zainab kin cuce mu, akan cikin yaron da kike so abaki ki rik’e kikayi sanadiyyar mutuwar mahaifiyarsa, saboda rashin yadda da k’addara, kuka zage ke da mijinki kukayi mata dukan mutuwa, harda karaya biyu tsabar rashin imani da tausayi, tsabar babu tsoran Allah kwata-kwata a zuciyar ku.